Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 48

Sponsored links

Mika masa wayar tayi tace…..

“Check your call log, I want to know the exact time!”…….

Taso ta duba a tata wayar saidai kash Iphone ce, ita kuma Iphone dauke past calls take musamman ita data kasance me yawan making calls saboda yanayin aikinta, shi kuma inda Allah ya taimaka Samsung yake using……

Karban wayarshi data kasance kirar ‘Samsung Galaxy Z Fold4New’ yayi, sannan ya shiga call log dinsa, scrolling down yayi har yazo gurin call din da yayi da ita, shiga kan call din yayi sannan ya mika mata wayar……

Karba tayi ta duba time din, har zata basa wayarsa idonta yakai kan sunan dayayi mata saving, da sauri ta dago ta kalleshi tace….

“You must be very stupid, nice ‘this woman’?!”…

Zaro ido Deen yayi, shap yamanta haka yamata saving gashi yanzu ya mika mata ta gani…..

Kafin yace me ya nemata ya rasa a wajan, sai a lokacin wani danasani ya kamasa, betaba ganin illar yanda yayi saving sunanta ba sai a lokacin, sosai yaji wani iri ranar, yaji kuma ashirye yake ya bata hakuri gashi kuma tariga tabar wajan, shikuma bashida damar fita…. Kwanciya yayi a kan gadon yana tinanin yanda ze shawo kanta, yasan mutum dayace kadai zata iya shawo masa kanta gashi bata kasar…..

Zuciyarta fess tabar office din daddy, dan tariga ta kudirta aranta ko yanaso ko bayaso saiya aureta, har lissafin yanda zamansu da mama a matsayin kishoyi ze kasance tayi, kwata kwata taki bawa zuciyarta damar tinanin halin da khaleel ze shiga, ba abinda ya shafeta da momma dama…….

Yananan inda tabarsa kamar tace masa ya jirata, shiga motar tayi tace masa ya kaita gidan daddy, dan so take tayi maza ta dau abinda zata dauka tabar gidan kafin a saki mama dan bataso su hadu sai ranar da zata kawo mata kayan fadar kishiya, tariga tasan yanda zatayi da daddy ya barta ta kawo kayan….

Kicibus sukayi dasu khaleel a compound din gidan, ita tashigo su kuma sun fito zasu tafi masallaci…..

Batace musu komai ba tashige ciki, da sauri khaleel ya bita ciki….

 

Sameer daya makale kamar gunki ya bisu da kallo, ko baa fadamasa ba yasan wifey din khaleel ce, aiko bazaiyi sake ba wannan karan, bibiyarta ze farayi a sirrince har yasamu burinsa ya cika…..

 

Smirking yayi jin wani shegen tinani ya fadomasa….

Driving take rai a bace, ace dan da ka haifa yayi saving sunanka da wani ‘this woman’?, me hakan yake nufi? Batada mahimmanci a rayuwarsa kenan?

Ita sai yanzu tagane Deen kamar playing dinsu yake daga ita har uban nasa, kullum sai tadinga ganin kamar ubansa ne ya janyesa shiyasa baya zuwa wajanta kwata kwata, ashe haka ubannasa shima yake tinanin ita ta janyeshi? Zatako kyaleshi har sai yagane kurunsa, sai ya tabbatar da bata da amfani a rayuwarsa, saita tabbatar masa da this woman ce ita…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button