Hausa Novels and Stories

Sanadin Zane 7-8

Sponsored links

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

 

 

Cikin kankanin lokaci ta cinye ta saki wani katuwar gyatsa

 

 

 

Kawu ya yatmusa fuska yace”shegiya kurma ba abinda aka sani sai abincin

 

 

 

Kallonshi tayi tana harararsa Kamar taji maganarsa yace”da yike ta rainani Ni in nayi magana tana ji,na rasa wanan matsifa ta wanan yariyar shi shaida ne kwata-kwata Bata ji amma wani lokaci Yana da kokonto a lamarinta Dan shegen matsifar son zuwa gun DJ ne da ita in ta gan ana rawa zata Fara takawa

 

 

 

Tafi da yaji tanayi yasa ya kalleta sai ya gan alama takewa hafsat da Kar ta bashi indomie

 

 

 

Yace”yariya kinyi karya me Shiga tsakanin Mata da miji ai sai Allah bare ke kurmar banza ”

 

Hafsat tace”Kai dai ka bar magana kasan tana iya karanta laben mutum in akayi sa’a ta gano me kace sai kuyi tashin hankali tunda ka girma ne baka San ka girma kayi ta biye Mata Kuna tashin hankali yariya na rainaka toh ka sani duk Randa data kashe ka ba lallai in maka takaba tunda har ta Kai ga tana d’aukar ice wata Rana tayi sanadinka saidai inyi matsa mudu biyar a bika da sadaka Dan Kai ka jawowa kanka Amma aure zanyi”

 

 

 

Tashiwa zaune yayi yace”da kuwa kin kafurta hafsat ke kin Isa aiko sakin ki nayi ba ma mutuwa Baki Isa kiyi sure ba sai kin min idda saidai in Zaki ja da fadar Allah”

 

 

 

Hafsat ta shiga ciki ta watsa ruwa ta fito da taburma ta zauna tana kallon kawu daya kurawa kurma Ido

Tace”Wai lafiya kake Mata wanan kallon ”

Yace”hafsat watoh kullum in na kalli kurma sai nayiwa Allah tasbihi da Kuma mamakin kasancewarta a ahalin nan kin dai San Yar kanwata ce Amma wallahi wani lokaci sai inyi ta Jin kamar da wata a kasa Dan yariya gata dai kamar balarabiya ni kyaunta ma firgitani uake shiyasa Kika gan na dage Ina ta zuba hanun jari a kanta,kudina kanta yake karewa dan wallahi bazan bawa talaka ita ba kinji rantsuwar musulmi,duk inda akayi ranan da aka halliceta ranan sa’a ne ki dubeta fah watoh shi Allah ba ruwansa da ya Mata kyau yayi Mata diri ya Mata tsayi sai kawai yayi ta kurma,Allahu Akbar Allah buhayi gagara misali Kuma uwarta a balaguro ta sameta can uwa duniya Cameroon

Hafsat tace”Ni kaina Ina tausayin wanan baiwar tasa”

 

Kawu yace”Kuma ita Bata tausayin kanta ba ‘

Jibrin ne ya shigo da sallama da niyyar ya ci abinci sai ya gan murhu a jike kwalawa ummi Kira yayi ta fito ta zauna kofar d’akinta yace”ummi Ina abinci na”

 

 

 

Ummi tace”banyi ba sai Kuma gobe so Nike kowa ya kwana da yunwa duk uban wahalal da naci wajen had’a wutar fannah ta kashesa sanadin kabiru baxan kashe kaina ba

 

 

 

Ai jibrin Fara buga kafa yayi Yana yi Kamar zaiyi kuka Yana cewa”kawu ka gan abinda ka jawo yanzu me kake so inci

 

 

 

Kawu yace”gani har sai ka nimi abinci kawai dai in kwanta kayi ta datseni kana ci in Banda iskanci godai godai da Kai kana kukan yunwa ko da yike ban gan laifinka ba laifin uwarka ce da ta muku wanan b’arnan,shekaru baya ba abinda ba a Gaya Mata ba karta auri mahaifinki tace tsam soyayya ya rufe Mata Ido ai tare zasuyi arziki,lokacin wani alhaji Allah ya jikan musulmi alhaji mato ya sota taki tace

sai mahaifinki gashi dai har ya mutu beyi arzikin ba an haifeshi Yana fama ya mutu Yana fama yanzu da a ce alhaji mato ta aura ai da Kuna da gado Amma taki mahaifinku ko tabarma ya bar muku

 

 

 

Jibrin ya samu wuri ya zauna yayi tagumi ji yake kamar ya rufe kurma da ko a jikinta zanenta na jaraba take hankali kwance kawai Dan kawu ya cinye Mata abinci sai ta kashe wuta a zuciye ya mike zai Kai Mata duka saidai kafin ma ya Kai kawu yace”karka kuskura dan da ka tab’a min ita gara ka lakada min duka wallahi insurance kake gani zaune itace co’operative Dina duk wata kudina kanta yake karewa ka sani. so kake ka daketa in Shiga uku wani Abu na samunta wallahi haukacewa zanyi

 

 

 

Komawa yayi ya zauna ita Bata ma San sunai ba Dan Bata ji me ake ba

 

Kawu yace”in Banda duniya ta lalace Kai baka Isa ciyar da kanka ba ka wani Zo

Shigewar Fahad ba jimawa sai ga sa’adatu ta shigo da kuka

 

 

 

Kawu ya zabura Yana cewa Yaya Yaya da wanan Daren badai yaji kikayi ba

 

 

 

Sa’a na kuka tace”ummi wallahi na gaji da auren alhaji Ashe dama ba shi da lafiya ya aureni ku duba fa watan goma da aure Amma a ce dudu befi so biyar mukayi ba ”

 

 

 

Ummi data rikece tace sako ki yayi ne?”

 

 

 

Kawu yace”ban Gane ba kukayi me so biyar ”

 

 

 

Kuka ta fashe dashi Fahad dake jinsu ya fito ya dakawa sa’a tsawa yace”miye haka miyasa Baki da kunya ne wace irin magana ne wanan kikeyi

 

 

 

Kawu ya d’aga me hanun yace”Bari tayi magana”ya maida kallonsa ga sa’a itama

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button