Hausa Novels and Stories

The Sexy Boss 4

Sponsored links

Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba… Regular group ₦300…Vip

 

group₦500… Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*

*D*

 

 

 

 

 

*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba… Regular group ₦300…Vip group₦500… Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*

Kuka Umaima ta juma tana yin shi mai ban tausayi na narkar da zuciya , a yau ta gama nadamar Son kuɗin ta ,wanda duk son ka dasu wata rana dole zaka mutu ka bar su , a yau gashi ta jefa rayuwar ta cikin watangariri , tasa rayuka da zukata da dama cikin tashin hankali ,akan son ranta kawai . Kuka take tana ƙarawa har da ƙyaƙyatawa kana ta ɗaga hannayen ta biyu sama tana Addu’oi ,don Muryar ta baya fita saboda tsaban sheƙewa da maƙoshun ta yayi don kuka . Kusan awa biyu ta ɓata bata ko iya motsi ,jin ta take ta zama kaman wata konho fiyau take jin kan ta ,kaman a iska . Tunani take ta ina zata iya miƙewa ma tsaye ,don tsoron hakan take ji , kasantuwar ji da take kaman a iska take ,babu komai da take ji mai nauyi a jikin ta . Ƙafarta ta motsa tana ƙoƙarin saukewa daga saman gadon zuwa ƙasan tiles Nan ta Saki wani irin azabtaccen kuka ,na wahala ,wayyo Umma ,Hajiya Hajiya na shiga uku ya gama da rayuwa ta.! ALLAH ya isa na mugu azzalumi , wallahi sai ka gani Inshaallh “. Ta ƙare maganan kuka na cin ƙarfin ta . A haka tana kuka take motsa ƙafan kaman wanda yayi mata tsami , sai kuma ta dura a saman ƙafafun nata ,tana fara jan jikin ta tare da rarrafawa ta nufi inda taga ya fito don tafi tunanin nan ne toilet ɗin . Da rarrafawa ta shiga don ta kasa takawa da ƙafafuwan ta a haka ta shiga bathroom ɗin .

 

Sauke ajiyar zuciya tayi ganin komai na wurin fari ne ƙal ,bin ko ina take da kallo , kamin a zuciyar ta tace ” Anya nan Toilet ne kuwa? , Idon ta ne ya sauka akan baf da squater yasa ta girgiza kai a hankali tana faɗin Toilet ne . Tsawon lokaci ta dauka ta rasa ta yanda zata yi amfani da komai ,don tsoron tabawa take ji , a tunanin ta shima kar yazo yana laɓe yana kallon ta itace bata sani ba . Wannan yasa ta juyawa tana komawa inda ta fito , a wannan karon bata nufi gadon ba , Blanket kawai taja tana ƙwanciya a saman sofa cushine tare da lumshe idanun ta da suka sauya daga fari zuwa jajaye . Fuskar ta da idanun ta duk a kumbure suke . A hankali take tuno da rayuwar ta na baya .

 

 

 

Ƙiirrrrr taji motsi kaman na ƙararrawar ƙofa. Cike da mamaki take kallon Shatin Shadow Kaman na wata mace .! A Hankali ta furta mecece wannan ai , dama aƙwai mata a gidan nan . Banza tayi tana komawa tare da lumshe idanun ta , can jin ba’a bata umarnin shiga ba ,yasa Badi’a ɗaga wayar ta tana kirar Sir Umair . Ohk Umaima taji matan tace tana danna wasu nombobi a jikin glss door ɗin sai gashi ya buɗe , cike da natsuwa take takowa zuwa inda Taga Umaima ƙwance , Sunkuyawa tayi a hankali a matsayin ta na Nurse tana dafa saman goshin Umaima da taji shi zafi rau . Sorry dear . Sir Umair ne ya turo Ni ,na duba ki tare da baki magunguna da zai rage maki zugi . Wani irin kallo Umaima ta watsa mata ,tana daga ƙwancen da take. Cigaba da magana Badi’a tayi da cewa ” Yanzu zakiyi iya watsa ruwa ki gasa jikin ki ,ko Ni na taimaka miki?.

 

A matsayin ki na wace kenan? . Umaima tayi maganan tare da muskutawa tana miƙewa daga zaune ,don kirar sunan Umair da akayi nan taji ciwon nata ya tafi mata don haushi da takaici . Cike da rashin fahimta Nurse Badi’a tace ” Eyya Doctor Umair ya turo Ni. Ga lunches ɗin ki can ,idan nayi maki allurai sai kici abinci ki ƙwanta. Ke baiwar Allah tattara ki fita ki bani wuri. Idan kuma kin ƙi duk abun da nayi maki ,ki sani ki kuka da kanki. Ki koma ki ce masa Ni Umaima nace ” In shi ya isa yazo yayi mun duk abun da kika lissafa zaki mun ,ina jiran shi ,fita ki bani wuri…… Tayi maganan a tsawa ce ,wanda yasa cikin sauri Nurse Badi’a ta aje mata basket ɗin tana cewa ” Ohk ma”. Ɗaukar ƴar box ɗin ta tayi cikin sauri tana fichewa daga Bedroom din , a zuciyar ta tana tunanin wacece Umaima? Kodai Umair yayi aure ne dama? Ko kuma already yana da matar sa ce ,sune basu taɓa sani ba.

 

 

 

 

 

Bayan Nurse Badi’a ta fita ne Umaima ta kalli Basket din dake shaƙe da different types na dishes kala kala , ƙamshi duk ya cika ta , amma bakin ta ba dadi ,wani irin ɗaci ma takeji . Ƙwallah ne ya ciko idanun ta ,tuno da ada baya yanda take ,cin abinci kaman ita ce tayi kan ta . Kullum a haka take ,bata ma iya sana’a indai bana ci bane . Sauke ajiyar zuciya tayi tana tuno da malaman Maths ɗin su , da tana shigowa idon ta akan Umaima yake , don tasan a tauna take kullum ,nan cike da masifa zata ce fiddo da abun bakin ki. Don dole Umaima zata fiddo da komeye take ci ,ta wurgar ta Window ,sannan malaman zata rabu da ita . Allah sarki Malama Ko tana ina Oho .

 

A hankali take takowa tare da shigowa office din Sir Umair ,Wanda Jin ƙamshin Ru’aifa kaɗai yasa shi saurin ɗagowa don yasan tabbas yayi sabuwar baƙuwa . Zama tayi tana bin sa da kallo ido cikin ido ,duda shima bai sauke nasa tsayayyun idanun ba . Sunana Ru’aifat.! Ehemm?? Yayi maganan yana maida hankalin sa sosai akan ta. Gyara zama Ru’aifa tayi tana kallon sa tare da sakin masa wani irin murmushi na ƴan duniya tana ciza laɓɓan ta na ƙasa tare da cewa ” i hope ka fahimci inda na nufa. Murmushi yayi mata hushiryar sa na bayyana ,yana sa hannun sa tare da shafa sajen fuskar sa . Lumshe idon ta tayi da take ƙara ƙankantasu a dole ga Sexy eyes tana gyara zaman ta. Gani tayi Umair yakai hannun sa tare da ɗaukar wani dan Remote Yana latsawa . Sai ga security ya shigo . Sir”. Yace tare da maida hannun sa baya . Fitar mun da ita . Ke tashi ki bani wuri. Cikin sauri Ru’aifa ta ɗago tana kallon sa . First in her history ,tazo wurin namiji ya koreta ya nuna baya buƙatar ta . Wani irin ciza yatsa tayi na takaici zufa na karyo mata ,a lokaci guda idon ta yayi jah. Kar ka ƙara barin ko wa ya shigo ina buƙatar hutu. Ohk sir. Security n yayi maganan tare da shirin tasa Ru’aifa .

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button