Hausa Novels and Stories

Sanadin Zane 5-6

Sponsored links

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

 

 

Yace”innalilahi wa’ina ilahy raji’un na gan ta kaina Ni kabiru yau sunana gawa na Shiga uku ban lalace ba ya Allah ka fiddani”

 

 

 

Kallon bakinsa take da hanun tayi me alaman what?”

 

 

 

Ya girgiza Kai,kallon jibrin tayi ta Fara me yarensu na kurame da yike ya iya sosai Dan special education ya karanta anan c o e ya iya sosaiĀ  Kallon kawu yayi dariya na niman sub’uce me kawu yace”kayiwa annabi karka fad’a mata kasan kurma Nan mahaukaciya ce yanzu sai ta hanani sukuni a gidan ta kullaceni na shekaru kafa santa Ni wallahi da a ce Maryam ta fad’a min abinci toh me zai kaini gigin tabawa ai gomma yunwa ta kasheni da inyi kuskure cinye Mata ab noinci Ni kabiru

Lura da Kamar magiya yake ta karasa gun ummi dake Duke tana kokarin hade wutarta da yike icen ya jike abinka da damina sai wahalal da ita yake yanzu ta samu Roba ta saka wutan ya tashi d’agowa tayi tana kallon fannah a kullum in ta kalli fannah tausayinta ne ke lullubeta Dan tasan irin rayuwar da marigayiya mahaifiyarta tayi kafin ta bar duniya wanan lalura cuta ce Mai girma shiyasa Bata kaunar abinda zai tabata

 

 

 

Nuna kawu tayi da yatsa ummi tasan halinta Bata tsaya Jan magana ba ta Kai hannun bakinta tana Mata alama da kawu ya cinye Miki abinci….abinci Amma karki damu Zan girki wani yanzu”ummi tana maganane tana Mata demonstrating

 

 

 

Fannah da yunwa takeji da k’yar ta karaso gida cikin gurnani da b’acin Rai sai uhhmmmm kake ji alamun matsifa ke cinta sai nuna shi take tana wani irin huci

Ba abinda kawu yake sai salati dan fushine da ita na tashin hankali gata da shegiyar kwadayi sai uban rowa in kana son ka gan b’acin ranta ka ci Mata abinta

 

 

 

Beyi aune ba ya gan ta jawo icen dake wuta sai hayaki yake

 

Idanunta a rufe tayi kansa Allah ya kiyaye yayi saurin dukawa jikinshi sai rawa yakeyi sai salati yake ganin tayi kansa ya mike da gudu yayi cikin d’akin ummi da ko kallonsu batayi ba dan inda sabo ta Saba

 

 

 

Ai da kurma ta Fara bala’i Saida ta hargitse lissafin mutanen anguwa bala’i take ana Bata hakuri Dan Saida ma ta sauke ruwan tuwon ummi ta jikar wutan ummi ko ta koma gefe ta samu wuri ta zauna,sai Yan anguwa ne ke fitowa suna bata hakuri

 

Saida hafsat ta dawo ta siya Mata coke da biredi

Cikin lallashi hafsat ta d’auko Mata kujera ta zauna ta Fara mata alaman ta kwantar da hankalinta zata girka Mata abinci me Dadi

 

 

 

Haushi ya dibeta ga magana na cinta a Rai ba hanya fiddashi sai kawai ta fashe da wani irin kuka

 

 

 

A lokaci d’aya mutanen dake tsaye kanta Dan in ta Fara kamar me iska Suka sauke ajiyar zuciya Dan kowa yasan in har tayi kuka ta sauko kenan dan kamar me iska haka take Abu in ranta ya b’ace

 

Kallon hafsat tayi tana yagan biredi da Coca-Cola idanunta yayi jazur saboda b’acin rai

Kallon hafsat tayi tana yagan biredi da Coca-Cola idanunta yayi jazur saboda b’acin rai

 

 

 

Hafsat ta fito da indomie a jaka tace”Sha cock indomie yanzu yanzu Zan dafa Miki

 

 

 

Murmushi tayi ta jingina da bango sai ta saci kallon ummi ta gan ummi ko kallonsu batayi ba sai kawai ta cigaba da yagar biredinta

 

 

 

Kawu ko har uwar d’aka ummi ya shiga ya kulle duk wanan hayaniyar Yana jinshi yaki fitowa

 

 

 

Ummi ce ta mike ta shige daki ta Fara bugawa tana cewa”ai sai ka bude malam Zan shiga d’aki Ina da uzuri

 

Dan budewa yayi ya leko Kai yace”ta huce ne Maryam”

Wani kallo tayi me sai ya fito Yana wani cika Yana batsewa

 

 

 

Ratsata yayi ya fito ya tarar da hafsat ta girka Mata indomie ana juyewa a plate sai turiri yake

 

 

 

Kallon kurma yake harda had’iye miyau ya zauna daga kofar ummi Yana kallo,hafsat na soya kwai kurma ta mike ta Zo ta d’au plate din indomie din da zafi yayi ta kaiwa Baki har aka saka Mata kwai

 

 

 

Kawu ya gyara Zama tare da kishingid’a a bango

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button