Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 40

Sponsored links

Mami sama ta haura bedroom dinta,yaran gaba Daya Suka shiga Nasira da Hamra ta Fara Kora tace kuje kuyi Assignment dinku ayi Sallah Kuma,Sultana ta kalla tace kije kiyi Sallah ki shiga kitchen kiyi girki tace to ta wuce shi kuwa Autan nasu sarkin ball ya wuce dakinsa tuni,Nawwar kwanciya yayi a gadon Mami ita Kuma tana zaune a gefe a hankali tace wacece? Nawwar yace Mami ba fa wata bace,bana son karya me yasa baka ji Nawwar me yasa kake son sani a masifar mutananne? tunda kasan halinsu Kawai kabi umarni a zauna lafiya,Mikewa yayi ya zauna yace Mami kin san fa tsarin Allah dole haka rayuwarka zata bi,Kuma wlh ni nayi Niyyar taimakonta bazan fasa ba,Ido Mami ta zaro tace sonta kake Yi? da sauri yace haba Mami so Kuma Allah ya kiyaye bata layin Kalar matan Dana ke son aure ma,ni da nake son Ustaziya kullum a hijab Yar Shuru Shuru saliha bana son mace Yar duniya,nafi son me addini da hankali, Murmushi Mami tayi tare da cewa Allah ya baka to,yace Ameen,to fada min tunda kace ba sonta kake Yi ba me zakayi ka taimaketa Kuma wacece ita? yace ni so nake Kawai ta sanadina ta shiryu yanzu dalilin kawota gidana so nake na raineta na bata tarbiyya sannan na aurar da ita,au ashe yarinya ce ma shekarunta Nawa? Mami ta tambaya,yace 22yrs take,dariya Mami tayi tace Dan Allah Nawwar bana son Wasa 22yrs sabo da rainin hankalinka kace Wai zaka raineta ka bata tarbiyya ka aurar da ita,to ki bari Mana kiji labarinta Mami ba kya cin ribar zance

Kunne Mami ta Miko Masa tace to Ina ji,Murmushi yayi yace to ki daina kallona ma kunyarki nake ji,yau kuma,dariya yayi yace I’m serious,Ina ji,yace Kinga Mami bana boye Miki Abu karki ce nayi rashin kunya, lokacin Sabreen tana min wulakanci Ina nemanta bata yarda ko naje na iske tayi bacci Kuma baza ta tashi ba,lallai maganin Iyamami yayi aiki,idonsa ya rufe Wai kunyar Maminsa yake ji,tace uhum Ina ji,shine naji haushi na gaji Kuma a lokaci Ina cikin yanayi na bukata,Mami tace Allah sarki My son Sannu,dariya ya sake saki yace Mami kunyarki fa nake ji,to na daina Ina jinka,yaci gaba sai nace bari ma na fara Neman Mata na dinga bin titi shine na ganta,a lokacin ta Yi maka ka dakko ta ko? Mami ta tambaya yace ae,Amma ba abinda ya faru banyi komai ba,Mami Hannu ta daga sama tare da furta ya Rabbi na gode maka Ina Addua Inshaallah yarona bazai lalace ba na sani,daga nan ya bawa Mami labarina kaf da komai har labarina dana bashi cewar Ni Yar tsintuwa ce da labarin Dagaci inda na taso,Mami tana gama ji tace ya sunanta? Rabiah,tace duniya kenan idan kaji halin da wani ke ciki sai ka godewa Allah Kai.

Abinda mutum zai Fara godewa Allah akai da aka Yi auren sunna aka haife shi ya taso cikin asali da dangi,idan aka jefar da Kai ko akasi yasa kazo a Dan tsuntuwa baka San kowa ba shike nan Kai baka da asali da nasaba,Babu dangi bare uwa da uba baka San kowa ba a duniya sai Kai kadai wannan kadai ya Isa a tausayawa yaran tsuntuwa da Wanda ke gidan marayu Allah sarki kaga rashin iyaye da dangi shi ya taba wannan yarinya da ace ta fada Hannu na gari da shikenan, idan aka samu akasi baka fada Hannun na gari ba to fa ka shiga Uku,a wannan Zamanin wa Yana zina da kanwa,Kani yayi da yayarsa,kanin uba ya Nemo Yar Kaninsa ko Yar yayansa ana samu uba me Neman yarsa to bare mariki Dagaci Wanda ya rike yarinya ganin bata da kowa irinsu Kuma Allah Yana musu baiwa da ba kowa ke samu ba sabo da Allah baya hadawa mutum biyu

Wannan marikin nata yaci Amana matuka Kuma na tausaya mata,yanzu kaga Wanda ya riketa yaci amanarta ya koreta amma karuwai sun karbeta har fada suke akanta suna daukar Mata fansa,suna kiranta da Yar uwarsu su basu kyamaceta ba Zama ya hadasu na banza Amma sun dauki kansu Yan uwan juna ne,ga masu hankali Wanda basa shashanci sun tsani junansu Kuma suna Yan Uwa musulmai,wani ya taba musu ita sunzo sun daukar Mata fansa Allahu Akbar,kaima gashi Allah yasa maka ita a ranka,a’a Mami nifa ba so ne ba Kawai naga ta lalace ne da yawa shi yasa nake kokarin taimaka mata,Mami tace ka taimaketa da duk abinda zaka iya da karfinka da dukiyarka ka taimaka mata amma kayi da iyawa sabo da mahaifinka idan ya gane Kuna tare zai dauki matakin da baka zato kasan halinsa ita Kuma matarka bata da hankali ka sani Sarai zata sake fada musu,Amma yau Zan bika naje na ganta ashe itace Hamra take cewa kazo da wata ziza kyakyawa Sam bata Yi Kalar Kauye ba,yanzu kaje kayi Sallah in yaso sai muci abinci muje,no Mami bazanci abinci ba nasan ta dafa yanzu Yarinyar fa tana da Yar biyayya abinda nace tana Yi she is so caring, Sabreen bata bani abinci tunda na aureta naci banci ba babu ruwanta amma ita har rokona take yi sai naci dole,Mami kin gani har durkusawa fa,a haka tasan idan Ina Fushi kiji dan Allah dan lokaci kadan ta karance ni she is so brilliant,Mami tace kaji Yar baiwa Kudirar Allah,yace dama sunanta ne Kuwa Kamar kin sani Miracle ake ce Mata,ya sake furtawa, Mami ki tashi kiyi Sallah tace to ko bakya Yi yau ne? Slifas din dake kafarta ta dauka tare da jefa Masa ya fita da gudu,Tsaki Mami taja tace kaji min yaro dan Allah Kai yaran zamani Allah ya shirya ta kwanta Kuma bata Sallar Kamar ya sani.bai samu Sallah ba tasa yayi ya dawo gida a Hanya Suka hadu da Iyamami ta fito daga wajen danta tace au hararata kake Yi Nawwar gaba kake dani ko,bai kulata ba cikin takunsa ya shiga sashen Maminsa ya ganta a main Palo suna cin abinci fuskar Mami ya kalla ya ganta da kwalliyarta alamun ba a sa ruwan Alwala ba,sake lekawa yayi tace lafiya wai,

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button