Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Page 3

Sponsored links

Karfe takwas na dare ta bude ido tin bayan baccin daya dauketa, jinta tayi wani iri kamar wacce aka daukewa abu kamar dai ba itaba, juyi ta farayi a gadon kamar wata yar karamar yarinya, sai kuma chan ta tashi ta zauna……

“Har kin gama wasan?”…..

Deen ya tambaya, yana zaune chan gefe akan couch yana aiki da system, tindazu yake zaman gadinta wai kar wani abu ya sameta, su mami sunyi sunyi ya tashi su zasu zauna da ita yaki, haka suka hakura suka kyalesa dan yanzu sunyarda genuinely yakesan taimakonta, koda ta tashi akan idonsa ne amma yayi kamar be gantaba ganin itama bata san yana dakin ba.. Sosai ya fara shiga yanayi da take juye juye nan, yanda komai nata yake kadawa kamar tanayi da gangan, sai yaji tsigar jikinsa na tashi……. Kauda tinanin yayi ya dauko tray din abinci da aka kawo masa tin dazu beci ba ya nufi gadon…..

Zama yayi yana facing dinta ya debo abincin yakai bakinta, saurin kauda kanta tayi tana kallon gefe…

Dogon hancinta dayake bashi sha’awa yaja yana fadin;

“Your body said it all, your skin is so soft da an tabaki sai kisawa mutum kuka, harna fara tausayawa wanda ze aure ki wallahi zesha fama”….

Haushi maganarsa ta bata taji kamar ta dakesa, wai har kura yace da kare maye? Dama ance lefi tudu ne saika take naka kaga na wani, in banda haka duk muguntarshi be gani ba sai nata?….. Murguda baki tayi tace;

“Khaleel baze taba gajiya dani ba!”….

‘Taraaassss’…..

Taji karar fashewar kwanukan daya zubar dasu a kasa harda abincin gabadaya, da gudu ta fita daga dakin karya shaketa……

Huci ya shigayi kamar mayunwacin zaki, ya daga murya yace;

“I’ll get hold of you bitch!!”……

Sai kuma ya tashi ya bita da sauri….

Da gudu ta shige dakin mami, Umm dake zaune akan gado taji kamar an jeho mutum, rungumeta fatima zainab tayi tana boyewa a cikin jikinta…..

“Lafiya! Lafiya kuke guje guje haka? Da katawo nan ina zakayi?”….

Umm dataga Deen na kokarin hawowa gadon ta dakatar dashi…..

Kwafa yayi yace;

“Wallahi zan kamaki, sai kin maimaita abinda kika fada”…….

“Basai kazo ka kamata mugani ba, ko kunya bakaji kayita cin zalin yarinya, my friend get out!”….

Mami da fitowarta kenan daga toilet ta fada tana nuna masa hanyar waje……

“Ikon Allah sai kace wasu jarirai”…..

“Kema dai kya tayani fada, kome tayi ai be kamata ya biyeta ba tinda ba lafiya ne da ita ba”….

“Ni mamaki ma ya bani, Allah ya kyauta kawai”….

“Ameen”….

Dagota Umm tayi tana tambayarta me zataci, cewa tayi batajin yunwa ita bazataci komai ba, lallabata Umm tayi da kyar ta yarda taci kadan, shi dinma saida ta bata a baki…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button