Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 138

Sponsored links

Iya abinda Iffah kenan ta iya ji ta shige. Lokacin da ya shigo dakin zai shirya tata fatan ya shigo da file din amma sai ya shigo babu komai. Kuma bai mata maganar ba. Amma koda suka kammala shirinsu suka fito Sultan da kansa yau ma da yayansa maza biyu da uwargidansa sukai musu rakkiya har airport Iffah harda kwallarta hakama Uwargidan Sultan abinka da sabon mata bayan shigarsu jirgi sun zauna tana a jikinsa yana lallashinta sai ga file din nan ajiye a gefensa. Ta danyi mamaki amma sai ta basar, sai dai zuciyarta na sake tabbatar mata da koma akan wa file din ya kunsa yanada matukar muhimmanci ga mijin nata. Jirginsu na dagawa babu dadewa barci ya kwasheta……

Duk da saukar dare sukai tako ina a airport din zagaye yake da matakan tsaro. Kai da gani kasan mai kasar ruman dinne da kansa zai sauka. Ta bangaren masu tarbarsu kuwa manyan masarautar ne masu fada aji. Ga wasu lafiyayyun motoci ababen birgewa ga mai kallo. Sosa barcine a idon Iffah dan yanzu kam bata da aikin da yafi wannan. Hakan yasa ta kasance a kusan rabin jikinsa lokacin da suke fitowa, Dole duk wanda ke wajen yay kasa da kansa cikin jin nauyi. Shika gogan nasu ko’a kwallar rigarsa rungume yake da ita hankali kwance yana daga musu hannu daya alamar amsa gaisuwarsu har zuwa motar da aka ajiye domin su kawai. Sai da suka shiga har aka rufe sannan hadiman da sukal masu rakkiya ke fitowa a jirgi suma. A wannan tawaga musamman ta matan Diwa ce kawai zuciyarta ke a tsarkakake game da nado labari, amma sauran duk yan daukar rahoto ne. Sai dai kuma basu samo yanda suke so ba sam kasancewar su/Iffah’r sun musu wahalar ma gani ba kamar yanda su Uwa sukai tunani ba.

 

Tun daga airport har cikin masarauta jami’an tsaro ne, a cikin masarautar ma tarba suka samu da taima Iffah dadi, dan harda Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da kanta. Sal wata da Iffahr bata sani ba amma suna kama da Daneen Ammarah sosai kuma tana kama da Jaddah. Haka kawai taji a ranta itace Daneen Waheeda da aketa fada. Lokacin da take dagowa da ga rungumar da taima Malikat Haseenat zata rungume Daneen Ammarah idanunta suka sauka kan wata kyakykyawar farar budurwa sol tana balla mata harara. Bata santa ba, dan haka ta dauke idanunta ta maida hankali ya Daneen Ammarah din cikin rashin damuwa. A hankali ta saketa ta nufi Daneen Waheeda da ke tsaye tana kallonsu kusa da Malikat Ashwaq fuskarta babu yabo babu fallasa. Gabanta ta rissina ta gaisheta tare da Malikat Ashwag din. Amsa mata tai da dan murmushin yake sakamakon kallon da Malikat Haseenat ta watso mata. Sai kuma ta nufi Malikat Bushirat ta rungume, itama dai gain kallon da ake musu ne yasata shafa kanta tana yake, Jasrah kam saita boye bayan Malikat Bushirat din dan da gaske kunyar Iffah take ji. Murmushi Iffah tai itama ta rungumeta, dan koba komai kafin faruwar hakan al ta nuna mata soyayya ta gaskiya..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button