Hausa Novels Complete Documents

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 31

Sponsored links

Kamar daga sama yaji alamun ana waya daga chan gefensa,bega fuskar meshi ba kasancewar me wayan ya juya baya,sai ya kasa tantance waye dan da alama meshi ba dan gidan bane,jin sunan Deen da aka kira yasashi bude kunne sosai dayake gurin is so silent shiyasa yake iya jin abinda ake cewa,a hankali yaji an kara cewa….

“Nan da kwana uku nakeso ku kashemin Deen!”…. A gigice sameer ya mike jin wani abu kamar saukar aradu,wai zaa kashe Deen nan da kwana uku? Toh waye wannan dayake farautar rayuwar Deen haka? Kodai shiyasa Deen yace masa haduwarsu hadari ne yanzu? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un dole yayi wani abu…. Mikewa yayi da sauri ya nufi inda meyin wayar yake tsaye,gashi ya kasa gane muryar waye,yasan dai koma waye yanada alaka dasu Deen tinda gashi a gidan…. Da sauri meyin wayar ya bar wajan jin kamar ana nufar inda yake…….

Sai da mama ta tabbatar komai na building din ya cinye sannan ta kira fire extinguishers sukazo suka kashe wutar ganin makota sunfara kawo agaji gudun kar a zargeta,da aka tambaya koda mutum a ciki mama tace babu incase in fatima zainab bata mutu ba ta karasa mutuwa a ciki…….

Sai la’asar ta farka,addu’ar tashi daga bacci tayi sannan ta fada wanka,shiryawa tayi cikin fitted gown kasancewar tana da kaya a part din. Bacci takeji sosai kuma ka’idarta in tanajin bacci batacika magana ba, hakanne yasa ko kallon mama batayi ba data shigo,haka kawai taji bazata iya baccin a part dinta ba,harta kwanta ta mike ta fita lokacin ana sallar azahar… Part din momman su khaleel ta tafi,tashiga bedroom dinta tayi baccin,ita bata masan momma batanan ba tinda taga part din a bude…. Koda ta fito bata tarar da kowa ba dayake lokacin sallah ake so bawanda yaga fitarta daga part dinta…. A cikin bacci taji kamar wayarta na ringing,sharewa tayi sai da taga calls din yayi yawa sannan ta daga,nan abdul yake cemata ta bar part dinta hankalinsa duk a tashe wai konata zaayi,jin abun tayi kamar a film amma fa hakan be hanata cigaba da baccinta ba…

 

Da yake bata sallah,karasa shiryawa tayi sannan ta fita daga dakin ko dankwali bata daura ba,jelar gashinta sai lilo yake a bayanta,ta fita ta nufi part dinta,mamaki ne ya kamata ganin lallai maganar abdul gaskiya ne,yanzu inda tana ciki shikenan saidai ta kone murus haka? Lallai mama bata da hankali,kuma yau saita nuna mata tinda ta kasa konata,toh ita bari ta konata…..

Komawa part din momma tayi tana tinanin shigar jikinta bebi da tsarin abinda zatayi ba,wani crazy three quarter ta dauko ta saka ta dora da wata armless top sannan ta fita ta nufi part din mama…….

Banko kofar tayi ko sallama babu,husna da imaan ne zaune a hadadden parlourn mama suna kallo… Binta sukayi da kallo ganin irin shigar dake jikinta kamar zata club,matar da kullum a hijabi take,mamaki suka dingayi wai dama haka take? Tabdi jan! Lallai anyi halitta anan,sufa sun dauka wani abun take boyewa shiyasa takesa hijab ko yaushe,kullum sai sunyi da ita suna cewa kyawun fuska kawai gareta shiyasa take abunda taga dama… Imaan ce ta kasa shiru dan batasan lokacin da tace

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button