Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 174

Sponsored links

Wanna furici nasa ne yasa kowa fahimtar ba ainahin Iffah’r bace iskokinta ne yau suka bayyana kansu abinda basu taba yi ba, sannan kuma maganar cikin jikinta tabbataccene tunda har shi da kansa ya kirata (MALIKAT). Neman afuwa suka shiga yi, da tsayawa tsaye akan kafafun Iffah’r. Alokacinne Sayeed Fayzul-haq ya yafito Kaka dake tsaye kawai yana murmushi. Sai da ya fara mika qaisuwa ga Shahan-shan shima sannan ya duba Iffah, kamar yanda sukaima Tajwar Eshaan bayani haka shima kakan sukai masa. Kansa kawai ya jinjina da cire jakar hannunsa ya ajiye. Ruwa ya bukata, cikin kankanin lokaci aka kawo masa. Magunguna ya fiddo da yawa ya shiga zubawa a ruwan nan. Wani irin ihu su Banou suka dingayi da rokon yayi hakuri, bama su ishesa kallo ba ya fara dibar ruwan maganin yana watsa musu. Ihu na gaske suka dinga kwallawa da surutai suna girgiza da gunji. Sai da yay musu ligif sannan ya basu umarnin bayani da bakunansu. Biyun sun tabbatar da su ba mutane bane sun rikidane kawai. Kuma a yau din nan suka shigo cikin masarautar bisa umarnin uwa da Iffah ta raunata a dazun. Banou kam mutum ce ita, sai dai akwai aljanun maita tare da ita, irin kusan duk zuri’arsu ke da shi, dan itama cikin zuri’ar uwa take. Cikin galabaita ta shiga fadin tun sanda take tare da su.

“Ni shekarata goma sha tara anan, tun bayan korar uwa da akayi da ga wannan masarauta. Ina daya daga cikin zuriarta da aka kora shekaru masu yawa da ga cikin wannan alkaryar, a da kakanninmu wannan filin masarautar shine garinsu. Amma sanda za’a kafata sai aka tashesu aka canja musu waje. Ransu ya baci matuka da wannan al’amari, dan tunda suka taso anan suka samu iyayensu da kakanni suma, nan kadai suka sani matsayin kasarsu kuma gari, ga abubuwan bautarsu masu tsahon tarihi tsahon shekaru duk an ruguza musu. Dan haka sukaji zafin tashinsu da akai da bata musu wajen bauta da abubuwan bautarsu saboda gina masarauta bayan akwai filaye da yawa da babu kowa a cikinsu miyasa baza ai acan ba. Wannan haushin yasa sukaki zama inda aka basu sukai hijira zuwa cikin jeji. A haka suka cigaba da sabuwar rayuwarsu wadda da kyar suka saba da wajen, sai ya zam duk wanda aka haifa a cikin zuri’ar mu wannan

 

shine labarin da za’a raineka a kansa, da kuma kiyayyar wannan gida. A haka duk muka rayu da burin daukar fansa. Mun dade da shiga jikinku muna muku illa da suffar bokanci, hatta lokacin da kuka samu ambaliyar ruwa a kusan kasar baki daya zuri ‘armu ne suka balle wani yanki na kogin da ke zagaye da ku. Mu bamu taba jingina da ku domin mu taimakeku ba sai dan mu ruguzaku, a haka iyayenmu da kakanninmu suka dinga shudewa. Uwa ta kasance mafi girman hatsabibanci da yin tasiri a al’amuranku a cikin duk wanda suka zo da nufin masu taimako a gareku a cikinmu. Duk da dai akaf zuri’armu daga maye sai matsafi, kuma kowannenmu nada abinda yake yi domin ku. Jajircewar uwa da zamowarta mafi iyawa a kan iyawar kowa cikinmu yasa ta zama shugaba a garemu, kuma ita muke fata da gain ta kusa karbo mana wanna masarauta data kasance tushenmu ta koma tamu. Amma sai abubuwa suka fara canja salo a dalilin tsohuwar can (ta nuna Malikat Haseenat) ta kanainaye komai tana faman rushe duk wahalhalinmu da muke gain saura kiris komai ya kare. Dan haka mukaita kawo mata hare-hare amma bam samu nasara a kanta ba. Ana cikin hakan rana tsaka ma sai ga Uwa mun tsinta a yashe cikin mawuyacin hali anci zarafinta a dalilin wanna mutumin da mahaifinsa (ta nuna kaka). Hakan ya mana ciwo matuka, ga uwa nakan gangarar mutuwa, a take muka tattara duka karfinmu wajen cetonta, dan duk karfin dake tare da ita na tsafinmu na gado da ma wanda ta samarwa kanta wannan mutumin ya lalatashi. An bada umarnin wasunmu su sake dawowa cikin masarautar nan, duk da zuwane na kasada ni a kasance a daya da ga cikinsu. Kuma nice nan a kashe Shahan-shan Abdull-Majeed a cikin suffar maciji, dan inada maita mai karfin gaske fiye data kowa a cikin zuri’armu. Bayan mutuwarsa na cigaba da bibiyar rayuwar war masu gida, sai dai na kasa kaita kasa saboda abubuwan kanta, nadai samu nasarar nakasar mata kafafu ta hanyar ciyar da ita abubuwa a cikin abincinta. Amma tun randa na had da Zawjata-almilk abubuwa da yawa suka lalace min, dan tanada iskoki masu karfin gaske, itace ta dakusheni akan abubuwa masu yawa. Ta kuma min daurin da bazan iya barin wannan gidan ba duk da naso yin hakan tun a ranar farko dana hadu da itan. Uwa tayi iya kokarinta itama na son ganin ta fiddani amma ta gagara”.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button