Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 179

Sponsored links

Akance a cikin yaya an fidda maka zakka, to tabbas Bushirat ni itace zakkata. Ka bashi Hubba kawai zamuyi alfaharin da ita”) wannan bayani na Abbie ya tayarmu da hankali matuka. Dan ga koshi ga kwanan yunwa ne. Zama nai naita nazarin mafita, dan har wata zuciyar na bani shawarar kashe Hubba dan itace kawai matsalata.Naki karbar wannan shawarar, dan ko yaya ina matukar kaunar yan uwana, Haka na cigaba da saka ido a duk motsinka da na Abbie, sai dai shiru bakayi maganar ga Hubba ba balle iyayenmu mata. Dan duk da mahaifiyarmu ta rasu wajen haihuwar Jasrah bamu taba kukan rashin uwa ba ga matan babanmu, sun rikemu hannu biyu tamkar sune suka haifemu. A cikin dogon nazari dana bama kaina kwana biyu a samo mafita. Ranar na yini cikin farin ciki sosai dan inaji a raina na gama zama matar Shahan-shan. ALLAH kuwa ya yarjemin, dan a randa na gama yanke wanna shawara a bibiyar Akhi da nakeyi da Abbie na samu jin Akhi zai tura sako ga Miran Haysam ibn Abdul-majeed Aliy Qutb na zabin matar da ya nema.Tuni na garzaya na rubuta wasuka mai nutsuwa tare da saka hotunana a ciki da dama na tanada. Dakin Akhi na lallaba batare da sanin kowa ba, nai sa’a kuwa yana wajen karatu dan haka a shiga bincike dakinsa. Na samu nasarar gain hotunan Hubba da ya shirya tura masa cikin jin dadì na kwashesu na ajiye nawa da wasikar nan na sake sabon manne envelope din. Gudun a yanka ta tashi na kone hotunan Hubba a cikin toilet batare da sanin kowa ba…. Kamar yanda Akhi ya fada ya aika sakon Miran Haysam batare da sanin na canja hotuna ba. Kwana biyar tsakani sai ga masu neman aure sunzo. Hankalina ya tashi naita kaikawo da neman hanyar da zanji yaya akai amma ban samu ba. Dole na hakura har bakin suka tafi Abbie da Akhi suka shigo gidan. Cikin muryar damuwa najiyo Abbie na sanarma Ummu cewar maganar da sukayice ta taso, sai dai sabanin Hubba da su suka zaba shi yanzu ya aiko cewar Bushirat, harma sun rasa a ina ya sanni. Kokwanton da suka shiga yasa Akhi tashi da kansa zuwa masarauta dan tabbatar wa. Amma magana daya ce dai Bushirat ya zaba. Babu alamar damuwa akan fuskar Ummu tace ai duk kai da kaya mallakar wuyane ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, dan itama dai batai magana bane kawai amma abin na damunta. Kar ace dan Hubba yarta ce aka tsallakeni aka bata alhalin nice babba. Oho ko dar banji da kalamanta ba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button