Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 52

Sponsored links

Kalmar ta fito da ga harshensa a ɗan fisge tamkar wanda akaima dole. Batare da ta yarda ta kallesa ba ta ce, “Suna da yawa, muhimmai a cikinsu dai yanzu duk sun shafeka”.

Wani kallo da ke nuna alamar ni ɗin yay mata. Tako ɗaga masa kanta idanunta na ɗan cikowa da hawaye tana ƙiƙƙifatasu. A raunane kamar ba ita ba ta ce, “Ina son sanin halin da Iyayena ke ciki duk da an sanar min ka halaka su. Ina son sanin wanene Ajmaal?. Ina son idasa tabbatar da masu fuska biyun daular ruman wa duniya koda ni bazan iya wanke kaina ga kowa ba”.

Yanda yake kallonta kamar wata sabuwar halitta sai ka ɗauka idanun nasa sun kafe ne a kanta. A hankali ya ɗaga kafarsa yay ɗan taku ɗaya zuwa uku, a gabanta ya dakata gab-gab kamar zai haɗe jikinsu. Sai dai kuma baiyi hakan ba ya ɗan bar tazarar da bata wuce tsahon yatsa manuniya ba. Da sauri-sauri ƙirjinta ya hau dokawa ganin ya mata runfa, dan duk da kasancewar ta mai ɗan tsayi a gabansa ba komai bace duk da shima ba wani dogo bane na bala’i can, sai dai kuma dole a kira shi da dogon. Kamar yanda yake duban cikin idanunta haka itama ta ke dubansa, sai dai nata cike suke da ƙwalla ga tsumar da jikinta keyi ta kasa janyewa. Hannunsa ya dogare jikin lafiyayyar ƙofar mai tsananin ɗaukar ido, sai hakan ya sake bashi damar rufeta ruf har tana jin shaƙar numfashi ma na neman mata wahala tsabar yanda kwarjininsa ya cika mata ko’ina, har ji take kamar ma ɗakin ya musu kaɗanne.

Rasa abin cewa ya sashi ɗaura yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau suna kallon juna, nasa ya sake lumshewa da sake buɗe wa a cikin natan cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara ya furta.

“Bayan kin cika waɗan nan sai me kuma?”.

Yanda yay maganar yana mai sake sarƙe kaifafan idanun nasa cikin nata da ke tara ƙwallar da bata san dalili ba ya sata shiga jujjuya masa kanta a hankali idanunta na sake cikowa da ƙwalla dan jin kusancin nasu take kamar wani dabaibayi da ya fi ma zamanta a kurkuku. Lips ɗinta ta motsa a hankali, cikin raɗa-raɗa muryarta na ɗan rawa ta furta, “Yi maka hukunci akan laifukanka”.

Da ƙyar ya iya haɗiye murmushin da ke ƙoƙarin yinƙuro masa. Sake matsar da fuskar tasa yay gab-gab da tata, hakan sai ya sake hauhawar bugun zuciyarta har yana iya jiyo yanda nunfashinta ke fita a sarƙe. Amma sai ya fuske abunsa ya cigaba da jujjuya nasa ƙwayoyin idon a nata cike da wani irin salon da ke neman fallasa sirrin da yake faman dannewa a ƙasan zuciyarsa.

“Bayan hukuncin da kikai min na son kasheni duk bai isa ba *_Niazmina_*?”.

Idanunta ta waro a matuƙar razane, tari mai ƙarfi ya sarƙeta, dan maganar tasa tazo mata a matuƙar bazata. Duk yanda yaso shanye dariyarsa a wannan karon hakan ya gagara har sai da lallausan murmushi ya suɓuce masa. Sai kawai ya jawota ya manna da jikinsa ya cigaba da yin abunsa dan ya kasa riƙewar..

Sosai take tarin har sai da ya janyeta suka koma bakin gado, shi dai murmushin sa kawai yake yana cigaba da shafa bayanta. Sai da ya ɗan lafa mata ya ɗauka tambulan ɗin ruwa da ke a side drawer ya tsiyaya kaɗan a ƙaramin cup. Ɗagota yay, batare da yayi magana ba ya ɗaura mata akan lips ɗinta. Da sauri ta shiga sha ƙwallar da ya cika idanunta da yay jajir na cigaba da sakkowa. Sai da ta shanye tas ya janye yana ƙara tsuke fuska kamar bashi ne ya gama murmushi ba yanzun. Ƙin yarda tai su haɗa ido, sai ma ta zame ta kwanta abunta ta juya masa baya. Shima komai bai sake ce mata ba yama miƙe.

“Dan ALLAH kada kaje zasu cutar da kai, dan sun saka abu a ƙasan kujerar zamanka”.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button