Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 29

Sponsored links

Ya tsinkayi furucin nata yana ƙoƙarin ficewa. Yanzu kam sai da yay murmushin a zuciyarsa da sake jinjina ƙarfin halinta. Bai kuma juya ɗin ba yay tafiyarsa. Ta ɓarauniyar hanyar da ya fito ya koma sashensa, dan dama fita ce ta ɓadda kama. Turus ya ɗanyi da ganin Malikat Haseenat da bai zaton gani a irin wannan lokacin ba, kuma a falonsa da bazai iya tuna sanda ta shigo shi na ƙarshe ba. Basar da yanda take binsa da kallon tuhumar da ya gani a idanunta yay ya ƙarasa takowa gareta. Sai da ya kai zaune ya riƙo hanunta ya sumbata. Sannan ya furta “Idan amintacciya na buƙatar ganin gudan jininta shin ba umarni kawai zata bada ba ya isa gareta”.

 

 

Murmushi ta saki a karo na farko, itama cikin nata salon girmamawar garesa duk da matsayinta kanta ta ɗan rausayar. “Idan uwa ta girmama ɗanta da ke amsa sunan shugabanta laifi ne Hafidi?”.

 

Kansa ya girgiza yana ɗan murmushi a karo na farko. Ta san iya amsar kenan daga garesa. Dan haka cikin rashin nuna damuwa ta cigaba da faɗin, “Fita ce ta sirri, dan idanuna sun kasa rintsawa a wannan daren a dalilin furucin Zawjata-almilk”.

 

Idanunsa ya ɗan motsa, kamar bazaice komai ba sai kuma ya nisa, “Jadda-ti miye abin hana barci a ciki? Faɗin akwai wanda ta ambata bayan mun san da su? ko kuwa furtawarta kasancewar bamu taɓa ji da ga bakin wani ba?. Shirmenta da son kare kanta da ga laifinta ne kawai ya sata furtawa itama, nasan tana da hujja kan wani ba…..”

“Ina bazai yiwu ba Eshaan. Na jima da fahimtar wannan yarinyar nada wasu ɓoyayyun al’amura tattare da ita, sannan tana da ɗabi’ar zama kaifi…..”

(Mai hatsarin gaske ma kuwa, dan tafi duk yanda kike tunaninta Jaddah) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai ya ɗan yamutsa fuska kaɗan, dan kansa ke ciwo. Can ƙasan maƙoshi ya ce, “Yanzu mi kike son ayi?”.

“Karmu matsa mata da son sanin da wa sukai wannan aikin. Kamar yanda tace mu bincika da kammu muyi ƙoƙarin hakan, dan akwai wata hikima a zancen ta na bamu damar mu bincika ɗin”.

“Yanda kikace haka za’ayi Jadda-ti. Sai dai kuma idan bamuyi bincike ba taya za’a yanke mata hukunci? Ni fa ƙara aka kawo min, dolene na hukunta mai laifi ko na wankesa akan gaskiyarsa”.

Murmushi tayi mai ma’anoni da yawa da ita tasan dalilin kayanta. Taja numfashi ta fesar da ƙara damƙe hannunsa cikin nata. “Wannan sune siffofin adalin shugaba. Sai dai inaji a jikina a kwanaki ukun nan daka bada wani abu zai iya faruwa, dan duk masu hannu a ciki a yanzu hankalinsu ba’a kwance yake ba sam. Suna can neman hanyar ɗaukar mataki a kanta kafin cikar kwanaki uku harma da mu kammu”.

 

Idanu ya tsira mata da mamakin jin kalamanta. Amma sai bai iya cewa komai ba. Itama bata sake cewar ba ta sumbaci hannunsa tana mai lumshe idanun da buɗewa alamar sallamar kenan. Shima nasan ya lumshe tare da rissinar da kansa ya buɗe a hankali fuskarsa da ɗan yanayin murmushi sai dai bayin yake ba. Sai dai ta kurema ganinsa sannan ya janye idanunsa da ke binta da kallo. Ya maida bayansa jikin kujera ya maida idanun ya lumshe…

Duk yanda yake son hana tasirin kaikawonta a zuciya hakan ya gagara. Ƙarfin halinta, tsaurin ido da kauɗin zance na matuƙar zaburar da shi. Koda a tsoracan take sak take a zahirinta. Ba mata ba mazan ƙasar ruman gaba ɗaya shakkar masa magana suke kansu tsaye, amma ita tar idonta da muryarta ke fita garesa. Itace ta farko dake iya kallon cikin idonsa ta faɗi magana bayan mahaifinsa, amma ko Malikat Bushirat da Malikat Haseenat bejin tunda ya mallaki hankalin kansa sun taɓa hakan musamman a yanzu da yake matsayin Shahan-shan, suna masa magana da taushin harshe da kuma kimantawa, duk da kasancewar sa ɗa garesu. Amma ita duk da akwai girmamawar tattare da fitar sautinta garesa kai tsaye take babu alamar shakku, bata kuma iya ɓoye abinda ke ranta koda a inda tasan anfi ƙarfi ta ne.

“Fitinanniya”.

Ya furta a hankali kan tausasan lips ɗinsa yana mai miƙewa da wani irin makirin murmushi a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button