Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 14

Sponsored links

Tashi tayi tashiga bedroom dinta,ta bude bedside drawer,ta shiga bin car keys din dake wajan da kallo,guda biyu ta zaro ta rufe wajan….. Fitowa tayi taga abdul yayi zuru yana jiran fitowarta,karasowa tayi tace mishi “muje”,jiki na rawa ko ya bita a baya……….. Fita sukayi ta nufi parking lot abdul na biye da ita,juyowa tayi ta kalleshi tace”abunda nakeso dakai shine,karka kara karatu in zaka shiga exam hall”…… Zaro ido yayi cikin tsoro yace “Kai anty nayi karatun ma ya aka kare bare banyi ba”…… Cilla masa daya daga cikin car keys din tayi sannan tace “Nidai nagaya maka,in kaga dama ka dauki shawarata”…. Wani farinciki ne ya lullubesa harda tsugunawa kasa yana mata godiyar jindadi,yes yasan motar yayanshi ce amma muddin yace masa ita ta dauka ta bashi,yasan zance ya kare….. Bata saurareshi ba shige mota kirar Mercedes benz ta tafi……..

Tafe take cikin sabuwar motar data dauka Tana jin music mai dadi,wani nishadi na kamata,ko banza ta haddasa fitina harda saki,ko tausayin mama bataji a ranta ba tinda mama muguwace,kawai sai traffic light ya tsayarda ita,gyara zama tayi tana lalubo niqab dinta a jakarta…..

 

Tinda Dr ya baro gidan alhaji yayi parking a nearest cafe,yashiga yayi ordering coffee,yashiga sha yanajin kamar idan ya koma gidan alhaji yanzu ze ganta,domin zuciyarshi kwatakwata taki amince masa bata gidan…….. Ya dade a zaune,chan kuma ya hakura ya fito,ya nufi motarshi ya shiga yaja…….

 

A daidai traffic light daya tsayar dashi,kawai yaji zuciyarshi na fuzgarshi daya kalli gefe…………..

 

Hmmm ku biyoni dan jin yanda zata kaya tsakani Dr Deen da fatima zainab,ko zasu hadu a traffic??!!😅

 

Tinda aka shiga da Deen emergency likitoci ke kansa,taimakon gaggawa suka bashi ganin yana internal bleeding,iya taimako sun bashi sannan kuma suna expecting farkawarshi anytime soon,amma shiru ba labari,tini Dad da Mom sunzo abuja,Dad sai fada yake akan yayi warning dinshi akan dawowa abuja,amma dake kunnen kashi ne dashi be jiba,toh zeyi maganinshi very soon,ze mishi abinda dole ya zauna guri daya…. Mom dai lallaba dad take tayi,tana kuma bashi shawaran yanda zasu shawo kan abun…… Ansamu komai ya daidaita har anfita dashi daga emergency amma kume be farka ba,mom da dad na zaune a aminity din da aka dawo dashi…….. A hankali Deen ya fara bude idonsa,sai yaji kansa ya sara masa,kokari yayi ya bude ido yana tinanin ina ne nan,chan kuma sai ya tino yarinyar da yake bi a mota,kalle kalle ya dingayi ta ina ze hangota,ganin ya farka dad yayi maza ya kira doctors,taruwa sukayi a kansa daga su dad har doctors din,binsu da kallo daya bayan daya yayi,mamaki ya shigayi ganin mom da dad a tare dashi,a hankali cikin muryar marasa lafiya ya kallesu yace “dan Allah ku fadamin WACECE ITA?”…… Kasa gane me yake magana akai sukayi,sai kawai aka mishi allurar bacci,nan da nan ya koma bacci kuwa……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button