Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 38-39

Sponsored links

,Suka tafi abinsu Suka sake tashin motocinsu Kamar zasu kashewa mutum dodon kunne,Suna barin kofar gidan ya juyo ya kalleni yasan Yana masifa Zan gudu can bariki yace me yasa bakya ji? Me yasa kike da taurin kai? Lokacin Sabreen ta bude idonta tana kuka wiwi tana kallonmu, nace ya za ayi tasa karti maza su min duka daya ya rikeni ya daureni,Ido ya zaro yace ya rikeki nace ae sai da ya rungumo kirjina sau uku Yana taba min nono Kuma itace tace su taba na banza ne na karasa da kuka na fada jikinsa na rungume shi nace shi yasa nace gwara kai ka dinga tabawa tunda kana biyan kudi,Tsaki yaja ya janye jikinsa da sauri ganin Sabreen tana gani, tana daga kwance tace ta tabbata wallahi Karuwarka ce yau gidan ubana Zan kwana,duk dukan da taci haka ta mike Yana tsaye taje ta hado kayanta ta fito tana tafiya da kyar ta shiga motarta,ihu nayi Ina dariya nace bye bye,Me gadi da ya tashi tuni Yana uzurinsa ya bude Mata gate ta fice a tsiyace, Nawwar ya kalleni yace kinji dadi shike nan? dariya da farin ciki ya kamani nace ae mu indai za a taba mu to fa uwarsa baza tayi bacci ba ko waye in ka gaji ka maida ni bariki na ka huta ni banga abin takura ba a nan duk inda Naga Sabreen sai ta San fada damu ba dadi.

Ido ya lumshe a hankali tare da juyawa ya koma Palo ya fada saman kujera Yana huci zuciyarsa tana Masa zafi ciki na koma nima na zauna Muka Yi shuru ni da shi,ba a fi 15mnt ba sai ga Kiran Baffansa,sai da yayi tunani dama ya daga Yana dagawa yaji ashar sabo da shi babban mutum ne amma Babu Kalar zagin da baya yiwa yaro sai da ya kutuntuma Masa ashar iri iri karshe yace to Dan uwarka Dan ubanka kazo gida Ina nemanka,to kawai yace ya tashi bazai iya driving ba yau driver dinsa na ya tukashi zuwa gida.

Kowa ya zauna yayi Shuru Yana saurare Nawwar yana kusa da Maminsa, Iyamami itace ta Fara magana tace wallahi Nawwar ka bani mamaki ka bani mamaki tirrr da hali irin naka,Mami a ranta tace ba tirr ba ban haifi dan tirr ba wlh Allah yayiwa dana Albarka Inshaallah sai yaga dai dai,Iyamami tace dama wannan lusarar uwar taku ai ita ke zuga ku wato Kai ka girma mace daya ta maka kadan sai ka Kara da karuwa,to bari kaji ko zaka Kara aure sai dai a dangi a samo maka wacce aka sani aka San iyayenta da asalinsu,Muna wannan gari Wanda ya tara baki garin kazo nazo ace ka hadu da wata ka aura bazai yuwu ba ko bana raye Matukar da sauran yarana a duniya baka Isa ba,idan Karin aure kake so ka koma can danginmu Shuwa ka Nemo Yar dangi idan Kuma baza ka iya ba ka bamu zabi,Kuma ba yanzu ba sai Sabreen ta tara iyali,Mamin Nawwar ce tayi magana tace idan Allah ya rubuta ya zakuyi wannan fa hurumin Allah kuke shiga,laaaaaa……Iyamami ta dafe kirji kunji Salamatu abinda take fada min wato ke ba a Isa ayi magana akan yayanki ba sai kin shiga kin tare musu shi yasa Suka taso basu da tarbiyya basa ganin kowa da mutunci

 

Papa ne yace dan Allah ku kalli jikin Sabreen ‘yata Daya tilo tace gaba daya matan tsirara Suka Zo da Yan daudu sunfi su talatin Suka Mata dukan tsiya,Sabreen da bakinta yake a kumbure da idonta daya ya kumbure tace ai iya Yan daudu sunfi sunfi su goma,Nawwar ya kalleta tare da furta kiji tsoron Allah lokacin dai kin ji jiki bakya gani dai dai,Baffa ne yace rufe min baki yanzu kalli Yar uwarka kalleta matarka wata banza ta Mata haka idan baka Yi Wasa ba sai na tsine maka,Mama tana gefe tace ato a dauki mataki wallahi idan wani Abu ya samu yata tilo baza aga dai dai ba duk da nima Yar uwa ce amma ai Da baifi ‘Ya ba,Sultana ce tace wlh Namiji yafi ‘ya ko a gado ba daya bane,Baffa ne ya kifa Mata Mari ta dafe kunci yace uwata tana magana kina magana,Iyamami kuka ta fashe da shi tace dama yaran Salamatu basa ganina da mutunci sun tsaneni ta gama zuga su,Amaryar Baffa Yar gaban goshinsa sai yanzu tayi magana tace ato gwara ku gani da idonku nima da yarana biyu ne rak basa kaunata basa kaunar yarana Kuma jini daya muke dadin abin dai mijin ko kwana baiyi a dakinki sai dai ki dafa Mana a matsayin baiwa kike shi yasa ban damu ba,Iyamami tace ita take jawa kanta da kuturun iyayinta,Baffa ya kalli Nawwar yace ka tabbatar ka gyara kuskurenka idan ba haka ba ga shedu kar ku ce ban fada ba duk abinda na maka kaika ji,Kuma ka tababbatar ko wacece ta bar gidan nan Kuma Kar najita a Daya daga cikin gidajenka Zan dinga bincikawa Kuma Kar a kawota gidana ko bangaren uwarka ta koma barikinta kaji me nace? Nawwar yace naji,Sabreen tace Saura Maganar dazu Baffa,yace Ina sane ai tace dama baka kwana tare da ita Kuma kana da lafiya,idan da kana muamular aure da ita ai da mun ganta da ciki,Nawwar ransa ya Fadi da Sabreen har wannan zancen ta iya fada kwafa yaja a ransa,sai da Suka gama fadansu sannan Suka sallami kowa,Mamice ta Fara mikewa yaranta kaf Suka tashi Iyamami ta furta idan aka zagemu aka ci Naman mu Allah ya Isa munafukai duk kin lalata yara Anya Kuwa wannan jinin mu ce,tafiyarsu Suka Yi Suka barsu suna ta magana akan Mami da yaranta.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button