Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 86

Sponsored links

_Ana tayi muna tayi manyan mata dai da gaske sun dage sai sun zama kalar gaban mota kalar camera tare da gudummawar Mg’s skin care Hajia ta kina ina ake ta wannan harkar arziƙin mata nata glowing suna faranta zuciyar mazajensu da laushi da santsin fatar su ke kina nan kina fama jiki duk kirci😱😱?

Ah haba madam yunƙuro ayi tafiyar nan dake ki shiga ki wataya acikin shahararrun matan nan da ko’ina ake fatan gani dan an daɗe ana jin su watau *team glow by Mg’s*

Macen da ta isa itace mace karki bari ki zama cikin irin muna matan nan da suka rako mata duniya kuna tafe da mijinki yana kallon wata har miyau na zuba tsabar haɗuwarta da kyan fatarta

Mg’s skin care sune sirrin duk wata macen da ta isa a ɗaga kai a kira da suna mace wacce ba’a jin kunyar shiga taro da ita daga nan har villah kizo/kuzo mu haɗe a wannan ƙasaitacciyar tafiyar ta Mg’s skin care domin sune na gaban gaba sune suka ciri tuta indai a harkar gyaran skin ce hajiata kiyi wani fresh kiyi smooth wow🥰🥰🥰kina tafe kina walwali idan fa kina amfani da *Mg’s skin care* ba kya buƙatar ko wanne irin mai product ɗinmu katt ne duk matsalar fatarki muna da maganinta uhmm inata miki labari nace ba sister shin meye matsalarki ta gaban goshin ƴallaɓai?

Acne?, pimples? spot?, strech marks?, sunburn?.

to hutas bi’izinilLah muna da maganin matsalarki kina ganin mata a tiktok fuska luwai lumus kice dama ni ko? to in dai kina tare da *Mg’s* matsalarki tazo ƙarshe bama cika baki gaskiya itace takenmu haka nan kuma siyen nagari mai da kuɗi gida *MG’s skin care gagarabadau*

Price ɗinmu daidaitacce ne sannan kuma dai dai da aljihunku

……Duk da yanda zukatansu ke suya da tsagwaron salon wulaƙanci da raini da suke jifansa da shi game da wannan halin nasa da babu komai a cikinsa sai tsantsar miskilanci da kasancewar jinin mulki da ke yawo a jikinsa basu bari fuskokinsu sun nuna ba har ya gama shan ƙamahinsa da basarwarsa ya tanka.

“Amfanin kasancewarsu cikinmu yafi rashin amfanin muhimmanci Aam. A lokuta da dama nafi son zama da maƙiyi fiye da masoyi saboda dalilai biyu”.

Wani irin kallo suke masa har fuskokinsu na barazanar bayyana sirrin zukatansu. Miran Arshaan yay saurin katsesa da faɗin, “Abni wace irin magana ce wannan? Kakuwa san illar hakan da kakeyi?”.

Miran Jasim dake masa kallon gefen ido cikin takaici yake masifa a zuciyarsa. (Shifa wannan wawa ne baima iya jin ƙarshen zance sam). A zahiri kam kallonsa ya sauke ga Tajwar Eshaan da yay biris tamkar bashi ya ɗakko zancen ba. “Ihm kaga Abni ƙarasa, zata iya yuwuwa naka hangen gaskiyar cikinsa rinjaye ne ga namu. Domin kowa da irin yanda UBANGIJI ke fahimtar da shi abu”.

Tajwar Eshaan da bai ko motsa ba ga zancen Amin nasa sai da ya shaƙi iska iya buƙatarsa kafin ya ɗan ɗage kafaɗu a yanayin ko’in kula. “Ku manta kawai muje kan magana ta gaba. Wataran zamu ƙarasa wannan ɗin”.

Sosai takaici ya maƙure musu maƙoshi su dukansu. Sai dai Miran Jasim har Miran Arshaan yake jin takaici kasancewar shine sanadin katse zancen. Suma shiru sukai kamar bazasuce komai ba a wannan gaɓar. Kafin Miran Jasim ya nisa. “Abu na gaba shine farin cikin tsallakewar matarka. Alhamdullah addu’oin mu sun karɓu, ALLAH yasa ta kasance uwa ga ƴaƴan da zaka haifa masu albarka”.

A maimakon amsawa da Amin daga garesa ƙasaitaccen murmushinsa mai ƙara bayyana ƙyawun da ALLAH ya azurtashi da shine ya saki kaɗan yana mai kauda kansa gefe babu alamar zaice wani abu. Suma basu nuna alamar sun damu da sai yace ɗin ba Miran Jasim ya cigaba da faɗin, “Ya kamata a zauna da Tajwar na jihar Hubab da shugaban tsaro akan waccan matsalar itama. Kar muyi sakaci dayin biris da wannan maganar dan bamu san minene manufa ko dalilin faruwar komai ba. Abu mafi ruɗanin shine makamancin haka bai taɓa faruwa a ƙasar ruman ba sai dai muji a wasu ƙasashe har ma mu bada shawara da gudun mawar ganin sun samu zaman lafiya. Idan haka kuma ta fara faruwa a garemu lallai maƙiyanmu na barazana akan nasararmu kenan”.

Nan ɗin ma dai kamar bazai tanka ba sai kuma ya dubi Miran Jasim ɗin da alama zancen ya shigesa. “Na baku damar yin duk yanda ya dace Aam”.

A take fuskokinsu suka nuna jin daɗin wannan girma daya basu. Sanin halinsa yasa daga haka sukai masa sallama. Har sun miƙe Miran Arshaan yace “Af niko kaga na shafa’a da wannan batun. Abni baka ganin yayi kusa kuwa ace fitar Zawjata-almilk har cikin books room? Yakamata ace tayi haƙurin cigaba da killace kanta kodan maƙiyan da bamu san ta inda suke shirya sabon shiri ba, dan yayi wuri ace mun shagala da tsallakewar ta ta a nawa ɗan hangen. Ai ƙoƙari a tsawata mata ALLAH ya cigaba da kare mana ku ku duka dai”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button