Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 68

Sponsored links

me gadi hannun alamun ya dakata basai ya karaso sun gaisa ba……..

A kan three sitter ya kwantar da ita yana kallonta, so yake ya koma base gudun kar sameer yazo be gansa ba, sai ya masa karya yace be ganta ba toh amma gaskiya yana tsoron barinta ita kadai musamman idan ya tina encounter dinsu da wanchan mahaukacin, wannan wani kalan dilemma ne? Yanzu wanne zeyi a ciki?….

Ya dade yana sakawa da kwancewa be zabi wanda ya kamata yayi ba, karshe dai yaga gwara ya zauna da ita kar wani abu ya sameta kafin ya dawo ko wanchan dan iskan yazo ya dauketa, inyaso daga baya komai zasuyi da sameer saidai suyi……

Motar Deen na barin gurin sameer ya karaso, taba gate din gidan yayi ya jishi a rufe, mamaki ne ya kamasa amma be damuba da yake yanada extra key a hannu, be kawo komai ba ya bude gidan ya shiga…. Be bi takan neman Deen ba ya tafi dakin daya ajyeta straight, wayam yaga ba kowa, still be karaya ba ya shiga duba sauran dakunan gidan ko yamanta ya chanja mata daki saidai ko alamunta begani ba…

Ba karamin shiga tashin hankali yayi ba na rashin ganinta, gashi bega Deen ba, toh kodai Deen ya tafi da ita wajan daurin auren ne? Wai ko surprise ze masa ya dawo masa da ita a matsayin matarsa, tinanin hakan ne yasa hankalinsa ya kwanta sosai, duk wata damuwar dayazo da ita gidan yaji ta kau, ya kara samun kwarin gwiwar bijirewa mahaifinsa akan abinda yazo masa dashi, sam beji dadin haduwarsu ba dukda bawai yanajin dadin haduwarsu bane dama saidai wannan is worse, tinda yaje yake masa masifa ta inda yake shiga batanan yake fita ba, karshe kuma ya basa umarnin yin wani aiki me wahala da yake ganin ko duniya zasu taru akansa baze iyaba, Hakadai ya amsa masa zeyi badan zeyin ba……

Wayarsa ya fito da ita da niyar kiran Deen sai ya tina Deen be fito da waya ba, kishingida ya danyi yana jiran dawowar Deen da good news dan yasan ba shakka shiya tafi da yarinyar…….

Haka Deen ya zauna yana kallonta kamar wanda aka bawa ajiyarta, har lokacin mamaki yake wai shine haka akan mace, macen ma irin wannan da sai a hankali? Yanzu idan wani yaji ai sai y masa mummunan fahimta ya dauka sonta yake, shi ko me zeyi da wannan da daga gani zata basa ciwon kai, bama wannan ba meya hadashi da yarinyar da wa’yanchan mahaukatan ke hauka akanta tsabar rashin class, shi in soyayyar zeyi ai sai ya nemo yarinyar da shine ze zama first and last love dinta, bayasan mace me tarkacen masoya, sannan kuma bayasan reni so gwara ya dauko mace age mate dinsa atleast ta kai 30 ba irin wannan ba da daga gani she’s still a teenager (haba mallam deeni yada jumping into conclusion🙄) tazo tana basa wahala….

Ganin lokacin sallah yayi ya sasa tashi ya dauro alwala, a nan parlourn ya tada sallah a nitse…..

Samun kansa yayi dayi mata addu’a duk sujjadarsa kamar wanda aka bawa kwangilar mata addu’a, abun dariya kuma addu’a biyu yake maimaitawa, Allah ya shiryeta da Allah ya bata miji nagari yaketa fadi harya idar da sallah. Still be hakura ba ya cigaba da mata addu’ar ko bayan ya idar da sallah……

Yana cikin wannan hali yaji ‘tasssss tassss tasssss’ alamun fashewar abu me glass, mikewa yayi da sauri ganin ta dau center table ta buga akan tv, a take tv’n ya fashe kuwa, rasa abunyi yayi ya tsaya yana kallon ikon Allah, wurgi take da duk abinda ta samu a parlourn kamar mahaukaciya sabon kamu, tsabar shock ya kasa motsi bare ya hanata, toh yaushe ma ta farka? Wannan wace kalan yarinya ce haka?….

Ganin ta nufi dining ya daka mata wani mugun tsawa yace;

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button