Hausa Novels and Stories

Mijin Malama Page 5

Sponsored links

Ta ko’ina suke jifa mata duwatsun jikin ƙaramin lokacin suka farfasa mata jiki. Wani saurayi wanda kana ganinsa kasan criminal ne yana da dakakkiyar zuciya ya ɗauki wani dutse tare da faɗin. “Fasiƙa, mazinaciyya, duk yadda akai kema ba ƴar halak ba ce, shi yasa tsayin shekaru talatin da biyar ki ka sa yin aure kina bin mazan aure da samari” yana faɗin haka ya sakar mata dutse a goshinta nan take ya fashe jini ya wanke mata fuska,ta fara gani dishi. Sunayen Allah take kira da neman ɗaukinsa, tsoro ya kamata jin babyn nata ya daina motsi da kukan da yake fatan ɗaya Allah ya sanya jifan bai same shi ba, balle ya yi sanadin mutuwarsa.

“To, wai me muke jira ne? daga ita jar jaririn mu sanya musu fetur a ƙona mazinaciyya mai ci da musulunci, a kuma ƙone mugun iri!”

Wani wanda yake da ɗan hankali ya ce “Amma kana ganin ba muyi kuskure ba? Ai ba jifeta ya dace ayi ba, tunda ba matar aure ba ce, budurwa ce bulala ne ya dace da ita” cewarsa.

Saurayin ya ce “A to mene martabarta da matar aure? Ai auren ne ba tayi niyya ba shi ya sa take ta gantali ta shiga rigar addinin musulunci ta ci zarafin Musulunci da musulmai, ita fa yankata ya dace ayi”

Kafin kowa ya sake magana hasken wata dalleliyyar mota ya haske wajan duk da irin fitilar da suke kan hanya.

Gabaɗaya suka kalla motar mai ƙirar Mercedes-AMG G63 Ash colour, slowly yake driving har ya ƙara su wajan, ta cikin motar yake ƙare mata kallo ganinta durƙoshe har yanzu ko motsi ba tayi, ya ja idanunsa ya lumshe wani abu ya daki zuciyarsa zafi da raɗaɗi yake ji sosai abinda yake ji tsayin shekaru ya ƙara yawa a ƙirjinsa. Ya fesar da numfashi tare da sanya hannu ya ɗan danne gefen zuciyarsa, gently ya gyara Bluetooth na kunnenshi speaking calmly ya ce.

“Meet me at my house right now” Yana faɗa ya ɗauki face mars ya sanya tare da ɗaukan Glasses ya saka a idanunsa, cikin tarin nutsuwarsa da kamewarshi wacce ta riga ta zauna a jikinsa musamman yanzu da izzar mulki ke ɗawainiyya da sh.

Ya fito daga motar fuskarsa haɗe duk da babu wanda ya san waye, bai kula kowa ba ya nufeta tare da sanya hannu zai kama nata a firgice ta ɗago idanunta tare da girgiza kai cikin wata murya mai rauni da tausayi ta ce

“Kuyi mini komai, ban taɓa jikina” “ji banza shashasha, uwar mene ya yi saura a jikin banda najasa…,”

Marin da aka sauke masa ne ya sanya ya yi shiru da bakinsa domin har tsakiyar kansa ya ji marin shatin yatsun His Excellency ya fito raɗau a fuskar.

Ya ƙara kai hannu zai riƙe nata hannun domin taimaka mata tayi saurin ɗauke hannu kamar bai son magana murya can ƙasa ya ce “Please Hawwa’u, akwai jama’a”

Ta girgiza kai numfashinta na fita da ƙyar ya ƙara rusunawa shi kansa kamar wanda ya yi jinya ya ce “Haba Jiddo” ganin da gaske take ya sanya ya tattara ƙarfinsa waje guda tare da sunkutar ta gabaɗaya har jaririn sai cikin mota, ya kwantar da ita a baya ya sanya hannu ya zare jaririn tare da ɗaukarsa ya nufi ɓangaren diver. Yana shiga ya yi wa motar key da hannu ɗaya ya fara driving cikin sauri ɗaya hannun kuma ya rungume jaririn, keɓantaccen gidansa ya nufa da ita direct.

Wani tsohuwo ya ce

“To ba ga irinta ba, ɗaya daga cikin kwarton abokin alfashar nata ya zo ya ɗauketa, ai ni duk wani ɗan shege na daina tausyainsa tunda ana sane ake haifarsa”

Haka suka dinga surutu, suna faɗin duk wata mace mai irin shekarun Majeederh wacce ba tayi aure ba to kawai iskanci take tana aikata zina.

Lokacin da His Excellency Abu-turab ya isa gidansa P.a ɗinsa na tsaye yana jiran zuwansa, Hammad ya nufi Abu-turab wanda yake ɗauke da jaririn yana zuwa ya miƙawa Hammad jaririn shi kuma ya koma wajan motar, lokacin Majeederh ta gama sumewa jikinta ya ɗauki zafi sosai a ransa yake istigifari kafin ya tattara ya ɗauketa cak, sanin halin Abu-turab yasa tuni Hammad ya shige ciki da jaririn wani ɓangare ya nufa da ita ya kwantar kan bed, bai tsaya jan aji ba ya samu ruwan zafi da showel ya danna duk inda aka fasa mata tare da yi mata allurar kashe zafi data barci,

After ya gama ya duba babyn. A hankali ya fito yana dafe kansa sbd ciwon da yake masa yana zuwa ya faɗa saman kujera idanunsa rufe. “Amma yana da kyau ka huta Your Excellency” ya ware Idanu tare da tsiyaya black tea a cup sai da ya shanye ya ce

“P.a, kana tsaya iya aikin ka” “Am sorry sir, bayan p.a you’re my best friend hakƙina ne na faɗa gaskiya kuma na kula da kai, idan kana son hakƙin Majeederh tana bawan Allan nan kada ya kama mu yana da kyau a bata wasiƙar ta karanta” ɓacin rai wanda Hammad bai taɓa gani ba ya bayyana kan fuskar Abu-turab, idanunsa da suke a ri ne ya ware akan P.a cikin kakkausar murya ya ce

“Kasan me hakan ke nufi?” Ya shiga kaɗa ƙafa a duk sanda ransa ya ɓaci kafin can ya ce

“She never choice me, ba zata taɓa zaɓata a matsayin miji ba, she most go back to him ba zata gane shekarun da nayu ina jiranta ba” ya miƙe yana kai kawo

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button