Hausa Novels and Stories

Ya Fita Zakka Hausa Novel Complete

Sponsored links

_____________ Maryam ki kawo mana abincin mana zan fita mun soma makara ya fada cikin fada……..gani Nan fitowa na gama hada wa Kayi hakuri ta fada tana fitowa daga kitchen cikin sauri kamar zata kifa,, kuyi hakuri zan saka ku makara ba laifina bane gas din ne ya kare sai Dana hada dayan tukkuna na karasa girk…..kiyi mana shuru malama in Banda rashin sanin darajar ilimi ba abinda kika iya shiyasa kike bata mana lokaci Koh kin dauka kowa irinki ne Wanda baiyi karatu ba jahila kawai mijinta(Saminu) ya fada cikin zafin Rai tare da fara cin breakfast…..ita kuwa Maryam Koh a jikinta saboda inda sabo ta Saba da halin mijin nata da dukkan yan gidan shiyassa ma bataji haushi bah,hasali mah kawai cewa tayi Afuwan Mai gidana bari na koma kitchen na karasa ayuka na…Inda ya kamaceki kenan cewar Saminu…..Ta tafi cikin sauri sauri ta karasa aikin kitchen din.

Bayan ta kamalla aikin ne ta fito taga har kowa ya kama gabansa,Yarta ta tafi makaranta,Babansu Kuma ya fita aiki ba sallama saboda dan laifin da tayi na lattin breakfast,,,,Basuda uzuri Sam idan ta aikata laifi cin mutunci suke mata kamar yar aiki,,,Wanka tayi ta shirya ta fito ta kwankwasa daki Mama(uwar mijinta)……… Shigo aka bata amsa,Ta shiga tana cewa Mama barka da hutawa dama na gama ne zan tafi kasuwa shine na zo ki bani kudin kafin lokaci ya kure min ,kwafa Mama tayi kafin ta nuna mata gaban madubi taje ta dauka,Fitowa nayi cikin sauri saboda lokaci… Koh Karin kumallon banyi ba saboda bala’i aikin gidan Dana yan gidan ba Mai tausaya min a gidan Koh a cikin Yara na,, In ba Samar ba sauran duk ji suke dama bani na haifesu bah saboda tsanata da sukayi……..Samar ne ya tareni Yana cewa Momma kawo kudin inje kasuwar ke Kuma ki ci breakfast kafin na dawo naga yau Koh arzikin breakfast din Baki samu ba,Samar ka bari naje Kai ba makaranta zakaje ba , A’a Momma yau lecture din azahar ce Dani bani kawai ya karbe kudin da takardar hannunta Yana cewa sai na dawo…..Murmushi na saki na Jin dadin yadda Samar din yake kyautata mini a Koh Wani lokaci, Allah ya Maka albarka a dukkan lamuranka ta fada cikin Jin Dadi,zuwa tayi kitchen don tayi break din kafin ya dawo

.Saminu Yayi kwafa Yana zaune a wajen cin abincin company dinsu shida sauran workers dinsu bayan anyi Break saboda kowa yayi sallah tare da cin abincin na tsawon 1hr.,Wata kwafar ya Kara na kusa dashi yace haba Saminu ka damemu mana meke faruwa ne,,, cikin bacin Rai yace wlh matata nake ta kira bata dauka ba,shine zaka damemu ta yuwu tana aiki wayar bata hannunta ka kira Wani a gidan mana a bata wayar,juya akalar Kiran yayi a wayar Mama bugu 2 ta dauka tare da amsa Sallamar sa ,,,Ya aiki fatan komai lfy ko. Eh Mama inata kira Maryam bata dauka ba Koh tana kusa, Eh gata chan bari na bata wayar Mama ta tashi ta nufi inda Maryam ke gyaran wake..Gashi ta fada tare da Mika mata wayar kallon screen din wayar tayi taga mijinta ne gaba sai daya Fadi ta dake tayi sallama ya amsa cikin fada wai ke wace irin mutum ce da bazaki dauki wayar mutum ba indan Yana kiranki,, kayi hakuri ta katseshi,wayar tana daki ne Ina waje ta fada cikin rawar murya ,,,,Kiyi yadda kike so Maryam ke ba ilimi ba sai tarin kayan haushi wlh na tsani halinki na jahilci wlh ….sunkuyar da kanta tayi hawaye na zubo mata kusan kullum sai ta zubar da hawaye saboda mijinta akan rashin ilimin dayake cewa batada shi Wanda gwargwado itama tayi iya nata tunda ta sauke Alqurani Mai girma Kuma tayi primary kafin ta tsaya saboda wasu dalilai na rayuwa,,,,,Kashe wayar yayi ba tare da ya Fadi dalilin Kiran nashi ba Jin tana kuka…….

 

 

 

Asalin Maryam yar

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button