Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 15 Hausa Novel

Sponsored links

Khalil ya koma baya yana kallonta, still taki barin wajen sai ma wayarta da ta hau dannawa xata kira Aliyu taji ko ya karaso layin, kawai ya bangajeta ya wuce ciki, xaro ido tayi lkci daya ta riko rigarsa a fusace ta cakumo kwalarsa tace “Are you mad?? ni xaka bangaje ka wuce? baka da hankali ne ko ka fara shaye shaye?” Yana kallonta straight in the eyes yace “Irin wanda kike sha?” Bai bari ta gama digesting abinda ya fada ba ya fixge hannunta daga rigarsa ya juya ya bar wajen yana tafiya majestically, baki bude ta bi sa da kallo, irin wanda take sha??

 

Me yake nufi kenan?? Kallon wayarta da ya fara ring a hannunta tayi ganin Aliyu ne, ta daga a hankali tace “Ina ji” yace “Gani kofar gida….” Leka gate tayi taga yayi parking a kusa da gidan dake kallon nasu, ta fita gate din, duk yanda ta so ta sake fuskarta kasa yin hakan tayi don abinda khalil ya fada mata yayi mugun tsaya mata a rai, ta nufi motar, su Aminu suka bi ta da kallo, Aliyu ya sauke glass dinsa yana kallonta, ta kirkiri murmushi tace “Sannu da xuwa” Sai a sannan ta lura ba shi kadai bane a motar tare yake da abokinsa Mujahid, Mujahid yace “Madam ya gari” Tana murmushi tace “MB, ya kwana biyu?” Yace “Alhmdlh Nihad, ya karatu” Tace “Alhmdlh, sannun ku da xuwa” Ta kalli Aliyu dake kallonta tace “Bismillah mu shiga ciki” Yana kallon masu gadi yace “driver din ne can a xaune?” Ta girgiza kai tace “Ya shiga ciki” Bude motar Aliyu yayi ya sauko, Mujahid ma ya sauko, tayi leading dinsu xuwa cikin gidan, Aminu ya dinga kallonsu ta side eye, tun daga takalman kafarsu, kayan jikinsu, agogon wrist dinsu, da hula xaka san rich kids ne, su ne elite… tuni kamshin turarensu ya baxa tun daga bakin gate har cikin compound din, in dai kyau ne kam a wajen Aliyu ba a cewa komai sai dai kawai he is black! Fine black. Nihad dai na gaba suna baya, ta kai su har parlon baƙin Abbanta, the parlor was cool and smelling so nyc sbda AC da ta bari a kunne tun daxu, bayan sun xauna, ita ma ta xauna saman kujera ta gaishesu gaba daya, suka amsa tana Murmushi tace “Bari in kawo maku ruwa” Aliyu ya shafa kansa yace “With food, Kinsan ko lunch ba mu yi daga Abuja ba” Lkci daya jikinta yayi sanyi ta dai saki murmushi tace “Ohk, let me get the water first” Fita tayi daga parlon, she was so confused, bata san me xata yi ba, to ko order din abinci xata yi kawai ta juye masu a plate ta kai masu, but that might take a long time kafin ma abincin ya iso, tana shiga main parlor bata ga kowa ba, ta nufi kitchen jiki ba kwari, Umma ta gani tsaye a bakin kofa tana cewa “Ni dama idan da an bi ta nawa a gidan nan tuntuni da an sallameta, babu dama ka aiketa yanda kasan ta tafi da pillow da katifa, idan kayi magana ace ka fiye takura ka fiye tsanani, haka Farooq ke ce min, ko kema nasan haka kike gani, amma ba haka bane dole sai mutum yana yi yana jan ido, to ai gwara da ta guma ma kowa yau…”

 

Umma ta juya ganin Nihad tace “Kin shigo da su Daughter?” Nihad kamar xata yi kuka tace “Umma abinci fa xa su ci wai, ni yanxu ya xan yi don girman Allah?” Umma tace “Atoh ai dama baxa mu bar su haka ba, dole xa a samu alternative….” Nihad ta leka kitchen din ta ga Mumy tsaye bakin gas tana hada ingredients din Chinese fried rice da yake akwai left over cooked rice a kitchen din, sannan ga kaza a gefe tana sarrafa shi, farin ciki ne ya rufe Nihad, Umma tace “Ai ban ta6a ganin tsinanniyar yarinya irin Hafsah ba, ko kare ya shafa mata lafiya a yawo, babu dama ka aiketa ko nan da nan ne sai ta bata maka rai” Mumy dai aikinta kawai take, Nihad ta karasa kitchen din ta dau abinda xata daura masu drinks, ta dau glass cups tana kallon Mumy, a hankali tace “Mumy nagode” Ko kallonta Mumy bata yi ba, sum sum ta juya ta bude fridge ta debi drinks din ta daura a tray ta fita kitchen din, tana ajiye masu a parlor Aliyu yace “Xa mu gaisa da su Mumy yanxu ko?” Tace “Toh bari in sanar masu” Mikewa tayi ta fita, suka dau lemo da cup, tana komawa kitchen ta kalli Umma tace “Umma wai xa ku gaisa” Umma tace “Toh su shigo nan parlon, ai a shirye muke” Juyawa Nihad tayi ta koma, Umma tace “Ai ba sai mun wani yafa mayafi kamar wasu tsofaffi Maryam, suna shigowa parlon sai mu fita kawai” Mumy dai tayi Murmushi tace “Gaskiya ne” Umma ta karasa bakin gas din tace “Ko da yake ke nasan sai kice baxa ki fita haka ba sai da Hijab, bari in dinga duba girkin ki dauko Hijab din naki a sama” Mumy tace “Xai iya yiwuwa sun shigo parlon yanxu ai ko” tana fadin haka ta tafi inda ta ajiye wayarta a kitchen din ta dauka tayi dialing number kanwarta Jamila, tana dagawa tace “Jamila sauko min da Hijab dina sai ki taho da snacks din” Tana fadin haka ta katse wayar, taje ta ci gaba da abinda take, sai ga Nihad ta dawo tace “Umma suna parlon” Umma tace “Toh bari mu je a gaisa”

 

Umma na fita kitchen din jamila ta shigo da hijab din Mumy, Mumy ta amsa ta saka, Umma na shiga parlon ta samesu xaune su biyu saman lallausan Carpet dake tsakar parlon, Umma ta xauna saman kujera tana masu sannu da xuwa, suka gaisheta da ladabi ta amsa tace “Fatan kun xo lafiya ya tsofaffin?” Suka amsa mata da “Alhamdulillah” Umma tace “Toh madallah, sannunku da xuwa… Tana ta cewa xaka zo yau dai gashi Allah yayi” Mumy ta fito suka gaisa a tsattsaye ta juya ta koma kitchen din, Umma na Murmushi tace “Toh wanene surukin namu cikin ku” Mujahid ya nuna Aliyu yace “Shine Aliyu” Umma na kare masa kallo tace “Madallah, maa sha Allah, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi Aliyu, Allah yasa ayi da mu, ya nuna mana wannan lokaci lafiya” Suka amsa da “Ameen” Umma tace “Kai ne ɗan Janar na fari kenan ko?” Yayi Murmushi yace “Ehh haka ne” Umma tace “Allah sarki, Baabarka ce uwargida amma?” Jamila dake can bakin kofar kitchen tana juyo conversation din da Umma ke yi da su ta saki baki da mamaki tana saurara, Aliyu yace “Aa ba ita bace” Umma tace “Ikon Allah, ta biyu ce kenan, dama kam ance matansa biyu ashe da gaske ne, Allah sarki, amma kai ne dan sa namiji babba ko kana da yayyi maza?” Ya girgiza kai yace “Kanana ne kannena maza” Umma tace “Maa sha Allah, abu yayi kyau wllh, amma ai duk ku kan zo hutu kano” Yace “Ehh muna xuwa lokaci lokaci” Tace “Madallah, ita uwar gidan bata da namiji ko daya kenan?” Ya girgiza kai yace “Mata ne” Umma tace “Ikon Allah, matan har nawa?” Aliyu ya daga kai ya kalleta for the first time, haka Mujahid ma kallonta yake ta yi, Aliyu yace “Su uku” Umma tace “Wayyo, wato dai Ummarka ita ce me ‘ya ya da yawa a gidan, toh ai hakan da kyau” Farooq na tsaye can bakin stairs ya kasa karasowa jin interrogation din da Mum dinsa ke masu, Jamila ta shiga kitchen a fusace tana kallo Nihad dake hada inda xa a sa masu abinci tace “Ke, maza tafi kice masu ga abinci can xa a kai su tashi daga parlon nan haka” Nihad tace “Toh” Daga haka ta fita daga kitchen din xuwa main parlor, Umma tace “Amma ai kai ba kasar nan kayi karatu ba ko?” Yace “Eh” Umma tace “Yauwa ko da na ji, ka kama aiki dai” Ya sauke kansa yace “Eh” Tace “Aa abu yayi kyau, wani aikin kake yi?”

 

A takaice Aliyu yace “Business” Umma yace “Toh Allah ya sa albarka, yaushe xa ka turo magabatan naka kenan, in ji dai ba yanxu ba ko?” Aliyu yace “Yanda Allah ya tsara” Umma tace “Gaskiya ne, batun aure a hankali ake bin sa ba abu bane na gaggawa, ku kara fahimtar kanku sosai kar ayi gaggawa a lamarin nan, Nihad dai ‘ya ta ce, bata da wata matsala wllh baxan cuceka ba, kuma ina fatan Mahaifiyarka tasan kana nemanta dai ko?” Yace “Eh” Nihad ce ta shigo parlon tana kallonsu tace “Xa a kai abinci can” Umma tace “Eh kwarai kuwa, ga abinci can ku je a kai maku, sannunku da xuwa, Allah yayi maku albarka” Mikewa Aliyu yayi Mujahid ma ya tashi suka koma can daya parlon, Umma na kallon Nihad tayi kasa da murya tace “Ke bandir din daloli ne a aljihunsa wllh na hango” Dariya Nihad tayi, Umma tace “Allah kuwa, kawai ki ce masa wayarki ta samu matsala, su ai kudi abar banxa ce a wajensu….” Aunty Jamila ta kwalo ma Nihad kira ta tafi da sauri, Farooq ya karaso parlon rai a bace yace “Haba Umma, Haba Umma yanxu duk wannan tambayoyin kina matsayin surkarsu kinga ya dace kiyi masu? Me ya kai ki wannan tambayoyin fisabilillah?” Umma ta buda baki da mamaki tace “Wani tambaya nayi da bai dace ba farooq?” Yace “Umma ina ruwanki da ko matan babansa nawa ne, meye na tambayar baabarsa ce ta farko ko ta biyu, meye fa’idar tambayarsa ko a kasar nan yayi karatu kuma wani aiki yake? Ina ruwanki da tambayar ‘ya yan kishiyar baabarsa nawa” Umma ta hade rai ta kunduma masa zagi tace “Ka fita idona in rufe a gidan nan farooq, haka lkcn Kamila komai nayi kace ban iya ba ko bai dace ba, wai shin kai ka haifeni ko ni na haifeka? Laifi ne don nayi bincike insan inda xa mu tura er mu? Meye aibun tambayoyina? Ba neman aure ya xo ba? To kuwa ai dole ayi masa tambayoyi, Ko dama ance maza ne kadai xa su yi bincike banda mata? To wllh ka shiga hankalinka, ba ruwanka da harkana ko lamarina a gidan nan ina sake ja maka kunne” Farooq dai sai kallonta yake, can ya juya a fusace ya bar wajen, Umma ta bi sa da harara, Hafsah ce ta shigo parlon da leda a hannunta, Umma tace “Makira sai yanxu kika ga dama kenan, to kin kyauta kin ji ko? Ki tafi can parlona a sama ki jirani in xo in sameki ki gaya min gidan uban da kika je” Hafsah tace “Zan kai ledar kitchen” Umma tace “Aa wuce da shi sama, xa mu hade da ke a can” Hafsah bata ce komai ba ta wuce sama xuwa bangaren Umma, Nihad ta kai masu abincin da Mumy ta gama hadawa, wani tray kuma ga meat pie, samosa, spring rolls da doughnuts da Aunty Jamila ta kawo bayan Mumy tayi mata waya ta gaya mata tayi ta kawo, da yake tana da ma’aikata cikin kankanin lokaci suka yi suka gama, wani bowl me dauke da apples kusan goma ta kai masu a karshe ta ajiye, sannan tayi serving dinsu abincin.

 

Bayan sun gama cin abincin, Nihad ta shigo parlon tare da Ya farooq, bayan ya gaisa da su ya fita, Mujahid ya mike yana kallon Aliyu yace “Bani makulli in dauko wayata a mota, they might be plenty of calls i missed” Aliyu ya mika masa makullin ya amsa ya fita, Nihad dai kallonsa kawai take, wayarsa ya ciro a aljihu ya shiga gallery bayan few seconds ya mika mata, ta amsa tana kallon screen din wayar, sosai gabanta ya fadi, ta dai yi shiru bata ce komai ba, yace “You promised kin daina dukka ire iren outing din nan, so where did this come from?” Nihad ta marairaice tana kara kallon hoton, 4 weeks ago ne suka je wani babban restaurant da su Naf da Husnah da samarin su, shine aka yi hoton a can, wando ne a jikinta sai crop top me shegen kyau da tsadadden sneakers a kafarta, sannan ta daura baƙin dankwali a kai ta xubo dogon gashinta, su Husnah ma duk ire iren shigar suka yi a hoton… jin tayi shiru Aliyu yace “Why are u quiet?” Ta daga kai ta kallesa a hankali tace “Hoton nan ai ya dade” Yace “Karya kike, this is a recent pix, jiya da daddare Naf ta daura a status na gani nayi saving” Nihad tace “Am serious ba kwanan nan muka yi ba, kuma ai kafin in maka alkawarin daina fita tare da su ne muka yi hoton nan, ka tambayi Naf din ma” Yace “Nihad!!” Shiru tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, yace “Saboda ina sonki da aure ya sa ki ka ga har nake hanaki abubuwan nan da kike, banda haka i have no business with ur life style, quite alright kinsan i have other babes wa enda muke tare da su har yanxu, but ban ta6a daga kai na hana yarinya yin abinda tayi niyya ma rayuwarta ba, ban ta6a hanasu holewarsu yanda suke so ba, but ke saboda intention dina a kanki daban shi yasa nake hanaki duk wannan shiriritar da kike, Upon how wealthy my parents are, baxa su ta6a yarda in kawo masu mace mara kamun kai ince xan aura ba, baxa su ta6a amincewa, kuma ya kamata ki kara yarda yanxu tunda har na tako tun daga Abuja na xo gidanku to da gaske aurenki nake son yi, i will neva do that for any lady, sai sai idan dama ina da wata sabgar da xanyi a kano…. Nihad this should be ur last warning!!!”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button