Hausa Novels and Stories

Idon Naira 20

Sponsored links

Kamar lura da tsaftar babban bangaren mahaifinsa da aka maida sabon guri tareda zuba komai sabo na Jin dadi rayuwa na masu arziki yanzu shine aciki

duk da bayaso Yana Mata fadan yin aikin Amma takasa barwa kowa aikin kulawa da duk abinda ya shafesa sbd tasan rikakken halinsa daya gado gun mahaifiyarsa na kyankyami da rashin son takura Dan kusan yafi mahaifiyar tasa qyanqyami da tsandar abubuwa nesa ba kusa ba.

Hakama tsaftar bangaren Haj maryamah har kullum itace da wannan sbd Haj maryamah din nada tsananin qyanqyami da tsanda,

Abincinsa Dana Haj maryamah shima har Koda yaushe nata kawai suke ci Dan haka dai kusan anyi baayi bane.

Tunda ya kammala secondary School aka fara yimasa shirye shiryen tafiya karatu UK Kuma bai musaba sbd shi Kansa yana buqatar zuwan duk da Maminsa na cikin ransa ta yadda zai tafi yabarta baa qarqashin kulawar kowaba.

Da farko Jin tafiyarsa Zainab tashiga damuwa sosai saidai kuma Tunda karatu ne zaije,

Qaruwarsa ce hakama duk cigabansa tanaso Dan haka sai ta danne damuwarta kawai ta boye a ranta Tunda kafin zuwansa duniya cikin kadaici take rayuwarta batareda kowa Dan haka yanzu dinma zata iya idan Allah ya yarda.

Dayake Yana karantar yanayinta Kai tsaye kwana biyu duk yanda take dannewa ya gane Tana cikin damuwa da kadaicinsa tin yanzu Dan haka sai shima yaji damuwar barin nata ita kadai din.

Kwana biyu yafara tunani da neman yanda zaiyi da lamarin Dan kuwa bazai taba iya tafiya yabar Mamin cikin damuwa da kadaiciba Kuma Hakanan zuciyarsa takasa nutsuwa da barin nata…

Jin yake zai iya hakura da tafiya wata qasar ya zauna yayi karatunsa anan sbd ita

Amma Tunda Haj maryamah tafara fahimtar abinda yake Shirin faruwa na sauyin raayinsa dayake Shirin Yi take Hankalinta ya tashi sosai Kuma ranta yayi mummanan baci Dan kuwa wannan karon batajin zata sassautawa Aqeel din bare Zainab idai akan tafiyarsa ne.

Farko Kai tsaye ta tarasu a babban palonta da Aqeel da Zainab din wadda take zaune a kujera jiki amace

Ita kanta zaman kujerar sbd Aqeel Yana gurin ne take zaune akai Dan tuni yayi Hani da Zamanta a qasa Dan bazai iya yarda Yana ganinta zaune a qasa ba shi Yana kan kujera

Haka Haj maryamah tanaji Tana gani ta dauki wannan dokar tasa ta barin zaman Zainab din a kujera a palonta idan suna tare sbd kaucewa bacin ransa.

A yau din ranta bace yake sosai Wanda kusan su dukansu sun shaida Hakan

Dan haka palon yayi tsit suna jiran abinda zata fada musamman Zainab data Gama sanyi akan ko wane irin laifine tariga tasan itace zaace ta aikata Tunda akai kiranta.

Take jikinta ya sake mutuwa Dama kwanakin sai ahankali Tunda maganar tafiyar ‘dan nata ta tabbata takasa gane kanta Dan Jin takeyi idan ya tafi kamar sun rabu kenan…

Kai tsaye Zainab Haj maryamah ta kalla kafin ta maida kallonta akan Aqeel Wanda ya kalla Maminsa yaga yanda duk tayi sanyi take zuciyarsa tayi Dan nauyi Dan haka ya dauke kallonsa daga gefenta ya gyara zamansa tareda hade dogayen fararen yatsun hannuwansa guri daya Yana Dan lumshe fararen idanuwansa cikin Yar damuwa da rashin Jin dadi.

Aqeel maganar tafiyarka UK nakeson nasake Jin raayinka Dan kasan yanzu Kai ba yaro bane da zan zauna muna Abu daya koyaushe akan tafiyarka karatu,

As you can see manyanci yariga yaxomin Dan haka Dole zaka maida hankali kan karatu Dan is dakemun wannan nauyin na Aiki da kula da komai Nima nasamu na huta na fuskanci gyaran gobe na.. so me kace gameda tafiyar???

Ahankali ya sauke idanuwansa akanta tareda Dan sauke idanuwansa qasa Dan girmamawarsa ga manyansa itace Sam baya iya kallon idanuwansu ko tsaida kallonsa akan fuskarsu Dan haka Bayan ya kalleta kadan saiya sauke idanuwansa..

Muryarsa data fara zama budaddiya irin na mazan dasuka amsa sunansu maza yace”

Baya qarya kwata kwata sbd ilimin addinin daya ratsasa yasan illarta barema ba halayyarsa bace Dan tarbiyar da Zainab tayi Masa Sam Babu gurbatacciya a cikinta Dan haka ka tsaye yace”

Kasa magana Haj maryamah tayi sai data dafa goshinta dake sarawa Yana saka kanta wani matsanin ciwo Dama gashi rayuwarta gabaki daya tagama juyawa Tunda tazama itace komai hatta hawan jini na wahalar Aiki da tunanin duniya duk ya kamata gashi acikin gidanma Aqeel da Zainab na neman sake Dora mata wani hawan jinin akan Wanda take fama dashi.

Cikin sanyi tafara fada ranta amatuqar bace Dan ko energy din fadan sosai batada Amma ranta yayi bacin da Zainab din tajima Bata ganiba Dan haka takasa cewa komai sai hawaye datakeyi masu zafi da ciwo Dan kuwa maganganu ne masu ‘daci da zafi take fada Mata akan ba itace ta haifi Aqeel dinba shiyasa zata lalata Masa rayuwa..

Tun Tana hawaye karshe wata irin sheshekar kuka takeyi Wanda yake bayyanarda tsananin zafi da ciwon harma da ‘dacin da maganganun suke Mata a zuciya.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button