Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 43-44

Sponsored links

Sai da Muka gama komai sannan Suka ce lokacin fita aiki yayi suna da fadin aiki yau nasan aikin gefen kwalta za a tsaya Neman customer nace nayi missing street dama Ina nan yanda ake tallan local government Yana birgeni,dariya muka yi Muka fito tare Zan rakasu suka hau napep nace aci dadi lafiya Allah ya kawo manyan customers,Seraline tace Banda irin naki mu bamu bukatar aure, ni nace muku aure zany?da alama yanda guy nan ya rike miki wuta ai aurenki zaiyi,baki na tabe na furta a baya farko farko na so aure amma yanzu Kam bana bukata bana son aure ni nafi son yanci inyi zaman kaina in dinga siyar da kaina shine dai dai,Seraline tace haka ake so kuji dadinki yarinya kiyi komai ba komai,nace na true talk, me Napep dai ya gaji ya fisge su Suka Yi gaba ni Kuma na koma gida, na iske Baba kulu a zaune nace Babata zo kiyi wanka ki kwanta ki huta,Baba kulu Murmushi tayi tace yar nan ni baku bari ma nayi aikin ba a matsayina na Yar aiki kuka hanani aikin kuka ce ni babarku ce na zauna na huta,ai na gode muku ‘yata,nace Hmm Baba kulu karma ki dauki kanki a Yar Aiki ki dauki kanki a Mamana kawai,Baba kulu tace na gode Yar nan Allah ya Miki albarka,Ameen na furta ta mike ta shiga dakinta sai da ta kalli dakin sosai sannan ta shiga toilet,Nima wanka nayi na kwanta dama bana Sallah yau na Fara period.

Auren Gaji Yana ta matsowa har Saura sati Daya duk wani Abu anyi lefenta akwati hudu su a kauyen gani suke tafi kowa har yanga suke,Kaya masu kyan gaske,Amarya ta Sha gyara Aunty Amarya da Gwaggo kullum hudubarsu suke ma Amarya,yau ma da Yamma suna zaune Gwaggo tace kinji dai Gaji Muna fada Miki kina da ilimin zamani kin waye duk kauyen nan wa yayi makaranta ta gaba da sikandire sai ke da Mairo to kiyi amfani da bokonki ki nunawa kishiyar nan ke ba jahila bace,idan ta Miki karki ragawa shegiya ki taka ta,Kuma bance ki dagawa kowa kafa ba duk Wanda yace zai taka ki a Dangin miji,Aunty Amarya tace miji Kawai shi Zaki rike Kam da kissa da kisisina irin tamu ta Mata sannan ko shi yazo da rainin hankalinsu na maza karki yarda ki dora shi a tsarinki,Gaji tana ji tace ai Inshaallah ma Ina shiga za a saki uwar gidan ko tayi zaman bakin ciki,Gwaggo tace shaallahu Kuwa rubutun nan kinyi amfani da shi yanda aka saki ko? gaji tace da gudu ma ai duk abinda kuka bani ba Wasa,Aunty Amarya ta dakko sabon pillow din Amarya ta farke Kan dinki ta cusa laya a ciki ta mayar ta dinke da zare da allura tace Kinga babu me sanin akwai wani Abu ciki idan aka saka yadin gado ki cire pillow din da ya zuba Miki a gidan ki saka Masa wannan kullum ya dinga kwana akan laya, tace to,Gwaggo ta irga wake guda dari ba daya ta dakko kwai Wanda an gama rubuce jikin kwan da ayoyi ta hada tsubbunta aka dafa aka bawa Gaji ta cinye, Cikin lotion din da gaji take shafawa na gyara fata nan ma wani rubutu aka dan zuba aka cakude a cikin man,tozalin gaje na musamman ne da wani siddabaru a ciki Haka turare duk da sunan gyaran amarya ne, kafin biki sai da aka gama tsuma Gaji,Bangaren uwar gida Kuwa tunda ta tabbatar Alhaji Kabirunta Danbinni aure zai Kara itama iyayenta Suka tashi tsaye dama bata da uwa bata da uba a hannun kakarta ta girma kakarta itace ke karbo Mata magungunan tsubbu wajen Malamai itama tana ta tsuma kanta gashi gida daya zasu zauna da Gaji,tace in Banda Kabiru ma dabba ne ni Zayyanatu ai shike nan ayi mu gani wlh idan tazo ma Sai ta fita ta bar min gidana a shirye nake, Saura kwana uku daurin aure Zayyanatu tun kafin ayi jere ta shiga bangaren Gaji ko wanne kusurwa ta yarfa ruwan rubutu da tsintsinya ta fito ta rufe.

Bangaren su Gaji iyayenta sunyi sunyi suje suga gida tunda yace ya zubawa Gaji furniture ba sai sun siyi ko cokali ba komai akwai amma sai hanya hanya yake musu karshe ma yace shi yafi so idan an Kai Amarya a Yaba Masa da irin bajintar da yayi ya nuna musu hoton katafaren gidan a waya sai Murna suke yi yace sauran idan anje za a gani yasan sai sun gode Masa,daga Jin Haka sai hankalin su Gaji ya kwanta abinsu dama yace shi Dan Izala ne baza ayi Masa party ba albarkar aure yake nema,ranar daurin Aure 11am mutane Suka taru sosai da Dangin ango dana Amarya harda abokai aka sheda auren Fatima Usman da Alhaji Kabiru Danbinni Kan sadaki dubu talatin da biyar ko ganin Amarya baiyi ba Suka koma birni abinsu sai waya ya Mata.

 

 

Amarya kuwa an hade cikin leshi fari da Golden ga jaka da mayafi cikin Yan school kawaye da Suka zo wata tana make up itace ta tsara Mata kwalliya da dauri ba karya Gaji tayi kyau dama kuma ta kara haske sabo da man da take shafawa me kyau,Gaji ango Yana sheda Mata an daura ta tambayi wasu Yara da Suka shigo gidan maza,ko kunya a gaban mutane dangi da kawaye tace Kai Sadakina Nawa? Yara Suka ce dubu talatin da biyar Gaji tace Kai dalla ku rufe mana baki jahilan banza bakwa zuwa makaranta ta ya zaku gane lissafi,wata tsohuwa ce ta shigo tana guda Amarya tayi goshi dubu talatin da biyar Sadaki ayiririir…wasu ma yan matan Suka shigo Sadaki talatin da biyar,kowa yazo sadaki dubu talatin da biyar, ai jikin Gaji yayi sanyi ta tsaya sororo tace naji masifa yanzu Danbinni ko waliyyai na ne Suka yanke Masa haka ai yasan na wuce ajin dubu talatin da biyar sai kace kudin kajin turawa guda biyar ko tinkiya karama ta kiwon, da ilimina da komai ubana ya kashe min kudi naje birni nayi karatu makaranta ta gaba da secondary sabo da Allah,ubana ya sakani a primary na Gama ya biya min secondary na gama bai gajiya ba ya sake Nemo min admission na shiga college na karanta Hausa English na gama aiki Kawai nake jira amma duk a dubu talatin da biyar Zan Kare,eyye Ni ba mummuna ba mashaallah dani, gani da hankali,Ina da burin bawa yarana tarbiyya wani wawan Tsaki taja ta fige daurin dankwalinta da aka mata ta zauna duk kowa sai jinta ake ana kallo,waya ta dakko a jaka ta Kira Danbinni bugu daya ya daga kafin yayi magana ta lullube shi da masifa

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button