Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 111

Sponsored links

Sandarewa tayi a tsaye tsabar shock din data shiga, tunda take baa taba fadamata maganar daya mata zafi irin wannan ba, tsabar yanda maganar ta daketa sai taji komai ya kafe mata, ga tarin maganganu a bakinta amma maganar taki fita, she thought she just dislike him amma yanzu tagane this is more than dislike, it’s what we called ‘intense hate’ tsana sosai, bata tabajin ta tsani mutum kamar yanda takejin tsanarsa har kasan zuciyarta ba, yaci mata mutunci iya cin mutunci da ko a mafarki bata taba tinanin wani ze kalli idanta ya fada mata abinda ya fadaba kome tayi, hardasu ce mata whore(karuwa)? Kamar ya taba kamata da wani?…….

“I said GET OUT!!!”….

Firgit ta dawo daga maganar zucin da take, tafiya tashigayi a hankali harta karasa bakin kofar, sai a lokacin ta juyo ta kalleshi tace;

“Let me make my own confession too;I hate you! Natsaneka irin tsanar da ko kasheka naga zaayi zan bada gudunmawata, I hate you is an understatement!, dama bani na gayyatoka cikin rayuwata ba kaika gayyota kanka amma dukda haka zan bace bit daga rayuwarka kamar yanda ka bukata, don’t forget that I hate you so much, bye!!”……….

Tana fadin haka ta fice holding her self so tight not to breakdown……

Yana tsaye a inda ta barshi hartayi slamming door din bayan ta fita, sai yashiga tambayar kansa ‘can he really let her go a wannan condition din?’… ‘Does she really mean what she said, wai ta tsaneshi?’… Toh ai shi bece ya tsaneta ba, sai yakejin maganganunta kamar sunfi nashi zafi dukda abinda ya fada yafi nata yawa, babban abinda yake masa ciwo kuma yanda take jaddada masa ta tsanesa, babu wanda ya taba gayamasa ya tsanesa despite the way he always mess up sai yau wata da besan WACECE ITA BA take gayamasa zata iya bada gudunmawa a kashesa, how cruel!…… Amma kuma sai yaji he can’t let her go dukda tace ta tsanesa, tausayinta yakeji har cikin jikinsa kodan health condition dinta, she needs someone to be there and he wants to be there, wata zuciyarce tace masa ‘she hates you!’ dayar kuma tace ‘she needs you’…. Rasa abunyi yayi at the end ya bawa daya zuciyar dama, kawai ya fita yabi bayanta da sauri hoping to see her karta bace daga rayuwarsa kamar yanda ta fada…….

Ajye wayar yayi har lokacin hankalinsa yaki kwanciya da daddy, ita kuma ya mata tambayar duniya tace batasan abinda yake faru ba…..

 

A hankali take tafiya kasancewar batajin karfin jikinta har lokacin, haka ta daure harta karasa bakin gate din asibitin, rasa yanda zatayi tayi dan jakarta na motar khaleel bare ta hau cab ta wuce ko kuma ta kirasa a waya, wata ce tazo wucewa fortunately ta mata sallama, sai tayi using opportunity din tace ta ara mata wayarta tayi kira, ba musu kuwa ta bata, number khaleel ta kira dan ta haddaceta da dadewa, bugu biyu ya dauka ta masa bayanin inda take bayan ta karanta sunan asibitin, mikama matar wayarta tayi ta samu guri ta jingina tana jiran isowar khaleel

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button