Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 22

Sponsored links

**************

Ahmad Ɗakin shi dake daidai Ƙofar Fita daga sashin su ya karɓi Key wajan Kamal ya Buɗe ya shiga ciki, Ko ina na ɗakin Need babu datti sabida gyaran da yake sha wajan su Naja dan kullum sai sun Buɗe ɗakin sun share sun Goge kayan wutar dake Ciki wannan yasa ɗakin babu datti ko tarkace.

A falon daya sha manyan kujeru masu tsananin kyau da ƙatuwar Tv da Shinfiɗaɗɗan carpet kamal ya aje masa Jakar Shikuma Ahmad ya wuce Bedroom Domin yayi wanka nan ma a gyare yake tsaf dan hatta Bedshirt An sauya shi da wani fari tas mai kyan gaske Taka Luntsumemen carpet ɗin dake Bedroom Ɗin yayi zuwa gaban gado yana shaƙar ƙamshin turaren daya kama ɗakin ya sami muhalli aciki tare da soma Cire Botiran gaban rigar kakinsa………….

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

Ya ɗaura faffaɗan tawul a ƙugunsa Ya shiga Bathroom.

Ya Jima aciki yana wanka kafin ya fito Ya shirya Cikin wata Black jallabiya mai gajeran Hannu wadda aka mata aiki da Golden Ɗin zare mai layi layi Daga gaban ta Kuma a buɗe yake wanda ya bawa Gashin dake saman ƙirjinsa wanda ya tawo har ta wajan wuyan shi damar bayyana a sarari.

Turare mai daɗin ƙamshi ya fesa sannan ya ɗauki wayar shi daya aje a saman gado ya fita daga Ɗakin Gaba ɗaya ji yake ya gaji,Jin ana kiran sallar magariba yasa ya Ɗaura alwala a famfon dake Bakin Ɗakin nashi ya fice masallaci Zaman jiran Jam’i yayi har aka taru a masallacin suka yi sallar magariba sannan ya fito ya Nufi cikin Gida.

Babban falon Mama ya shiga Bakin sa ɗauke da Sallama.

Jin Shuru a falon ya tabbatar masa da duka Ƴan gidan sallah suke Domin hatta Tv an kashe ta.

A hankali yake taka ƙafarshi A saman Shinfiɗaɗɗan Carpet Ɗin daya malale Falon Har ya sami damar ƙarasawa Bakin Ƙofar Bedroom Ɗin Mama sai da ya buga ƙofar sau Uku sannan tai masa gyaran Murya.

Murɗa Handle ɗin Ƙofar yayi ya shiga Cikin Bedroom Ɗin Bakin sa ɗauke da sallama yana mai Lumshe idanunshi wani irin haɗaɗɗan Ƙamshin Turaren wuta wanda ya haɗe da Iskar Fanka na ratsa masa dukkan sassan Jikinsa.

Gyaran Murya ta kuma yi masa sabida haka sai ya nemi Gefenta ya zauna wadda take zaune a saman darduma tana lazimi da ƙaton Carbi mai Dubu a gabanta.

Zaman kusan Minti Talatin Yayi kafin ta shafa addu’ar ta Ɗago da kanta Cikin murmushi tace masa.

“Barka da dawowa Ina maka fatan nasara a cikin rayuwarka”

Ta furta hakan cike da so da ƙaunar ɗan nata cike da Ranta da zuciyarta.

Wani irin ƙayataccen Murmushi Ahmad ya saki yana shafa saman kanshi da Hannun shi cikin nagartacciyar Muryarsa mai cike da Haiba da nagarta yace.

“Mun same ku lafiya Mama? Yaya gida da yara Ina Alhaji tun da nazo ban gan shiba ko a masallaci?”

Cikin Murmushin daya ƙi gushewa a saman Fuskarta tace masa.

“Alhaji ya fita Cikin gari Gaisuwar abokin sa, Gida kuma Alhamdulillahi da kowa da Kowa muna cikin Godiyar Allah”

Daga haka taja Bakinta tayi shuru.

Shima Sunkuyar da kanshi yayi a ƙasa bai Kuma cewa komai ba sabida Rashin sabon doguwar Maganar da bata fiye shiga tsakaninsu ba sakamakon Alkunya da Mama take masa ta ɗan fari.

Mama Muje tare dan Allah yaushe rabona dake ai mayi Hirar yaushe gamo”

Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

Ɗago kanta tayi ta zabga masa harara tana mai kawar da kanta Gefe ɗaya Sanin ba zata tanka masa ba yasa ya miƙe Yana cigaba da dariyar daya keyi wadda In ba a gaban maman ba babu mai samun arziƙin Ganin dariyar tashi.

Dining area ya Nufa wanda aka jere shi da manyan Food Flask ɗin abinci kamar wanda za’ai ƴar ƙaramar walima ya Kuma shafa kanshi yana Cigaba da Murmushi yasan aikin Mama ne wannan wadda take Masa Hidimar Cikinsa duk sanda yake Gida ba dare babu rana dan baya yarda da girkin kowa sai nata.

Yayi Bisimillah ya zauna a saman Kujerar Dining Ɗin ya soma Buɗe food flask ɗin waɗan da akai girki kusan kala Uku aciki, kuma kowanne kalar Girkin daze gani daban waɗanda Duka abinci ne Irin namu na gargajiya.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button