Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 28

Sponsored links

Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faɗin, “Ranki ya daɗe ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”.

“Karki damu zanyi da kaina”.

Ta faɗa tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta ɗauke yake da addu’a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya ƙafa cikin toilet ɗin sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu’a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta ƙarasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da ɗazun, dan yanzu an ƙawatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie ɗin. Sai wasu nau’inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taƙi aminta da hakan, atake ta dinga ɗaga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma….

Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa, sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.

Knocking ƙofar da neman izinin shigowa ya sakata ɗaga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a ƙasa, tun’a bakin ƙofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waɗan nan mata”. Ta ƙare maganar da nuna bayanta.

Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai ɗan shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.

Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana ƙasa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saɓawa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.

Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana ɗazun bane.

“Dan ALLAH ku miƙe”.

Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.

Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta

Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saƙonta kamar haka….

Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buƙatar cin komai nikam Mama”.

 

Tamkar hadima Diwa zatai kuka, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Ki gafarceni ranki ya daɗe. Wannan suna bai dace da niba, jinsa a harshenki zai tabbatar da hukunci mai tsanani a gareni. Hakama rashin cin abincinki a yanzu”.

 

(Ya rabba).

 

Iffah ta ambata a zuciyarta cike da takaici dajin sake tsanar Tajwar Eshaan dama duk mai faɗa aji na masarautar. Bata sake magana ba ta miƙe suka fito da hadima Diwa. Dan matan da suka mata kwalliya tuni sun fice su. Babu kowa a ƙaramin falon da Diwa tai mata jagora, inda aka shirya abinci kala-kala kai kace su goma zasu cisa. Ita a rantama tunani tai ko tare da Tajwar Eshaan ɗinne ma. Sai da taga har takai zaune Diwa na ƙoƙarin fara haɗa mata abincin ta tabbatar domin ita kawai akayi kenan. Komai batace ba, har Diwa ta gama buɗe abincin duka alamar taga wanda take buƙata kenan. Komai kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, da ga ƙarshe ta nuna mata dafaffiyar madara kaɗai. Diwa tai jimm kamar mai tunani, sai kuma ta saci kallon Iffah ɗin tai saurin maida kanta ƙasa. Iffah da duk ke kallonta ta ƙasan ido ta cigaba da nazarinta harta kammala zuba mata madarar. Gabanta tazo ta ajiye, harta yunƙura zata miƙe ta dakatar da ita.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button