Hausa Novels Complete Documents

Yar Aikin Karuwai 18-19

Sponsored links

Sabreen da kuka ta shiga gida Mama ta tare ta tana tambayar lafiya? tace wannan Dan burar…Dan kutmar….tsinanne azzalumi mugu shine ya dakeni akan kudin nan, Mama tace Yar tamu guda lallai Nawwar baida mutunci bari Papanki ya dawo a sanarwa kakarku Iyamami ita zata dauki mataki tunda ita ta haifi ubansa,suna zaune Papa ya shugo da murna ya samu wata kwangila zai samu kudade ya iske Sabreen ya tambaya lafiya? Mama ce ta fada Masa komai harda cewa bazan yarda ba a kashe min yarinya ta tilo,Papa yace akan wasu Yan milliyan biyu zai kashe min ya lallai yaron nan Wasa yake dani wlh Naga dama sai na hanashi sakewa a rayuwa,bari naje ai Iyamami ce maganinsa Kuma duk abinda nace ta zauna daram.

Bai ko zauna ba ya nufi part din Iyamami inda Yar aiki ke Mata gyare gyare tana ganin Dan nata tasan ba lafiya, tace lafiya Yusufa? Ya kwashe zance ya fada Mata harda cewa yanzu Sabreen ba Yar uwarsa bace ai shi me bata kudi ne bare gata matarsa,Iyamami tace itama bata kyauta ba da ta satar masa shi Kuma Dan ubansa sai ya dake ta,dama na fahimci yaron nan yanda yake jiji da Kai magana ma aikine a wajensa ni gaskiya ki yiwa ubansa da uwarsa magana,Iyamami wayarta ta jawo tace kamo min number dinsa,Lokacin Nawwar suna ta labarin kwallon kafa da abokansa yaga Kiran Iyamami,Tsaki ya dan ja yasan zancen Khaleel Yana kallonsa ya daga Iyamami ko jira batayi yayi magana ba tace Dan ubanka kazo Ina neman ka,to yace Kawai ya kashe wayarsa,Khaleel ya kalle shi yace lafiya dai? yace hmm Kai dai bari wannan Yarinyar Sabreen Mana tunda na aureta wlh Banga amfaninta ba a wajena daga bacci sai sata,sata kuma? Ae sata fa dama Ina ganin ana sace min kananun kudi to yanzu har million biyu ta kwashe ban sani ba,gata bata da kunya bata da respect zata iya cin mutuncin kowa Dan iskan baccin nan nata na rasa na mene mace ta kwana ta yini tana uban bacci,kasan Ina ta Shirin ci gaba da magani akan rashin feeling dina sabo da na dinga bata hakkinta amma Yarinyar nan harda zagi,Khaleel yana tausayin abokinsa yace eyya sorry kaji sai hakuri kaci gaba da hakuri, Yana zuwa Iyamami ta hau bala’i harda kuka tana cewa inama ubanka zai dawo yau ko gobe daga kasar waje ya gani yanda kake wulakanta jininsa wallahi kabi duniya a sannu Yarinyar tace baka kwana da ita,Nawwar idan baka da lafiya ka fada na tafi Kauye na hado maka magani,Shi dai Yana jinsu har ta gama yace bani da lafiya Iyamami abar bata tashi,a gaban kowa ya fada ko kunya,Iyamami tace Sannu Allah sarki za’a Nemo maka magani dan Allah kayi hakuri ku zauna lafiya da Sabreen, Sabreen tana daki aka kirata ta fito idonta duk ya kumbura,Mama tana Fushi tace ke koma ki huta gobe na maidata da kaina ko nace idan ta warke,Iyamami tace to kaji,yace ba damuwa,Iyamami tace gobe Zan tafi Kauye kaji,yace to,Papa yace Dan Allah Nawwar Dana karka sake kaji kaida Yar uwarka itama munyi Mata fada baza ta sake ba,Nawwar dai yace to Suka gama ya wuce gida ,Mama da Papa suka sa Sabreen a daki suna fada Mata lallai Yana warkewa ta saki jiki ta haihu da shi idan ta haihu da shi to sun gama mallakar dukiyarsa da komai sai yanda Suka yi,haka suka zugata sosai ita Kuma Iyamami an tafi Kauye karbo magani,

,kwana daya tsakani sai gata ta dawo da tarin magungunan gargajiyar ciki harda rubutu har gida ta samu Nawwar ta karanta Masa yanda zaiyi amfani da magunguna,wani dan itace ta Mika Masa tace rike idan abar ta harba ko ta mike ka fada min,Nawwar ya karba ya rike Shuru ko motsi tace,yana rikewa ta furta to ya? yace ai ko motsi bata yi ba ko na nuna Miki? Iyamami tace gidanku fitsararre dariya yayi sosai hakoransa kyawawa Suka bayyana,Iyamami tace ji yanda kayi kyau kana Murmushi ashe mijin nawa dai yana dariya,yace idan magani yayi aiki sai a fara ta kanki dukansa tayi ta mike tace marar kunya ba ta tafi abinta,shi dai bai zaci magani zaiyi ba a banza yake kallonsa sabo da yayi masu tsada ma baiyi ba har na asibiti Shuru sai wannan garin ganyen bishiyar haka yana tabe baki yana wani kyankyami a haka ya fara amfani da magunguna.

Miracle…Miracle….Fitowa nayi da gudu naji muryar Yar zabil Ina Fitowa tace wanke wanken fa waye zai miki? nace kiyi hakuri na tafi nayi Mata na gama dakinmu na koma na samu Seraline ta kalleni tace Rabi ki daina zubar da mutuncinki a gidan nan duk layin nan babu me kyawunki Rabi kin tsaya a wanke wanke da shara wasu banzaye suna wahalar dake Wanda da zaki Fara sana’ar nan nasan sai kinfi kowa customers,yanzu kudin da kike samu basu isarki ci da sha da biyan haya bare kiyi saving ki fara gaki yanzu kin waye kin goge kin Zama tsagera wata Maganar da kike fada ko ni Watarana sai na daure zan iya furtawa,nace sana’ar ku bazan iya ba Ina tsoron Allah duk iskancina a baki ne wlh,to naji Kinga yanzu dare ya kusa zamu je aiki ki shirya muje dake kiga yanda ake harkar ki bawa idonki abinci ko banza kyayi kallo Zaki ga yanda ake aikin sai ki dawo gida nace wannan dai zan iya,to ai bani da Kaya masu kyau na fita,Sera cikin kayanta ta zabo min wata gown silver and black me tsadar gaske amma bata fi rabin cinya ba,ta fito min da dankunne da agogo me kyau da takalmi me dan tudu sai hular gashi dogo me tsada tace shirya,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button