Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 33-34

Sponsored links

Shuru yayi ya tsaya Kamar gunki sai da ya gaji ya shiga motarsa ya fito daga layi ya nufi inda yasan muna tsayawa,tun kafin ya karasa ya hangoni da tsinannun Kaya a tsaye, a gabanmu yayi parking ya bude mota ya fito,ina ganinsa haushi ya kamani na zumburo Masa baki.

Tsawa ya buga min Shiga mota muje,harara na watsa Masa Ina dire diren kafafu nace ni Allah bana so na gaji kamar Ina prison ni ko kudin ne bana so ka barni nayi rayuwata kaje kayi taka,mota nace ki Shiga ya furta Kamar zai dakeni sauran karuwan suna kallonmu baki bude, hannuna ya fisga ya jani na tirje ni ka kyaleni bazan je ba,Ina tirjewa harna zube a kasa Ina ta burburwa Ina Shure shure,Tsaki ya ja ya sakar min hannu,sai ya daukeni cak Ina wutsil wutsil ya bude gaban mota tare da jefa ni ciki ya rufe ya Shiga mota yaja muka wuce gidan dai da ya ajiyeni,Yana yin parking ya fito na fito Zan sake guduwa tsawa ya buga min na tsaya cak tare da juyowa yace come karasawa nayi gabansa Ina Kunkuni mari ya kwada min na dafe kumatuna da sauri na kalle shi cikin karaji yace Ina alkawarin da Kika min Zaki zauna? Mene a cikin karuwanci,karuwancin ma na titi ke bakya Jin kunya musulma dake hausa Fulani mene birgewa a karuwanci,bance Miki Zan biyaki kudi ba,har albashi na saka Miki duk wata, nace Zan maidaki school dan Kawai na inganta rayuwarki ba sonki nake yi ba karki Raina min hankali wallahi Kika sake barin gidan nan ba izinina sai Kinga abinda zan Miki useless girl baki San ciwon kanki ba kina yamace kalleki karuwanci bai dace dake ba,kuka zanyi Masa nace ai ni Kawai so nake nayi Ina so ne sai naji Ina son Karuwancin,shut up ya buga min tsawa shashasha wacce bata San darajar kanta ba wuce ciki,tsayawa nayi ya buga min tsawa shiga nace ya furta a tsawace, da gudu na fada ciki,Yana shigowa ya matso kusa dani ihun tsoro na saki na ja baya Kar ya dukeni, yace karki sake karki sake, kika sake zaki ga ba daidai ba yaja tsaki ya koma wajen me gadi yace idan ka sake barinta ta fita a bakin aikinka,Ilu yace Zan kiyaye, ciki ya koma Yana shiga yace tashi ki canja Kaya wannan yan iskan kayan sai na Kona su mijinki Kawai Zaki sakawa,tashi nayi Sadaf Sadaf na koma na canja silk material marar nauyi na fito,Ina Fitowa Kamar ba nice ya gama zazzagawa ba nace abinci fa a dafa,shi da Kansa a ransa yace bata da zuciya ya tabbata da wata ce ranar ko kulashi baza ta sake Yi ba ko matarsa ai sai suyi watanni tana gaba da shi,yace kin bani ne abincin,sum sum na Shiga kitchen na Masa jullof din taliya ta Sha kifi da kayan lambu, kawo Masa nayi har gabansa nayi serving dinsa Nima na zuba tawa Muna ci muna kallo,yace baza ki fada min wace ke ba I mean tarihinki,Ina cin abincina Ina bashi labarina komai ban boye Masa ba,yaji tausayina da yaji bani da kowa a duniya Yar tsuntuwa ce Ni,yace Kuma shine baza kiwa maraicinki gata ba ki Zama ta gari sai ki lalace,Shuru nayi Ina jinsa yana ta min fada ni dai bance komai ba, yace gobe ki shirya gidana Zan maidaki,kallonsa nayi nace matarka fa ni kasan bani da kunya Kar nayi abinda zata ji haushi in ta min ba kyaleta zanyi ba kasan halinmu,ai yar aiki Zaki zama aiki Zan daukeki tunda kince ke baza ki aure ba baza ki makaranta ba Mene amfaninki Kawai na kaiki can kiyi aiki ki gyara gida kiyi girki,nace yanzu Yar aiki zan koma haka gaskiya tace? Cutar dani zaka yi,ko baza ki abinda nace ba? Kamar zanyi kuka nace zanyi,Kuma kina kwalliya zata ce kwace Mata miji Zaki Yi ta Miki dukan tsiya,Nace wlh sai dai na daketa Kai kasan karfina kuwa hmm amma tunda kace nayi zanyi ai zaka biyani ko? Yace kudi ma Zan Kara miki, ihu na saki nace wane ni nace bazan Yi ba ai ya Zama dole,yace Good girl Kinga mun huta da tsoron shedan,ka huta dai Amma Ni kaina ai shedaniyace me zaman kanta na furta,yace to babu kyau dai kebewa mace da Namiji shi yasa Zan maidaki a matsayin Yar aiki sabo da dangina da iyayena da matata ce za a dameni amma idan a Yar Aiki Kika je sai kiyi zamanki a haka dama aikinki kenan aikin gida da girki,nace rashin yanci dai ya Kara tabbata a kaina ka bari sai jibi to na Kara hutawa,yace Allah ya kaimu.

 

Washe gari a gidan ya kwana Sai ga su Sera su bakwai sunzo gidan da kyar Suka gane gidan sabo da na taba fadawa Sera address,da masifa Suka shigo suna kwala min Kira, miracle…Miracle.. na fito Suka hauni da masifa Zaki tafi baza ki dinga fada Mana ba sai mu dinga tunanin saceki akayi,Nawwar ne shima ya fito a tsaya a gefena tare da harde hannayensa a kirjinsa, ni Kuwa nace yarinya ce ni da zan bata kunzo Kuna min ihu a gida,Nawwar sanye cikin kayan baccinsa Yana jinsu suna cewa Kai karfa ka rabamu da yarinya abin ya isheka haka,da sauri nace Sera zanyi diban albarka a nan wlh ki tsaya haka, Kar wacce ta zagi saurayina yarinya ce ni da zaku zo Kuna min ihu,wannan ba Kalar Yan iskanku bane ku Shiga hankalinku,Au haka Kika ce? Nace ae kuje gida idan na gaji zanzo ai Kun ganni kalau nake,Sabo da haushi juyawa sukayi Suka tafi suna masifa, suna tafiya ni Kuma na juya Muna facing juna Ilu dai tana kallo,nace karka damu dasu kayi hakuri ko me kake so zanyi Kai mutumin kirki ne,Shuru ya min na shafa gemunsa nace inya…. inya… inya….dariya yayi ba shiri nace muje ciki na ja hannunsa muka shige ciki,Muna shiga na rungume shi nace kayi hakuri kaji, jikinsa ya janye da sauri yace naji na hakura ki daina tabani nace fa bakya ji, kasan me na furta Ina gabansa a tsaye muna facing juna nace kana da kyau,idanuwa ya lumshe tare da furta ba kya ji,dariya nayi Ina kida baki na shima dariya abin ya bashi yace kin haukace maybe.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button