Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 70

Sponsored links

Wani bakon lamari ne ya ziyarcesu duka kowa da abinda yakeji, ita ji tayi kamar an zare mata laka jikinta yayi sanyi sosai amma batadena mutsu mutsu ba, shikuma Deen laushin jikinta ne ya tafi da imaninsa dan Allah ya sani karfin hali yayi ya samu ya zare wukar daga hannunta, ya kankameta kam kamar wacce zaa kwaceta…..

Murya chan kasa kamar mejin bacci yace;

“Ki nutsu dan Allah, karki jiwa kanki ciwo plssss”

Bata kulashi ba ta cigaba da fizge fizge burinta kawai ta kwace kanta daga wannan tight hug din dolen….

Tana cikin wannan hali taji an dage mata hijab, bata gama ganewa ba kuma taji kamar an chaka mata abu, kuka ta fashe dashi sosai dan a rayuwarta in akwai abinda ta tsana toh be wuce allura ba, bare wannan allurar batasan ta mecece….

Jin kukanta yake har cikin ransa saidai shine best solution daze taimaki situation dinta, patting back dinta ya shigayi sai bata hakuri yake ba tareda yasan abinda yake fada ba, suna cikin wannan yanayi yaji ana taba kofar parlourn !!!!!!…….

Juyowar da Deen zeyi sukayi ido hudu da mami da Umm da sukayi mutuwar tsaye a gurin suna bin parlourn da kallo da sakekken baki…..

 

Ba karamin tashin hankali Deen ya shiga ba da ganinsu saidai bazaka gane hakan a fuskarsa ba, sai a lokacin ya fara dana sanin kawota gidan bayan ya san mami tasan gidan, shi a plan dinsa ze mayar da ita a yau ya samu ya koma kafin su mami su gane ya fita ashe mahaukaciya ya dauko be sani ba, gashi yanzu har sun gane bayanan sun biyoshi, abun kunyar kuma sunganshi rungume da ita, shikuma ya kasa sakinta kamar wanda aka yiwa baki….

Har bayan minti biyar anrasa me magana tsakanin Umm da Mami, kowannensu was just speechless with lots of questions, kada ma Umm taji labari that was more than disappointed, koda yaushe ita take kare Deen idan mami na complain akansa, koda tana masa fada bata wani ganin stubbornness dinsa da mami ke fada sai gashi yau idanta ya mata kyakkyawan gani da batasan a mazaunin da zatasa saba, wai Deen ne rungume da wata haka? Yana ganinsu kuma ya kasa sakinta?……..

 

Itako mami rasa abinda zata kama tayi, gadai gida kamar anyi barin mahaukaciya ko film din dakin amarya albarka, toh wayayi wannan danyen aikin? Sannan kuma wacece haka da yake rungume da ita kamar zaa kwace masa ita?…

Itako mami rasa abinda zata kama tayi, gadai gida kamar anyi barin mahaukaciya ko film din dakin amarya albarka, toh wayayi wannan danyen aikin? Sannan kuma wacece haka da yake rungume da ita kamar zaa kwace masa ita?…….

 

Haka kawai zuciyarta ta bata suzo gidan dukda tasan bayanan dan baze zauna inda yasan zaayi saurin ganesa ba, but to her greatest surprise sai gashi sun samesa a gidan, a’a bama shikadai suka samu a gidan ba sun samu abubuwa dayawa, sannan ko ina is messed up bata inda zasu bi su karasa ciki ma, toh ya bazasu shiga shock ba?…….

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button