Hausa Novels and Stories

Auren Shehu Hausa Novel Page 3

Sponsored links

Cewar ta dan tsoro ta kasa magana, gani ta ke burin Halitta ta biye ma ta su yi hayaniya dan ta sami damar tona mata asiri. Halitta na fita Ammy ta bi bayan ta na faɗin

“bari na bi bayan ki Halitta, babu mamaki Falmata na nan ɗakin ta tsoro ya hana ta motsawa”

Suna fita ta fidda wayar ta da ya dame ta ta da ƙugi, ganin wanda ke kiran ta ta ja tsaki, ɗagawa ta yi tare da karawa bisa kunnan ta, cikin nuna fushi ta ke magana

“Bobo wai menene? Na faɗa ma ka zuwa na club in dai na dawo hutu gidan nan abu ne mai hatsari, ka bari mu koma school ka ce ah ah, ga shi kai ba za ka iya bari mu dawo da asuba ba sobada jarabar bacci irin na ka, ai gashi yau saura kiris Dady ya kama ni!”

Shiru ta yi na wani ɗan lokaci ta na sauraran shi, kafin daga bisani ta kashe wayar ba tare da ta sake tankawa ba. Nan ta kwanta ta na jiran tsammani, jin shiru babu wanda ya dawo ta san asirin ta bai tonu ba tukunna, dan haka ta tashi, kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka tare da ɗauro alwala domin rama salloli uku da ke kan ta, la’asar, magariba da isha’i.

***

Allah yayi dare gari ya waye. Babban ɗaki ne irin na ƴaƴan manya, komai na ɗakin an yi masa ado da kala biyu, wato shuɗi da fari. Ba wani tarkace ba ne a ɗakin, face ƙatan gado na alfarma tare da setin madubi da dirowa.

Kamar kullum yau ma sai da rana ta take, bayan ladanin masallacin da ke cikin gidan su ya ƙira sallar azahar sannan ta iya motsawa, wayar ta ta jawo, ta shiga Instagram in da ta saka hotan da ta yi daren jiya a club. Nan da nan hotan ya sami karbuwa in da samari da wasu yan mata su ka shiga danna mata “like” tare da “comments” kamar yanda aka saba. Sai da ta gamsu sannan ta aje wayar ta tashi da kyar ta yi wanka tare da ɗauro alwala.

Maimakon da ta fito ta yi azama wajen rama sallolin da ake bin ta, wato Asuba da Azahar, sai ma tsayawa ta yi gaban madubi ɗaure da tawul da ya tsaya iya gwiwa, cikin jin daɗi da alfaharin baiwar dirin da Allah ya mata, da ke masha Allah ita kan ta ta san Allah ya mata mata dire. Hakan ya s koda yaushe ta na kan social media cikin saka hotunan ta wanda ta yi da matsattsun kaya, dan kuwa ta na cikin ɗaya daga cikin sannanun matan nan da ake kira “Slay Queen” a Instagram.

Sai da ta ɓata lokaci wajen shafe shafe da kwalliya, ta fito fes cikin ɗinkin atamfa riga da siket, sannan ta ɗauko hijabi wanda ya ke kai mata har ƙasa ta sanya. Murmushi ta ke ganin yanda ta fito saliha sak, ita da kan ta ta shiga yiwa kan ta kirari

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button