Hausa Novels Complete Documents

Bakon Lamari 14

Sponsored links

Wata ƙara ta saki tana Ihun murna duk azaton ta, ta ɗauka sabida ita zaizo jin ƙarar tai yawa yasa ya datse kiran yana mai kashe wayar Baki ɗaya ya mirgina ba jimawa bacci yay awan gaba dashi.

Bai tashi ba sai magariba yayi sallah ya kuma fita Filin training wanda anan suka ɓata Lokaci har zuwa isha’i sallah kawai yayi ya soma haɗe tarkacen sa yana addu’ar In sha Allah daga wannan tafiyar yabar lagos gaba ɗaya In sha Allah arewa zai koma koda ba Kano state ba.

Ramcy zamu yi faɗa akan Baby wallahi ban haɗa soyayyar Baby data kowa ba rannan da Hajiya tai min baki akan Ahmad sai da nai kwana Uku ban ci abinci ba sabida haka kema zamu ɓata akan shi nina san Baby baze ci Amana taba yadda yake sona har yayi yawa”

Ramcy tabi zee da kallo tana mamakin rawar kanta akan wannan Ahmad mai wa mutane kallon banza.

Dan ita tunda tagan shi sau ɗaya taji baya burgeta sabida kama gidan shi yayta wani haɗe rai yana wani shan ƙamshi kamar wani basarake!

A gurguje Zainab taiwa Rahma Sallama ta wuce Gida ta ɗauki sabon kaya takai Ɗinki tun a ranar ta umarci masu Hidimar Gidansu akan su soma ƙara gyara gidan na musamman don akwai babban baƙon da zai zo.

Ranar haka zainab ta Ishi Hajiya da Dadyn ta da maganar Ahmad wanda suka Biye mata suna taya ta Murnar zuwan Masoyin nata don Dadyn ta har kuɗi ya kuma ƙara mata yace ta gyara Jikinta da kyau.

Washe garin ranar kuwa Zee ta wuce gidan gyaran Jiki wanda aka gyare mata Jikinta daga nan ta wuce wajan Mai make up tai Booking wanda zata je ranar da Ahmad zai sauka in an mata ta wuce airport ta ɗauko shi dan tuni tai masa waya akan cewa ita zata ɗauko shi idan ya sauka daga nan ta wuce dashi Gidan su inya Ci Abinci ya Huta sai ya wuce nasu Gidan ( kuji fa )

Shiko Ahmad koda zee tai masa wannan maganar kawai yaji tane batare daya bata amsa ba don shi tuni Yayi wa Kamal ƙanin shi waya wanda shine zai ɗauko shi don shi baze bi tawagar suba daban zai tawo sa haɗu a filin daga

Burin shi ya ganshi a gaban Maman shi dan yayi masifar Missing ɗinta Ji yake kamar yay tsuntsu ya janyo Jibi ya ganshi a kano.

Itama kuma Maman tun da yay mata waya zaizo take hidimar tarban shi dan takanas zata shiga Kicin ta shirya masa abinci na musamman wanda rabon ta da kicin tun da Ahmad yabar gida don baya cin abincin kowa sai nata wannan yasa tunda yabar kano ƴammatan ta ke mata girki sai yanzu da yace zaizo Jibi take Hidimar haɗa masa abincin da zai ci idan Allah yasa yazo ɗin wanda zatai mai abincinmu na gargajiya don yafi son shi fiye da kowani abinci

Yau tunda Imran yabar Gidan bai dawo ba sai Cikin dare gaba ɗaya ran shi a ɓace yake sabida haka komai ya gani a gidan ball yake dashi sakamakon Maganganun da Uban gidan shi ya gaya masa.

“Ina son ka Imran wannan auren da kayi ma dan babu yadda zanyi ne amman duk ranar dana tabbata ka kusanci matarka daga ranar zaka gane kuranka kasan ba’a yaudarar Tani Ɗan Manu”

Wannan maganar da Tani ɗan manu ya gayawa Imran shine ya sanya Imran bacin rai ba kaɗan ba Tsoro fargaba ɗimuwa shine ya ke ɗawainiya da IMRAN DARE ƊAYA sunan da jama’a ke kiran shi dashi kenan.

Tsoron shi ɗaya shine kada Tani Ɗan Manu ya gano fa ya kusanci matar shi har ta haihu wanda Auren ma sai da Imran yakai ruwa rana sannan tani ya bar shi yayi sabida a tsarin su tani babu auren wani jinsi wannan alƙawari ne sukai da ƙungiyar su koda yabar Imran ma yay auren dan babu yadda zai da son Imran ne wanda shi kuma Imran Mahaifiyar shice ta matsa masa akan sai yayi auren wannan tasa yayi aure akan sharaɗin babu kusantar matar.

Zama yayi akan Kujera yana saƙa wa da kwancewa na matakin daya dace ya ɗauka akan Amatullah da ƴarta ji yake kamar ya kasheta ya Gudu yabar Gidan.

A fusace ya Nufi ɗakin daya kulleta ya sanya Key ya buɗe ya shiga cikin sa…………*Wannan karon ba zan sai da Baƙon lamari complt ga kowa ba domin na riga da na sayar da labarin ga wata kafa jira kawai suke na gama posting na basu kayan su daga na gama shi ya tashi daga mallakina ya koma mallakin su don na sayar musu dashi, dan haka duk mai son karantawa ya saya tun yanzu da nake posting inna gama ya zama complt ba zan sayar da shi ba sannan innai nisa a paid page nan ma bazan amshi kuɗin kowa ba sabida abubuwa suna Mini yawa bazan iya turawa Mutum shafukan dana wuce ba dan haka duk mai buƙatar ayi wannan tafiya dashi sai ya hanzarta Biya kafin na gama free page dan wannan karon babu sanya Dana gama free pages zamu soma posting paid page babu tsayawa har sai mun gama da Izinin Allah*

 

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button