Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 85

Sponsored links

Tinda ta fito daga pharmacy din ya gane itace hakan yasa ya gyara tsayuwarsa tambayoyi fal ransa kan abinda ya fito da ita a darennan…..

Itama tun kafin ta karaso ta hangosa, saida taji gabanta ya fadi batasan dalili ba, kodai ganin ya hadarai ne oho, ta kuma samu kanta da boye abinda ke hannunta a cikin hijabi, itama ta hade rai tana jin dama akwai wata hanyar da zata bi ta gudu…..

“Mallam bani hanya in wuce”…

Ta fada tana sake kaucewa daga inda ya tare mata, shi kuma ya kara tare inda ta koma…..

“Dalla mallam ka bani hanya in wuce, ina ruwanka dani ne?”…….

Be kulata ba saima jewo mata tambaya dayayi;

“Me kika fitoyi a darennan duk securities din dake gidan mami?”…

“It’s none of your business”….

Ta fada tana kara boye abinda yake hannunta….

“Karki sake kimin rashin kunya yarinya, now tell me abinda ya fito dake”…..

“Ka bani hanya in wuce mallam!!!”….

“Anki a baki hanyar, in kinga kin bar gurinnan toh kin fadamin abinda kikazo yi ne”….

Dage kafada tayi tace;

“Toh sai me? Ashe ko zamu kwana anan, dama ba yau na saba kwanan waje ba!”…….

“Ai nasani sarai, shiyasa ko wani hotel sai an ganki”…..

“Good you know!!!”….

“Kehh me kike boyewa ne naga kinata wani kunshe hannu a hijabi, kiyitasa hijabi kamar wata ta Allah”……..

“Kayi kadan in boye maka abinda yake hannuna wallahi, idan ka gani meka isa kayi toh?”…..

“Kodai shaye shaye kike dan daga gani babu abinda bazaki aikata ba!”….

Lumshe idanunta dataji suna mata zafi tayi cikin sanyin muryarta dake kasa bayyana masifarta tace;

“Wallahi kamar ka sani, cocaine ne, ko zaka sha?”..

Zaro ido yayi sosai yace;

“Kikace meh?”….

“You heard me right! Babu kalan kwayar da bana sha”……:

“Dallah rufe mana baki stupid girl kawai! Shiyasa kullum idonki kamar na yan shaye shaye, Ko kunya bakyaji wai babu kwayar da banasha?”…

Girgiza kai Deen yayi ya shiga kakkabe jikinsa data bade da kura yana lissafin yanda zeyi tracking dinta, kamar yasan wani abu ze faru ya dauki tracker a gidansa yasa a motar da wata manufar daban sai gashi abun ze masa aiki a inda baya tinani, kawai yarinya tayi gaba da mota kamar ta ta, ji wani audacity dan Allah?…. Abu daya ne ze hanashi nemo inda take a darennan and that’s because he’s not with his phone dake tracker din is linked to his phone, yanzu dole sai ya koma prison tinda wayar na chan though yana da plan din komawa a yau kafin securities din su farka daga suman da basu san sunyi ba, yanzu kam saidai yasan yanda zeyi ya dauki phone dinsa ya sake gudowa……

Driving take a haukace har securities din unguwar saida sukayi kokarin tareta amma taki tsayawa, ganin kamar zata bi takansu ne yasa suka matsa mata da sauri after jotting down the plate number……

Ta dade tana shawagi akan titi kafin Allah yasa tayi shawarar zuwa school, school din da tafi sati nawa bata jeba, if she’s not mistaken ma kamar exam is starting on Monday gashi ko tests batayi, dage kafada tayi alamun ko oho idanma tayi failing……

Suna zaune suna dan hirarsu yanda suka saba duk dare idan suka dawo daga library kasancewarsu yan till day break duk inda 9 tayi sungama karatunsu sun dawo hostel, basa taba karatun dare…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button