Hausa Novels and Stories

Fulani Page 4 Hausa Novel

Sponsored links

AHMAD ASHIRU UNCE A A matashin sarauyin da bashi da aikin yi ba dan be yi karatu ba, sai dan aikin a Nigeria ya zama sai wane da wane, sai mai hanya da gata sai kuma wanda Allah ya tsago da rabon abincinsa a gabnatin jiha ko ta tarayyah, a gurin yayarsa yake zaune wacce ta tsaya masa bayan raye uwa da uba, ita ta zame masa tamkar uwa duk wani fadi tashi na karatunsa da hudimar rayuwarsa ita ce take masa duk kuwa da kasancewar ita ma din ba wani abun hannu ne da ita ba, sai dai tana sa’ar siyarda kayan masarufi a cikin gidanta sana’ar ta karbeta sosai a ciki take ci ta ke sha har ma tai ma mijinta wata hidimar kasancewarsa karamin lebara ne wata….

Shinkafa da wanke ce da mai da yaji an yanka tumatur a cikin da albasa, sai kuma ganyen salat da aka yanka a sama shi ma kadan. A hankali yake tauna ragowar shinkafar da ke bakinsa, hannunsa rike da waya yana duba duniyar facebook.

“Uncle A A ba zaka ci abincin ba sai ya sha iska? Ba dadi idan ya huce”

Dauke idonsa yai daga kan wayar ya kalli Jamila wacce ke maganar yai dariya.

“Anti abunda ke ban mamaki wai sai ka ji mutum daya ya yi sama da dukiyar talakawa ta miliyoyin nairori, ni har ganin na ke kamar kudin nan karya ne, wai yanzu akwai irin kudin nan muke zaune haka?”

Dariya Anti Rabi tai tana aikin kulla man kulin da take ta ce.

“Gaskiya ne akwai kudin idan kudi, sai dai masu kula da kudin ne macuta kuma mazanbata”

“Hmm Allah dai ya kyauta, mu ko aikin ya gagare mu samu, da ma degree ne wata kila da za ka fi samu amman ba kowa ke ganinta da daraja ba”

“Karka damu Ahmad wani abun a nesa yake, kuma kowa da irin kaddararsa”

©®Hakkin mallaka nawa ne ni kadai, ban yadda a saffaramin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya hanyowa mutum matsala a kiyaye ⚠

 

Ban yarda kowa ya hada document na littafina ba, ni ma na iya idan ina ra’ayi zan iya yi da kaina, ina albishir ga wanda ya hada document din Gobe na da duk wani littafi nawa cewar ban yafe ba ina rokon Allah ya saka min kuma ya mana shari’a da ko waye ne❗️

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button