Hausa Novels and Stories

Fulani Page 8 Hausa Novel

Sponsored links

Ta fada with smile on her face, sannan ita ma ta saka hannunta aljihu tana wasa da dayar kafarta, shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi

“This time around ina son nai wani abun da zai bawa kowa mamaki as a photographer i want to do something differently like….. ”

Sai kuma ta kasa karasawa ta ware hannayenta kamar mai tunanin abunda zata fada. Kallonta yai kadan ya dauke kai.

“Well i think ki shiga kauye, ki duba wata culture ko yare ki duba wasu addinai na wasu da suke wanda ya sha banban da wanda ake gani sai ki dauka”

Ta wara idonta tana murmushin jindadi.

“Wow shiyasa bana son kai nisa da ni, a duk lokacin da na nemi shawara sai ka sama min mafita”

Murmushi yai mata kamin ya juyo da sauri jin muryar Muhseen.

“Doc me ke sa su yawan zaburar nan ne wai?”

“To Wallahi ba zan iya fada ba, adai rika yi ana hada musu da addu’a especially idan za su kwanta bachi ko idan sun farka, and a daina barinsu a duhu ko barinsu su kadai”

Yana fadar hakan ya mike tsaye ya rufe akwatinsa yana musu sallama, sai Nana ta mike tsaye ta bi bayansa suka fita falon tare, yana saukowa stairs din ta ce.

“Doc yaushe zaka kai ni gurin wannan sister taka wace kace tana kama da ni”

Kallonta kawai yai ya dauke kai yana murmushi be ce mata komai ba har ya sauka ita kuma bata fasa tambayarsa tana masa magiya ba har ya isa gurin motarsa.

“You know what? Sometimes dabi’unku daya da Ya Shattima, sai ku rika yi ma mutum wulakanci idan kun ga yana son abu”

Sai da ya bude motarsa ya saka akwatin sannan ya juyo ya kalleta daga sama har kasa, green lace ne jikinta kanta ba dankwali ta kulle gashin kanta, babu yan yankunne a kunnenta babu makeup a fuskarta amman hakan be hana kyauta fita ba, kallo daya zaka mata ka san cewar jini daya ce ita da Shattima domin kamarsu ta bace kamar an tsaga kara.

“Fine, zan san abun yi ko dai na dauko miki ita na kawo ko kuma na baki address dinta idan kin shiga Abuja ki je ki ganta

“Okay”

Ta fada tana daka tsalle, kamar ance ta daga kai ta gani, sai ta hango Sirleem a sama daga can bangarensu yana kallonsu.

“Idan kai tunani ka kira Ya Shattima ka fada masa sai ya fada min ka ji?”

Tun kamin ya amsa mata tai saurin barin wajen ta koma sashensu.

 

Kai Doc Deen ya daga ya kalli Sirleem wanda ke watsa masa wani irin kallo na rashin kima, murmushi Deen yai ya bude motarsa ya shiga.

Daga backyard din da yake tsaye zuciyarsa take wani irin tafarfasa ganin Nana da Yazeed da yai, ba tun yau ya lura a duk lokacin da Deen ya shigo Masarautar sai ya tsaya yayi magana da Nana yake tafiya.

 

A fusace ya nufi bangaren Ammy zuciyarsa kamar zata fito tsabar kishi, cikin fusata ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Shattima da Muhseen Zainab da Nana zaune a falon, dukan su kallonsa sukai ban da Shattima da yai kamar be san da shi a duniya ba, be damu ba ya soma gabatar da abunda ya kawo shi.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button