Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 17

Sponsored links

Daneen Ammarah da dama sanin fushin malikat Bushirat ɗin kan al’amarin ya sata tada hankalinta ganin an kusanto da Iffah ga Tajwar Eshaan tai ɗan murmushi, tasan kalamanta sunyi tasiri, sai dai ba tasirin da zai iya ruguje abinda take son ganin ta ruguje ɗin ba (Wato ƙiyayyar Iffah a zuciyar Malikat Bushirat a yanzun). Kanta ta ɗan rausayar tare da kallon Tajwar Eshaan da yay kamar babu shi a ɗakin, dan idanunsa ma a lumshe suke kamar wanda barci ya ɗaukesa. Juyawa tai ta fice a binta itama zuciyarta cike da ƙudirin tsayuwar daka domin tabbatar da gaskiya da kuɓutar da yarinyar da takejinta har cikin ƙasan zuciyarta.

Idanun ya buɗe kaɗan ya bita da kallo tamkar yanda itama Malikat Bushirat ɗin data gagara iya cewa komai ta bita da kallon..

 

*_“Hummm!! Bazan iya hakuri ba sai na tofa”_*

“Idan nace Humm fa ina nufin Humm da gasken gaske. Idan har Iffah ta rayu yaya kuke tunanin a yanzu salon zamanta zai kasance da uwar mijin nata mai tsananin ƙarfin iko? haka koda an tabbatar da jagororin abinda ya faru ta dalilin nata. Masu karatu akwaifa cakwakiya, dan yanzu salon zai fara a ƙarƙashin abu uku ne, da zaku iya canko min su dana baku babbar ƙyauta😉😁🥱”.

 

★…. TA-ƘURYA ★…..

 

“Na daɗe da faɗa miki wannan yarinyar hatsabibiya ce kar ki sakaci da rauninta na kasancewa mai ƙarancin shekaru ko ƙanƙanta sama da ƙarfin ikon ki ta-ƙurya?. A duniyar cikar buri raina abokin karo kuskure ne kuma ganganci ne da kan iya rusa duk wani ginin da aka faro komai tsahon shekarunsa…..”

Ta-ƙurya da ke gurfane gaban Uwa cikin jin raɗaɗi a zuciya ta ɗago idanunta da launinsu ya koma jazur, cikin rufewar idon irin na mai ɓacin rai da manta wake a gabansa ta ce, “Mina gaza Uwa?! Minene ban bi ba a dukkanin sharuɗan ki a shekarun nan? Miyasa matsala bata kasance abokiyar gogayya ta ba sai a lokacin da zan girbi shukar dana ɓata tsahon shekaru wajen yimata barruwa? Miyasa? Miyasa?. Na ce miyasa hakan ne?!. Miyasa sai da na yarda na rasa komai domin samun abinda nake kallo komai a gareni sannan zaki hana mini? Ke ce kika ce karna taɓa kokwanto bazaki taɓa barin zubar waɗan nan hawayen da a yanzu suke kwaranya akan fuskanta ba da ga gareni. (Wa’iyazubillah 😭🙏). Miyasa? Miyasa a yanzu sabanin hakan nake gani? Yarinya ƙarama da bata wuce na murjeta da tsinin takalmina ba ta shigo rayuwata da barazanar yin kutse akan nasarata. Idan tafi ƙarfinki ne ki faɗa min danni batafi ƙarfi na ba, babu wata uwa data haifi ƴa ko ɗan dazai zama barazana akan cikar burina, in ko uwar ta haifosa har kuma ya kwatanta zan shafe babin zuri’arsa kaf da babu wani abinda za’a kalla a tuna su kuma. A yanzu kam zanyi yaƙin da hannayena dan bana buƙatar k……”

“K!! Ta-ƙurya ki dawo cikin hankalinki, kalleni da ƙyau ki san a gaban wa kike? Uwar mugu nake bata sakarai ba. Banyi lalacewar da ke zaki ci tuwo a kaina ba koda kuwa tuwun na ƙasa ne mai sauƙin wawaso. Idan kuma zaki gwada ga fili ga mai doki”..

Cikin nuna halin ko gezau ta-ƙurya taja tsaki mai tsananin sauti dai-dai lokacin da Uwa ke ɓacewa daga idanunta rai a ɓace. Ta rakata da harara tana mai miƙewa da ga durƙuson da tai. Waya ta fusga cikin tsananin fusata ta hau danne-danne tana kai kawo a katafaren ɗakin…

Alhamdullah a daren yau likitoci suka sami nasarar dawowar Iffah dake cika kwanaki huɗu hayyacinta, zuwa safiya kam sai dai ace Alhamdullah duk da bawai tana a cikin ƙarfin jikinta bane ko warkewa sarai kamar yanda take a baya. Daneen Ammarah har da kukanta na farin ciki, bata ɓata lokaci ba wajen sanar ma Malikat Haseenat. (Alhamdullah) ta dinga jerawa itama tare da jin nutsuwa na saukar mata, dan tunda yarinyar nan ta tsinta kanta a halin nan hankalinta ya gagara kwanciya.

Malikat Bushirat duk da labarin farkawar Iffah ya zo har kunenta ta hanyar doctor Afif batace komai ba hakama bata leƙa dubata ba, sai ma yazam a safiyar ranar har zuwa yamma bata leƙa sashen Tajwar Eshaan ɗin ba gaba ɗaya, ta dai kira waya domin jin cigaban lafiyar jikinsa. Shi ɗin ma dai bai shiga duba Iffahn ba sai yamma duk da kuwa jiyan ma a gaban idonsa ta farfaɗo, Sannan har yanzu jikinsa babu ƙarfi shima, dan da gaske gubar da suka haɗa da dafin macizan ta so masa illa ƙwarai da gaske tunda gashi ma har sai da akai masa aiki dalilin taɓa wani sashe na jikinsa data so tayi saboda ƙarfinta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button