Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 142

Sponsored links

Sai da ya dan ja iska kusan minti daya kafin ya nisa. “Al’amarin gaskiya yazo da rudani zance ne koba haka ba oho. Result din sun nuna shi Mahaifinta ne,amma macen ba itace ta haifeta ba”.

“What! Kamar yaya kenan?”.

“Shine na kasa fahimta why Jaddah. Tun a Saudiyya a rikice lissafina yake. A daidaiton kwanakin watan haihuwarta da na yarinyar Mamy dake rubuce kwana uku ne, sannan tambarin da ke nan a ajiye iri dayane da na jikinta, ita waccan ta mutu a randa aka haifi ita Fhareedahn. Sai nake ji kamar akwai abinda ya kamata mu sani, amma idan na auna yiwuwarsa ni a karan kaina sai naji abin yazo ba daidai ba”.

“Kai mi kake tunani akan hakan?”.

Nan ma sai da yay jima kafin ya bata amsa. “Itama Mammy a mata gwajin halitta tare da ita. Kinga muma sai mu samu nutsuwar yarda ba ita bace, ko itance. To amma ya akai ta samu tambarin zuri’armu bayan mahaifinta bashi da alaka da wanna masarautar? Sosai nakejin kaina a rikice a duka abinda nake tunani da fatan ya tabbata”.

“Tabbas al’amarin akwai rudanin, rudanin kuma suna da yawa, dan inhar babu alaka tsakanin wannan yarinya da Arnmarah to tabbas tana da alaka da wani a wannan masarautar kuma dole ne mu sani. Sai dai dabi’un yarinyar na rikita mun lissafi Eshaan. Dan babu abinda ya banbanta da na Ammarah tana a irin shekarunta. Sai dai ni nasan diyar Ammarah ta rasu tunda da hannuna na mata wanka da hadata aka kuma kai ta aka bizne”.

“Kamar yanda na fada miki Jaddah akwai abinda ke boye. Dan da gaske yarinyar nan akwai aljanu a kanta wilhy. Naga alamominsu da yawa tattare da ita, dan a wan lokacin ita kanta aljanar ma nake kallonta”.

Dan murmushin karfin hali Malikat Haseenat tayi, amma a ranta fal yake da rudani… Sun cigaba da tattaunawa har zuwa gabanin magriba sannan ya baro sashen domin zuwa yay shirin massalaci…..

A bangaren Iffah kam data nufi sashensa kai tsaye kitchen ta nufa, inda masu kula da abincinsa ke ta kaikawon lissafin abinda zasu shirya masa na buda baki. Tana shigowa duk suka zube kasa suna kwasar gaisuwa. Hannu kawai ta daga musu, kafin tai zaran bibiyar duk abinda suke shirin yin da kallo. Duk lissafinsu sal da ta wargaza ta shimfida nata, karshe ma ita ta koma shirya abincin da taimakonsu. Wannan al’amari ya matukar basu mamaki kam, dan ko’a tarihin masarautar basu taba jin a inda wata Zawjata- almilk ta shiga kitchen girka abinci ba koda na Shahan-shan ne kuwa. Sai gashi a yau Itfah ta ajye tarihin,

A matukar gajiye suka kammala aikin, tayi tibis da ita saboda a yanayin da take, duk da dama cikin nata nada saukin laulayi da tsurfan abinci. Sannan ita dai bazatace ga wani waje na mata ciwo ba mai jigatarwa. A dining room din ma tana tsaye suka shirya komai, aka kara turaren wuta ko ina ya dauka harami. Bayan duk wucewarsu bedroom nashi ta nufa, ta dinga binsu daya bayan daya tana lekawa har sai da ta shiga a inda ya kwana. Kamar ko yanda tai hasashe ba’a gyarashi ba, tunda ita da kanta ta hutar da amintaccensa tun kan su wuce. Duk da yanda take jin kanta haka tai dauriyar gyarawa, sannan ta shiga toilet din tayo wanka shima bayan ta tsaftacesa Bata da matsalar kaya anan kam tunda tasan tabarsu tunkan su tafi ba, tako shirya cikin wandon jeans 3quater blue da karama roga mara nauyi fara tas, sai hoton heart da akayi babba a gaban rigar. Kayan sun mata kyau. Tana barbaza gashinta da haushi na rashin son a taba mata shi ya shigo dakin da sallama. Dan turus yayi yana kallonta irin na rashin tsammani. Dan a yanzu haka da yake shigowarnan da ita a ransa ya shigo, kewarta yake ji sosai, dan duk yau bai ganta ba, rabonsa da ita tun daren jiya da ya kai mata ziyarar sirri sashenta.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button