Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 48-49

Sponsored links

Amarya Gaji ba a dade ba aka kwashe duk Wanda suka kawo Amarya aka tafi dasu gida,ya rage daga Uwargida da yaranta biyu sai Gaji a gidan,Ango bai shigo da wuri ba har aka maida Yan kawo Amarya gida suka yiwa Amarya waya sunje lafiya godiya ta musu,tana zaune babu ma ko mayafin a jikinta Zayya ta fado dakin ta Fara durawa Gaji ashar tace masu tare miki sun tafi dagani sai ke yau idan kin Isa kice Tak,Gaji mikewa tayi tsaye tace ba Tak ba nace Taka Takai, ta ci kwalar Gaji tana cewa dan uwarki sai kin bar min gida, Gaji tace Ubanki Sa’idu Dan Sa’ido,dama Gaji a munafuncin mutane sunji Sunan Baban Zayya Sa’idu Dan Sa’ido.. Ango ne ya shigo dauke da ledoji biyu,yace mene haka au har yanzu baki hakura ba Zayya duk irin tozartani da Kika yi bai isheki ba dalla sakar min Amarya, Zayyanatu sakin Gaji tayi tare da fashewa da kuka tace Danbinni Kaine ka fada musu sunan ubana har na banza Allah ya Isa

Danbinni bai ce komai ba ya mika mata ledar Naman Daya,ta fisge tana hararasa tace muga Dayar ko da banbanci nasan halin maza da munafunci ta bubbude ledar,Danbinni ransa ya baci yace Wai ke Zayya mene ne haka wacce irin rayuwa ce wannan kishi hauka ne Tsaki ya ja tare da fisge ledarsa yace bar dakin nan kafin Raina ya baci ai naji duk abinda Kika Yi ke da kawayenki da danginki daga kawo amarya ai kya bari ko me zakiyi tukun a kwana biyu ,zata fita yace tsaya zai Fara Nasiha akan su zauna lafiya kowa ta girmama kowa ai Zayya tsaki ta ja tace bazan ji ba karka ka bata bakinka wallahi Danbinni babu zaman lafiya ni da ita,Gaji tana Zaune gefen bed bata ce komai ba da katon tabo a goshi yayi wani dau har Zayya ta gama haukarta ta fice abinta,Gaji ta kalli Ango tace Alhaji Kabiru….shi kanshi wata muguwar kunya ce ta Kama shi yayi nadamar karyar da yayi musu yaji kunya matuka musamman da yaga Gaji ta Zauna a haka basu juya da abar su ba,duk munin halin mutum dole Yana da na kirki,nadama ta rufe shi,Gaji murmushin takaicin tayi hawaye ya zubo Mata tace suturar aro,motar aro,gidan da ka taba kaini dan ka lalatani shima na aro,gidan da ka nuna Mana a waya kace shine nawa shima na aro ,kudin da ka dinga kashe mana dan abinda ka tara ne ko shima na aro ne?

Dan Allah Danbinni baka ji kunya ba,menene na karyar idan Allah yayi Zan aureka dole sai na aureka a duk yanda kake,Gaji ita bata San Danbinni auren sha’awa yayi da ita in ya gama biyan bukata ya saketa,yace nasan idan nazo Miki da gaskiya yanda kuke da son kudi to fa baza ki aure ni ba,ku mutanene kwadayayyu maganin irinku mu,amma ba laifi Ina dan samu a shagon wani da ya saka ni Dan abinda za a ci bazai gagara ba Inshaallah,shi Abu gaji ko mulki ne ana samunsa ko ta hanyar halak ko ta hanyar banza Matukar Allah ya rubuta zaka samu,shi yasa na sameki ta hanyar banza wato karya

Gaji hawaye sharba sharba a saman kumatunta tace ka cuceni Danbinni ga matarka Yar bala’i Kai kanka tafi karfinka,da shegen katon cikinka sai kace mace me ciki wacce ake cewa Allah sauke mu lafiya, ciki Kamar irin tumbin kudi ne ashe ba komai sai Kashi a ciki, Danbinni yace to ya za ayi dani yarinya kinzo hannu kwadayi ya kawoki kin hadu da Zayya kawai idan ta Miki ki rama kiyi hakuri Amarya ki yafe min sonki ne yasa nayi Miki karya,Ina kaunarki ki yafe min Danbinni ya sake narke mata,wallahi duk komai na Ogana ne nake ara dake yaro ne matashi sai ya dinga goya min baya yace ai zaizo har gida ya ga Amarya,baki Gaji ta tabe tana hawaye tace uwar da ta haifi ogan naka Allah ya tsine Mata da Ogan naka harda kai da entire generation naku, sabo da Dabinni ya Gama sire mata,badan yunwa ba da Naman kajin da ya kawo baza ta ci ba amma haka Danbinni ya bude yace ci Mana kazar ya yago ya bata a baki Gaji tana shesheka tace Allah ya Isa ta lamushe kaza,ya sake yagowa Yana danne dariyarsa tana hawayen dai tace Zayya ma Sai na karya ta kuma wlh ka dameni sai na sace maka cikinka ta sake Mika baki ya saka Mata kazar ta hada da yatsunsa ta Masa cizo ba na Wasa ba sai da ya kurma ihu

Amma ya daure ya dinga bata a baki ya lallaba ta gashi Danbinni Kalar matasan masu kudi ce da shi Kuma ba mummuna bane wankan tarwada ne da Yar kibarsa har ya Fara aje katon tunbi sabo da Yana cin Dadi gidansa ba laifi,sannan Kuma mutum ne me tsananin tsafta da iya shiga duk kayan da yasa kyau yake Masa ainun sabo da yayi Kalar kudi,Gaji tace wanka zanyi inane toilet din? a dakinta ya nuna Mata wata kofa dake rufe wacce ita Gaji ma bata kula da ita ba sabo da dakin katone sannan bakin ciki yana cinta yace ai toilet dinki a cikin dakinki yake yar gatana ya bude Mata ta ga karamar me dauke da siririyar kofa wacce baho bazai shiga ba sai dai a kaikaice toilet ta Sha tiles har jikin bango,sai ta danji Dadi,Danbinni harda cewa ai shi yasa Zayya tafi Jin takaicinki kiyi hakuri kinji Amaryata ki min Addua Allah ya hore min Zaki ji dadi Watarana sai na gina Miki naki ke daya ko ya Kika ce? Gaji tace kaji da shi ta Shige bayi tana murda pampo ruwa ya kawo har da shower ta sama,Gaji tace to ta nan dai na dan ci gaba tayi wanka da brush ta fito,shima ya shiga wanka tare da sake brush ya dauro Alwala ya fito ya iske gaji ta shirya cikin rigar wandonta Jean pencil ya kankameta ta saka bra,ta saka vest sannan ta kawo riga me rufewa har wuya irin ta sanyi duk uban zafin da akeyi ta saka T-shirt a sama ta zauna tana furta zaka ga tsiya.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button