Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Ce Ita Hausa Novel Chapter 35

Sponsored links

Murmushi yayi ya dafa kafadar sameer yace

“Ni dama nasan you don’t mean it,amma it was an expensive joke,dan Allah karka sake min haka”…

“Insha Allah,I promise” Sameer ya fada kamar gaske….

“ Daga ina kake haka sam?”….

“Daga kano nake wlh,p man ne yamin kiran gaggawa shiyasa ban samu baka hakuri ba harna tawo”……

“Oh Allah sarki nima wani urgent abu ne ya kawoni wlh,hankalina yanzu baa kwance yake ba”…

“Subhanallah!,muje in raka ka dama na dade ban gaida momma da daddy ba”… Sameer ya fada dan so yake ya shigewa khaleel sosai….

Khaleel ji yayi kamar yace aa sanin fatima zainab na gidan,sai kuma yaga be kamata ba ganin yanda sameer ya nuna damuwa akansa….. Jerawa sukayi har suka karaso inda driver ke jiran khaleel,shiga sukayi ya jasu suka nufi gidansu khaleel….

Tun bayan sungama waya da sameer yake tinanin yanda ze fita daga gidan,shi in dan tashine be damuba zeta zama a gidan har sanda akaga daman sakinsa,saidai tinaninta ya hanashi sukuni,san sanin WACECE ITA na kara masa yawa,duk wani dan abu dayasani a kanta nanan makale a zuciyarsa,be manta da daddadar muryarta ba da kullum yakeji kamar a lokacin take masa karatun,be manta lallausan jikinta kamar na mage ba,be manta da zarazaran gashi idonta kamar wacce tayi fixing ba,inama ta bude idanuwanta sosai ya gansu,da yanzu ya kara a cikin dictionaryn dake zuciyarsa da yake rubuta komai nata a ciki….. Kai dole ma yayi wani abu,dole ya bar gurin dan yanaji kamar jininsa ze hau idan be ganta a yau ba……

Mikewa yayi yasa wayarsa a silent sannan ya tura ta karkashin pillow,a hankali ya murda kofar kamar yanda ya zata ya ganta a bude,komawa dakin ya sakeyi ya dauko wani powder daya gani a drawer yanada yakinin ita suka shaqa masa,murmushi yayi yana tinanin zeyi using way dinsu against them,zasuji abinda akeji suma,face mask din dake cikin aljihun kayan da yazo dashi ya dauka yasa sannan ya sake fitowa….. Luckily ba kowa a corridor din harya karaso parlour, komawa da sauri yayi jin motsi a parlourn,Allah ya taimakesa ba danno kai yayi ba….

Zaune suke su goma sha daya suna shayeshayensu hankalinsu kwance dan basu taba ganin kidnappern da be basu wahala ba kamar Deen,har mamaki suke ganin yanda ya sake hankali kwance,har tsaro suka rage ganin basa bukatar hakan…..

“Kai baba jibi zaa kashe wanchan wawan”…Daya daga cikinsu ya fada

“Ah haba haka boss yace kenan?” Wani ya kara fada yana zukar sigari

“Wlh ina fadamaka,ba shi ya sake ba yana ganin ana mishi duk abinda yakeso besan an kusa aikasa barzau……..

Maganarsa ce ta makale jin an bada musu abu a parlourn,take duk suka zube a sume…..

Mamakine ya kama Deen,it means he’s mistaken wanda yake tinanin shi yayi kidnapping dinsa bashi bane kenan….

“who’s behind this”

yafada kamar yana magana da wani

“Koma waye I’ll surely get you! Yanzu dama ba Dad bane yayi kidnapping dina ba?,God bless the unknown girl,da badan ke ba da yanzu ina chan thinking Dad ne yayi kidnapping dina,ze kuma sakeni at any time,ashe kasheni ake kokarin yi,Allah yasa inganki in fadamiki kin taimakeni”…..

Ya fada yana daukan bindiga daya sannan ya fita daga parlourn……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button