Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 88

Sponsored links

“Su waye ku? Miyasa kuka kawoni nan? Mina muku?”. Barrister ya faɗa yana mai bin zaratan samarin da kallo harma da ɗakin da suka kawoshi mai ƙarancin haske gashi a ɗaɗɗaure a kujera. Fahimtar bazasu bashi amsa ko ɗaya ba daya bukata ya sashi cigaba da magana a hasale. Dan shi mutum ne mai saurin fushi musamman akan gaskiya da mai gaskiya. Baya son zalunci shiyyasa ko baka da ƙarfi zai tsaya maka akan haƙƙinka in har ka kasance mai gaskiya.

“Idan ma akan case ɗin nan ne kuke ganin sakayeni ko ɓadda rayuwata zai baku damar yin yanda kuke so akan bayin ALLAH da basujiba basu gani ba ku sani ni bamai hukunci bane. ALLAH shine mai hukunta kowa, zai kuma iya kawo wanda ya fini ƙarfi ya cece su”.

Yanzu ɗinma dai babu alamar wani a cikinsu zai tanka masa. Idanunsa ya rumtse zuciyarsa na masa ƙuna. Bashi da wani buri yanzu a duniya sama da yasan asalin tushen wannan case ɗin nasu Babiy, yayi alƙawarin tsayawa da ƙarfinsa dana aljihunsa insha ALLAHU.

Har dare babu wani haske daya samu dan har lokacin yana a ɗaure, sai da aka kira sallar magriba ne suka bashi dama yay salla harda isha’i. Hakan ya ɗan sassauta masa zuciya, dan koba komai damar yin salla da suka bashi yaji a ransa masu sassauci ne. Abinci suka kawo masa basu sake ɗauresa ba, sai dai yaƙi yako kallesa hakan yasa suka sake zuwa kusan ƙarfe tara agogon ƙasar suka sake ɗauresa sukai ficewarsu da kullesa ta baya. Babu irin tunani da takaici da baijiba amma ya cigaba da ambaton sunan ALLAH dan yasan shine kaɗai zai kuɓutar da shi a wannan gaɓar.

Kusan ƙarfe sha ɗaya gyangyaɗi naɗan kwasarsa yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar, idanunsa ya buɗe duk da baya iya ganin mai shigowa saboda ƙarancin hasken ɗakin. A ɗan hasken ya fahimci yanzu mutumin uku suka shigo, wanda ke gaba kuma da alama ogansu ne dan yanda ya shigo da takun izza cikin ɗakin. Da sauri suka ajiye masa kujera ya zauna yana mai facing ɗin Barrister yay wani irin zaman ƙasaita yana ƙarema Barrister ɗin kallo ta cikin glasses ɗin daya toshe idanunsa….

“Miyasa kuka dauresa?”.

Ya faɗa a kausashe. Kame-kame yaran nasa suka fara kowa na ƙoƙarin kare kansa. Yaja tsakin daya sakasu nutsuwar dole yana mai faɗin, “Ku kwance sa”. Bayan an kwance Barrister ya sake bada umarnin a bashi abinci da ruwa. Barrister dai kallonsa kawai yake da mamakin wannan izza tasa. Baiyi niyyar cin wani abu ba dan haka yay saurin faɗin, “Bana buƙatar wani abinci. Kusanar min kawai dalilin da yasa kuka kawoni nan da kuma inda nake dan ALLAH”.

Har Barrister ya fidda rai ga samun amsa yaji an karɓama zancensa a kausashe. “Barrister Abdallah Aas ba shiririta ta kawoni nan ba. Dan na baro abubuwan da suka fika muhimmanci nazo nan. Duk da rayuwarka ce ba sanin inda kake ko sanin mu su wanene ba matsalarka. Dalilin kawoka nan kawai zaka iya sani, damar hakan kuma na hanunka ta hanyar bin umarninmu”.

Haka kawai kwarjinin wannan mutum da ko fuskarsa Barrister baya gani da ƙyau yay matuƙar mamayesa, duk da yanaji a ransa ba alkairi yasa suka kawosa nan ba sai yaji bazai iya jayayya da shi ba. Cikin sanyin jiki ya fara cin abincin, yaci kusan lauma bakwai yasha ruwa duk suna a ɗakin. “Na gama”. Ya faɗa cikin sanyin murya.

“Good for you”.

Aka bashi amsa cikin halin ko’in kula. Sai kuma yay shiru kamar baida abin faɗa kafin yaja numfashi cike da isa ya fesar.

“Lokacina ƙurarrene dan haka bani da lokacin cigaba da ɓatashi a rikeka nan. Aiki zakamun baka da kuma zaɓin cewa e ko a’a. Nasan kasan Barrister Akeem Ibn Behnam”.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button