Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 29

Sponsored links

“”Dauki petrol dinnan ka watsa minshi a ko ina na building dinnan”….

 

“Ban fahimceki ba hajiya” Ya fada a diririce ganin fatima zainab na ciki dan yaga shigarta,yana zaune kuma bega ta fito ba

 

Wankeshi da mari mama tayi tace “Dauki ka zuba nace,ko a bakin aikinka wlh”…..

Dafe inda ta maresa yayi ya shiga bata hakuri yana fadin “Da mutum fa a ciki hajiya”….

“Eh ai nasan da mutum din,konata zanyi”…

“Dan Allah dan annabi hajiya kiyi hakuri karkiyi kisa”…

“Ina ruwanka dan ubanka,zaka zuba ko kuwa?”….

A guje ya fita daga gidan ganin kiri kiri zaa sashi yayi kisa,shiko da yayi wannan danyen aikin gwara ya rasa aikin kawai…..

Kundume kumdume mama ta hau yi ganin ya fita a guje,nan ta dau petrol din ta hau watsawa a ko ina na building din,da yake kamar isolated site haka yake a gidan,shine gini na karshe kuma da tazara da sauran……

Saida ta tabbatar ko ina ya juku da petir sannan ta kyatta ashana,take ko ginin ya kama da wuta,budar bakin mama ta furta “Alhamdulillah” tanajin wani sanyi a ranta,sun rabu da alakakai!!!!

Wata muguwar dariya mama ta sheka ganin gidan sai ci yake da wuta,gashi ba kowa a gidan dama,me gadi kuma ya gudu…. Fadan irin farincikin da mama take ciki bata baki ne,sai yau taji hankalinta ya kwanta tin bayan shekara shida da suka wuce,ga alhaji nan ya zama sai yanda tayi dashi ga wannan munafukar ta kone mururus, itako meya rage mata a rayuwa banda taci duniyar ta da tsinke?…… Tafin murna tashigayi fuskarta dauke da annuri sosai……

Driving yake a haukace kamar ze tashi sama waya rike a hannunsa,tinda me gadi ya kirasa ya fadamasa kudirin mama be kara samun nitsuwa ba,kiran duniya yayiwa fatima zainab amma bata dagaba gashi kuma waya na ringing,rashin dagawarta ya bala’in tada masa da hankali,gashi yayi nisa sosai da gida….. A 360 yake driving amma ji yake kamar baya tafiya,a yau da yanada dama daya zama tsuntsu ya tashi ko ze samu ya isa gida da wuri,momma dama bata gida tayi tafiya,daddy ko yana office,megadi ya kuma tabbatarmasa da Fatima zainab na ciki a yayinda mama ke kokarin aiwatar da kudirinta… Number daddy ya soma kira saidai sam yaki dagawa kamar yanda ya saba masa a yan kwanakinnan tun bayan dawowar mama,changa akalar kiran yayi zuwa number yayansa dukda baya kasar….. Khaleel na dagawa abdul ya shiga masa bayanin da bala megadi ya masa,ba karamin tashin hankali khaleel ya shigaba dan yana tsaye saida ya zube a kasa,umartar abdul yayi da yayi saurin karasawa while shima ze cigaba da trying numberta,tabbas in wani abu ya samu fatima zainab yasan rayuwarsa tazo karshe dan baze iya rayuwa ba itaba……

Haka abdul ya cigaba da driving still yana kiranta a waya…. Kamar a mafarki yaji ta daga wayar,murya na rawa yace

 

“Anty anty ki bar part dinki yanzu,mama ta siyo petrol wai zata konaki,megadi ne ya kirani ya fadamin”……

 

Shiru tayi batace komai ba,jin tayi shiru hankalin abdul ya kara tashi,cikin muryar wanda ke shirin kuka ya kuma cewa

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button