Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 81

Sponsored links

Isowar labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya matuƙar tada hankalin duk wani mai faɗa a ji a daular ruman. Dan abune da bai taɓa faruwa ba a kasar ta ruman. Amma abin mamaki ga Tajwar Eshaan ba hakan bane, dan babu wani alamar damuwa ko

nuna kaɗuwa da lamarin. Kallo ɗaya yayma akwatin talabijin ma ya ɗauke kai kamar ba’a ƙasar da yake mulka matsayin shugan kowa da kowa al’amarin ya faru ba. A karan farko wani abu da tun shigowar Iffah masarauta bataji akansa ba ya tsikari zuciyarta sakamakon ganin halin da ya nuna akan wannan al’amari da duk wanda ya kwana ya tashi a ƙasar ta ruman bazai ce bai shiga ruɗani ba. Duk da ance ba’ai asarar rai ko ɗaya ba taji kamar ta tashi ta shaƙure wuyan Shahan-shan ɗin ta huta da ganin wannan azzalumin shugaba da kansa kawai ya sani sai ahalinsa.

“Mi hakan ke nufi?”.

Ta faɗa tana faman kai kawo a ruɗe itama duk da a labarin an sanar da ba’a samu asarar rai ko ɗaya ba sai dai dukiya. Abu mafi caja ƙwaƙwalwa ga kowa ma ba ita kaɗai ba shine jin wai wanda ya dasa bomb ɗin ya tsere Bayan wasu sun tabbatar da sunga fuskarsa da shigarsa motar, musamman ma wasu samari huɗu da suka tanbatar da tare suke da wannan mota tun daga ƙauyen Lufana da alama mutumin daga can ya fito. Tabbas sai tayi ajalin wannan mutumin a zuciyarta zataji salama. Dan a ganinta idan yau ya tashi kowa bai rasa ransa ba na gobe kuma fa? A wannan gaɓar ta fara zargin anya wannan sarkin bada wata manufa dama ya dawo ya karɓa mulkin mahaifinsa ba? Dan alamu sun fara nuna uban nasa ma shine ya kasheshi.

“Lokaci yayi da zan fara aikina gadan-gadan”.

Ta faɗa a zahiri cikin tabbatarma kanta da yanayin ɗaukar alwashi

A babban zauren majalisan manyan masu faɗa aji na daular ruman kuwa na can yana neman hargitsewa dangane da faruwar wannan al’amari. Kowa faɗar albarkacin bakinsa yake a duk yanda zuciyarsa ta ayyana masa musamman masu sukar mulkin Tajwar Eshaan a fakaice. Duk wannan kace nace da akeyi Tajwar Eshaan ɗin na zaune cikinsu amma uffan bai tofa ba har suka ci suka tsire. Sai da suka lafa dan kansu da kuma maganar Miran Arshaan cikin ɓacin rai a garesu sannan Tajwar Eshaan ɗin ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya gama ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya..

Akan Miran Arshaan dake cigaba da faɗa rai ɓace kan kausasan maganganu nasu ga ɗan ɗan uwansa kuma sarkinsu a yau basu dace ba ya sauke idanunsa. Cikin muryarsa mai zurfi da ƙasaita ya fara magana a gadarance kuma a fisge…

“Barsu Aami. Waninsu bazai canja komai ba, kamar yanda bazai tirsasa Eshaan yin komai ba. Abinda kawai nake son ku sani, Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed guguwace data gama turniƙeku, kuma babu ruwan kogin da zai iya shayar da ita ruwan da zata lafa. Ku daina bama kanku wahala ƙasar ruman da jama’ar cikinta a rubuce suke tsakkiyar tafin hannuna. Idan na murza kwafsanku kawai duniya zata gani a cikin guguwata, idan na matsa, jininku ne zai dinga ɗiga a ƙarƙashin sawun ƙafata na ringa bi ina takawa matsayin kwalta, ya rage naku ku zauna a inda na baku zaɓi ko ku zaɓo mummunan ƙaddararku da kanku tun lokacin ɓacewarku a doron ƙasa baiyi ba”.

Yana gama faɗa ya miƙe cike da takun Izza da kasaita ya bar falon. Da kallo duk suka bishi ran wasunsu na ƙuna, zukatansu kam tamkar zasu kifo ƙasa dan firgici. Cikin dauriya da nuna jarumta wani ƙyamusashen dattijo da tsufansa ya fara bayyana a cikinsu yay ƙwafa rai ɓace da kausasa murya.

“Lallai wannan yaron ya cika ya tumbatsa kuwa. Wai kenan haka zamu cigaba da zama yaro ƙarami na tafka kuskure da mulkin zalunci yana kuma takamu a yanda ya gadama. Akaf tarihin mulkin daular ruman ba’a taɓa tsageran yaro kamar wannan ba, amma ubansa ya ɗaura shi matsayin Shahan-shan bayan babu mai makamancin shekarunsa daya taɓa zama a wannan matsayin. lokaci yayi da zamuyi bore wajen tsigesa kafin ya gama halaka ƙasar baki ɗaya tunda naga shi ran ɗan adam ba’a bakin komai yake garesa ba. wama ya sani ko shine yasa a dasa nakiyar kamar yanda ya kashe ubansa da ƴaƴan mutane da aka aura masa. Koda yake minene ma na tantama tunda ga amsa ya bamu da bakinsa cewar ƙasar da ƴan ƙasar duk a tafin hannunsa muke”.

A zahiri dai kowa yay tsitt yana sauraren dattijon, amma a zukatan wasunsu farin cikine fal da zantukan wannan tsoho ga Tajwar Eshaan ɗin da mafi yawansu shakkarsa ta gama zagaye tunaninsu duk da kuwa kusan duk sun haifesa dan babu wani sa’ansa, dan har yanzu tun ƴan majalissar mulkin mahaifinsa ne bai canja ba. Dattijon na rufe baki Miran Jasim ya miƙe rai a ɓace shima. Dattijon ya watsama wani mummunan kallo da faɗin, “A lallai ka cika dattijon banza dan bazan kalleka matsayin Aami ɗinmu ba yau kam. Mun godema ALLAH daya fara nuna mana ku a zahiri, ai bamu san ɗan ɗan uwanmu ya kai muku har haka a zuciya ba sai yanzu. To ku sani duk ma mai irin wannan tunanin ya makaro, Eshaan kuma a gareku sai gani sai hange sai hararar nesa, dan badai mutum ba ku rubuta ku aje”. Ya kare maganar yana ɗan ƙyaftama Miran Arshaan daya saki baki tsabar al’ajabin ɗan uwan nasa da kasa fahimtar inda ya dosa. Cikin sauri ya kaɗan kansa da amshe zancen a fusace shima yana miƙewa. “Aam ai ban san haka kakeba wlhy sai a yau, ashe zaka zama na farko a jerin wanda zasu soki jinin Haysam Akhi kuma ɗan uwanka mahaifinmu dan ƙasa ta rufe idanunsu? To bazamu ce da ku komaiba a yanzu, amma kusani duk wanda yake da wannan ƙudirin a ransa jininmu fansa ne ga kare Eshaan tako wace fuska. Mun barku lafiya”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button