Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 3-4

Sponsored links

Saukar duka naji a bayana a firgice na juyo Ina Sosa bayana a inda nake bayan na ajiye garin tuwon na zauna a jikin bango na rakube Ina hutawa, tana zazzaro min idanu Kamar zasu ballako su fado kasa tace tashi tsintacciyar mage maza kije ki karasa aikinki kaf bana son ‘ya’ya na sun gama karatu sun dawo a samu matsala kaf garin nan babu kamarsu,ko akwai Wanda yayi makarantar gaba da secondary idan ba yarana ba munafuka kina kallona da idonki a soye Kamar an watsa waken suya, a hankali nayi kasa da kaina ina me runtse idona a cikin raina nace ya Allah yaushe zan fita daga wannan kangin Allah ka nuna min Iyayena ko dangina idan ma bazan gansu ba Allah ka hadani da Wanda zai rikeni a matsayin ‘ya Kamar kowa,wani saukar azazaben rankwashi naji tace wai dan ubanki bada ke Gwaggo take ba,juyowa nayi naga Aunty Amarya ce a kaina yanzu wanda dazu Gwaggo ce take dukana ganin zasu yi min taron dangi na mike nace yanzu da me zan fara? Da kan uwarki zaki fara cewar Gwaggo dake jawo ruwa a rijiya, Dagacin garin nan ya shugo Wanda muke Kira da Baban Mairo,nidai aikin gyara gidan nakeyi Wanda gidane a kauyen na rufin asiri gidane na bulon siminti ko Ina ya sha siminti cikin dakuna Kuma tiles ne da bandaki idan ka shiga gidan baza kace a Kauye kake ba sabo da daidai misali Yana da kyau,Baban Mairo Yana kokari wajen kula da iyalinsa kaf garin yaransa ne suka fi kowa ilimi dana addini dana zamani banda ni tunda Ni tsintata akayi iyakata primary na iya karatun hausa da rubutawa matansa

Aunty Amarya da Gwaggo Suka zugashi ya cireni sai Islamiyya Kawai nake zuwa da Yamma gashi har na Kai 21yrs a zaune ni banyi aure ba ni banje school ba sai aikin gida sabo da a garin ma duk kyan da Allah yayi min ba wanda ya taba zuwa wajena kowa cewa yake yi bazai auri marar asali ba babu Wanda ya sani ko yar shege ce ni sabo da mafi yawa Indai yaran halak ne ba a jefar dasu

Dagaci dan Asalin garin Argungun ne Wanda tuntuni iyayensa Dake Fulanin tashi ne Suka dawo Kano Ungoggo me yana da kanne biyu Mata Talatu da Hafsa duk a garin suke aure da yaransu maza da Mata,Dagaci Raliya Gwaggo itace ta fari ya Aurota daga garinsu Argugun Haihuwar Farko ta haifo Maryam ana ce Mata Mairo,ta sake haifo Bilkisu ana ce Mata Gaji,sai Namiji Imrana sai Abdullahi ana ce Masa Audu sai lawan da Autansu Sagiru,duk yaran Gwoggo ne.

 

Duk suna kanana Dagaci ya Karo Auren Kubra ana ce Mata Aunty Amarya a bazawara ya aureta bata haihuwa shi yasa sun dade bata taba haihuwa ba sai dai yaran Gwaggo Kawai ganin Gwaggo yaranta ne Kawai shi yasa basa zaman kishi da Aunty Amarya sun hade kansu duk abinda daya tayi to dai dai ne,basu da Imani Basu da tausayi ko kadan,Dagaci ma haka daga shi sai Yaransa Indai ba yaransa ba to baya son wani da ci gaba ko a kauyen baya son kowa da samu sai iyalinsa.

Gwaggo ce ta bani labarin Lokacin da ta haifi Bilkisu Gaji kenan da watanni bakwai lokacin Kuma aka tsince ni jaririya a nannade cikin sabon zani cikin jini Wanda ko cibi ba’a gama yanke Mini ba a jikin wani masallaci yarinya ce Fara kyakyawar gaske, ana ta cecekucen waye zai dauka a kauyen kowa yaki karba,kowa yace bazai dauka ba Shima Dagaci yaki karba aka rasa me dauka Jamian tsaro Yan Sanda suna ta roko ko za a samu me dauka Kar a bari a kaini gidan raino amma kowa yaki,Gwaggo tana Jin labari tace yo tunda kowa baya so ni a bani idan na raineta ta girma na samu Yar aiki komai na gidan sai ta dinga yi min na huta idan Allah yayi me kashin arziki ce ta zama kadara na dinga Neman kudi da ita,Gwaggo da sauri ta falfalo tace a bata tana so,Hukuma ta bawa Gwaggo Amana akayi rubuce rubuce aka damka Mata jaririya bada son ran Dagaci ba haka na taso cikin tsangwama da bala’i a gidan tun Ina karama Gwaggo kullum ita da yaranta sai hantarata da zagina haka Dagaci da aka auro Aunty Amarya ma haka Suka dora da ganamin azaba iri iri kaf kauyen da yan uwan Dagaci sun tsaneni basa kaunar ganina haka Dangin Gwaggo dana Amarya bani da inda zanje naji sanyi wahala idan da sabo na saba har Muka girma tare da yaransu suma basa so na har dama dama Mairo ma gashi Allah ya bani kyau da cikar zati,kaf garin bani da masoyi Namiji cewar ni Yar shege ce bani da iyaye ba Wanda yake zuwa wajena zance har gashi Ina 21yrs a kauyen Gaji tana 21yrs Mairo tana 23yrs,

Mairo da Gaji suna gama Secondary ya samo musu admission a poly Kaduna sukayi HND yanzu sun gama zasu dawo gida daga Hostel shine ake ta shirye shiryen tarbarsu Kamar zasu dawo daga kasar waje.

Washe gari da safe Dagaci ne ya kwala min Kira bayan na gama aikina da sauri na saka slifas dina dan Madina naje nace baban Mairo gani na durkusa har kasa kudi ya miko min yace maza jeki cikin garin kano ki siyo min Lemon kwali da ruwan roba ki hau machine saura ki zauna baki dawo da wuri ba ki tsaya karuwancin naki karba nayi bance komai ba na shiga daki na dakko Hijab dina blue na dora a saman doguwar rigata ta kodaddiyar Atamfa ta maroon,Gwaggo na samu tana juya Miya nace Gwaggo na tafi cikin gari,Tsaki taja tace to ko ki dawo lafiya ko Kar ki dawo lafiya Rabi Ina ruwana Rabi kike ko Rabi Kudirar Allah ko? Aunty Amarya dake linke Kaya tace Wai Rabi Miracle haka ake ce Mata a makaranta bakar kinibabba munafuka Yar shege anyi cikin Shege an jefar a bola,inda sabo na saba haka na fice Babu me Napep ko Daya a kauyen dole machine na hau na Shiga cikin garin kano bakin wani katon shago nace ya tsaya a nan,Me machine din ya sanni na sanshi garinmu daya nace dan jirani Musa naje na dawo,yace to ni Kuma na shiga ciki na Fadi abinda nake so aka ebo min na siyo

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button