Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 107

Sponsored links

“Nace maka auren ku ake daurawa”…….

“Wifey is that so?”……

“No! Ba auren mu ake daurawa ba and I don’t know what’s going on here too, I just found myself here!”…..

“Dad just know that I’m not ready to listen to you in kasan bazaka fadamin gskyr abinda kuke shiryawa ba! Wifey taso mu tafi”……

Ba musu ta mike tabi bayansa suka fita daga parlourn……….

“Yanzu kana ganin danka ya fita da ita amma bazaka tsawatarmasa ba? Yanzu wannan shirin shima ya kara rugujewa kenan?! Alhaji Ibrahim you’re playing with your life! Ku tashi mu tafi!”……..

Cewar alhaji habibu rai bace…..

“Dan Allah ku zauna mu nemo solution, ku bani last chance nayi alkawari ba zaa kara samun matsala ba……….

“Bamu da wannan lokacin yanzu, mu hadu a house anjima kawai!”……

Tinda suka fito daga part din daddy aka rasa me magana a cikinsu, kowanne yayi shiru yana fama da abinda yake tinani….Shi khaleel na tinanin abinda su daddy sukeyi dan haka kawai zuciyarsa taki aminta da abun alkhairi suke kullawa, harda masa karya wai aurensa ake daurawa ya tambayi fatima zainab kuma tace ba haka bane, she even seem so lost kamar batasan abinda ake ba tanadai zaune ne a gurin…….

Ita kuma tinanin irin ramar da taga khaleel yayi take, tabbas taso taje ta dubasa dukda batayi tinanin ciwon nasa yakai har yayi rama haka ba…….

Dagowa yayi yana kallon yanda dimples dinta yake lotsawa a yayinda take dariyar, be taba sanin tanada dimples ba sai yau, toh ta ina ze sani shida be taba ganinta tana dariya ba?…. It felt like a dream come true, yanzu addu’ar shi daya Allah ya dasa mata koda rabin son da yake mata ne, har imagining suna soyayya me zafi ya farayi……..

““Your beautiful laugh makes my heart melt; I can’t imagine a life without you. I love you dearly.”

“Bafa zan karanta komai ba, dan Allah ka fita ka bani guri, why do you talk too much?”…..

 

“Sorry, sorry, yanzu zan fita”….

 

Ya fada yana stammering ganin yanda ta fara zuciya daga magana kadan, kamar ba itace harda ce mishi he’s so sweet dazu ba, well koma menene shiya janyo daya sata surutu kuma yasan bataso saboda yaga ta kulashi yau……

Fita yayi da niyar yaje ya siyo mata handouts din koda bazatayi karatun ba kamar yanda ta fada, sannan ya kamata ya binciko mata time table dan yasan kila batasani ba…….

Yafi awa daya yana tafiya batareda yasan inda ya dosa ba, tsabar bacin rai ko gajiya beyiba saima wani karfi daya keji na karuwan masa, burinsa kawai ya samu abinda ze buga ko zeji sanyi a ransa, haka ya taka da kafa harya karasa gidansa… Knocking ya shigayi da karfi me gadi ya taso ya bude yana fadin “waye haka?”

“Ubanka ne!” …..

Ya fada yana hankadashi gefe, Allah ya taimakesa beji ciwo ba, ko bi takansu Deen beyiba ya shiga ya dauko mukullin daya daga cikin motocin dake gidan ya fito ya shiga yaja ya bar gidan……

Driving ya shigayi recklessly kamar wanda yake a cikin maye, duk inda yabi saidai a kauce masa tsabar yanda yake sharara gudu, a haka yayita tuki har Allah ya taimakesa ya isa kano, shida be taba driving daga abuja zuwa kano ba, sai gashi bacin rai yasasa yayi be sani ba…….

“Ya mukayi da kai akan Hamida last time?…….

Dad daya keta zazzaga masa masifa tun bayan sun hadu a parking space har suka shigo parlournsa ya tamabaya…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button