Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 37

Sponsored links

Juyawa yayi ya shige work room dinshi dake nan parlourn, computers ne a zube kala kala sai wasu drawers a jere daga gefe, jan kujera daya yayi ya zauna sannan ya kunna system din, saida yayi rebooting system din kafin yayi connecting tracker a jiki, saita komai yayi sannan ya dauko phone number dake cikin wayar Umm daga contact list dinsa na kan computer, imputing yayi ya kurawa system din ido ganin abun yana processing……

Ya fada yana dukan table din bayan abun yasamasa invalid means wayar a kashe take kenan, hargitsa gashin kansa ya shigayi frustratedly kamar yayi kuka, chan kuma sai ya kunna computer dake gefen wannan, latest calls din da akayi a wayar ya fara bibiya ko Allah zesa ya samu wani information ta nan, yana dubawa yaga ankira wata number kusan so biyar kuma shine last call din da akayi a wayar, sauran calls din da akayi a wayar ya kunna yaga duk office discussion ne kuma da Umm ne, dawowa yayi kan last call din ya dauki number yayi transferring dinshi to the next computer dake gefe saboda ko wani computer akwai abunda akayi designing dinshi yayi, information din me number ya duba sai gashi ‘Ibrahim khaleel Ibrahim’ yayi appearing, dukan system din yayi ya dafe kansa cikin tsananin bacin rai yace;

 

“I knew it! I knew it! Ni nasan shi kikabi, why are you so stupid bitch! Meyasa zaki bishi? Meyasa zakimin haka? Yanzu da kika bishi sai kuje kuyi aure da gaske? Inaaaaaaaa! Wallahi baku isa ba! Where are youuuuuuuuuu! I’ll make sure I slaughter him duk inda na ganku, kai dole in nemo ku ko ina kuka je, Why are you so senseless baby girlllllllllllllllllll!”…

 

Sai kuma ya fara hargitsa dakin yana neman wani encrypted tracker dinshi da ake tracking waya ko a kashe take, saidai sama da kasa ya nemeshi ya rasa, kamar yayi ihu haka yakeji ya dai daure ya cigaba da nema, yana cikin wannan dube duben hannunshi ya tabo wani flash, dauka yayi ya shiga jujjuyawa yana tinanin a ina ya samo shi, gashi it looks like bayanan sirri ne a ciki dan haka ake encoding dinshi, har ze cillar wata zuciyar tace yayi playing dinshi yaga menene a ciki, zirawa yayi a wani system ya dan nitsu yana duba abubuwan dake ciki, kunna first voice message din yayi yana sauraran abinda ake cewa……..

At first nitsuwa yayi yanason tantance muryar waye but it gets to a point daya sake baki yana kallon system din……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button