Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 11-12

Sponsored links

Nawwar a gurguje ya fito cikin shiri yasha wankan wani danyen yadi milk shara shara,gashinsa yaci gyara na gogaggun matasa kamar wani bature Yana zuba kamshi,agogonsa me azabar tsada yake daurawa yana sakkowa daga steps wani Yaronsa ne ya fito Masa da Yar karamar jakarsa wacce ya shirya kayansa da sauran abin bukata ya wuce Masa da ita ya saka a boot din mota,Sabreen tana dining tana breakfast sanye cikin kayan bacci tana ganinsa ta dauke Kai Wai ita me aji, kallo ma bata isheshi ba,har yanzu bai duba inda ya ajiye kudinsa ba bare yasan ta ebi wasu ba,Zama yayi ya hadawa Kansa tea yana Sha Yana cin chips sai da ya koshi sannan ya dauki wayarsa yace na wuce Kano Ina da meeting a can har na 2weeks,shekeke ta kalleshi ko a dawo lafiya babu tace to Kawai ta mike tare da haurawa sama,baki Nawwar ya tabe ya daga Kiran wani abokinsa Khaleel suna waya Yana fada Masa ya tafi kano,fita yayi ya shiga mota ya kame a baya securities a mota uku suna take Masa baya,gidansu ya fara zuwa tare da yiwa Maminsa sallama sai yaje ya samu Papa Yana gida har dakinsa ya shiga bayan sun gaisa Mama tace kaga dana ga iya wanka ga kyau,Murmushi Nawwar yayi ba shiri,Papa yace ai Yar mu ta dace,Sumarsa Nawwar ya shafa sannan yace Papa dama Kano Zanje

Ina da meeting da wasu turawa sunzo daga Finland akan business dinmu zanyi sati biyu,Papa yace a’a to Allah ya bada sa’a ubangiji ya ida nufi,Mama ta furta Allah ya tsare hanya yace ameen ya mike yace na tafi sabo da jirgi ya musu sallama ya fito direct part din Iyamami ya nufa kakarsa kenan,zaune ya isketa a kujera ta tasa katuwar tv gaba tana kallo tana tauna goro,Dan Nema sai yau aka ga damar zuwar min dama nasan ni ba kaunata kake Yi ba sai kayi sati ban ganka ba auren ma bana Yi na sake ka,Murmushi Nawwar ya saki yace dama ni me zanyi da tsohuwa ga matata sabon jini dama sallama nazo na Miki zanje Kano Ina da wani meeting, Iyamami tace aikin kenan to Allah ya tsare na zaci da matarka zaka tafi ma,ai ba dadewa zanyi ba,to Allah ya bada abinda ake Nema yace ameen tare da zaro kudi da yawa ya bata yace ga kudin cefanenki tunda na bawa Amarya karki ce na zalunce ki,dariya ta dinga Yi tayi godiya ya wuce Suka wuce airport.

Bangaren su Mama Kuwa Yana tafiya Papa yace bar shege ya gama tara Mana mu gaje dukiyar,wani ma yaji cewar Mama.

 

Nawwar yana zuwa Kano wani Yaronsa yazo da mota ya kaishi green palace hotel inda aka sauki turawan kuma a nan hotel din zasuyi meeting din kullum har a Gama,bai ko zauna ba kayansa Kawai ya ajiye yaje inda zasuyi meeting din dama shi ake jira,Yana zuwa suka Fara basu gama ba sai bayan Sallar Isha,wanka yayi da Sallah sannan ya zari motar da aka bar Masa ya fita dan zaga gari sanye cikin farar jallabiya me tsada

Rabi ina sauka a Kano ban San inda nake ba haka na samu wani lungu na fito da yagaggen Hijab dina ja,ya gama fatattakewa haka na saka nace Neman Sadaka yo ai sai anyi Kalar tausayi sosai a kasar nan basa ba da Sadaka sai anga mutum ya kusa mutuwa sabo da wahala,ni Rabi ina maganganuna ina canja kamanni nace gani jajir ai dole na Zama Yar dukununu na nemo gawayi a hanya da kyar na samu na dandaka da dutse na dan shafa kadan a fuskata Kamar me shafa powder nayi wani duhu,hakorana ma duk na goga musu bakin sukayi Kamar sunyi tsatsa in ka kalli Rabi Kamar ba ni ba,tafiya nayi me uban nisa ga rana tayi sosai sai da na samo wata makaranta wacce babu gate ta gomnati ce na shiga na samu saman baranda na ajiye kayana a nan sannan na fito gefen titi tare da shanye hannuna Daya ya dawo Kamar me shanyayyen hannu ina tafiya ina cewa a taimaka min sabo da annabi a taimakeni na samu abinci, na koma dai dai wajen danger inda motoci ke tsayawa jiran a basu hannu su wuce ina bi ta tsakiyar motoci ina a taimakeni sabo da Annabi, dan me Mana ruwa da iska abinci ya gagare mu,wani ya sauke glass zai siyi charger naje wajen ina Alhaji adubi girman Allah Allah ya kaika gida lafiya canjin ishiri ya mika min ni Rabi na karbe ina Allah shi Albarka,matarsa dake Gaban mota tace na tsani almajiran Nan duk su damu mutane wasu ma sunfi ka kudi da gatansu sabo da mutuwar zuciya sai su fito bara,mijin yace ai baka San wa zaka taimakawa ba a haka wasu ne Suka bata wasu,wasu da kike gani dole ce ta sasu bara baki San mene dalili ba.

Na hada uwar zufa sosai amma daga goma sai biyar sai ishirin yinin ranar gaba daya kudin abinci naci dasu zuwa Yamma na koma makarantar inda kayana suke naci sa’a Kuwa lokacin Yan makaranta suna hutu sai na fito wasu gidaje dake kusa da makarantar na lallaba na leka wani gida na talakawa sosai ai Kuwa a zaure na iske wani dan baho karami na dauke shi na gudu tare da komawa makarantar na ebi ruwa a tuka tuka din na duba jakar kayana na dakko sabulun wankina na zaga bayan aji tunda ajujuwan a rufe suke me gadi ma ya tafi hutu abinsa a can a tsorace nayi wanka na canja Kaya sannan na Kara Nemo gawayi na mulke Fuska ta na kwanta a barandar Ina hutawa bacci ya sace ni sai bayan Sallar Isha na farka,a gurguje nayi Alwala tare da Sallah sannan na sake Fitowa cikin dare ko zan dace,ko da na fito ban iya bara ba sai yawo Ina ta kallon birni ko Ina haske Kamar Rana Yan Mata da samari da Yan gayu ana ta lailaya Kan mota gaba Daya kallo ya dauke min hankali Ina ta yawona har nazo bakin wani hamshakin Hotel na tsaya Kawai Ina kallon haduwa motoci sai parking suke wasu a ciki wasu a waje,

.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button