Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 17 Hausa Novel

Nihad Chapter 17 Hausa Novel

Sponsored links

Har daki Umma ta tadda Nihad tace “Toh Abbanki ya amince sai ki fara hada kayanki” Cike da farin ciki Nihad ta mike ta rungumeta tace “Nagode sosai Umma” Umma tace “Sai dai fa Abbanki yace driver xai dinga xuwa duk safiya yana daukarki ya kai ki makarantar sannan idan kun gama lectures ya maida ki gida” Nihad ta zaro ido tace “Toh Umma ya xan yi?” Umma tace “To na dai amsa ma Abbanki, amma ke yanxu sai ki samu Drivern kice masa ba sai ya je ba, xaki dinga tafiya da motar Kamila, should Incase Abbanki xai masa magana….”

Nihad tace “Toh shkkn Umma” Umma tace “Xaki makarantar yau?” Nihad tace “Ehh ina da lectures karfe sha biyu” Umma tace “Da sauran lokaci ai, sai ki fara harhada kayanki against tomorrow…” Daga haka Umma ta juya ta fita dakin, Murna a wajen Nihad ba a cewa komai, she is going to have enough freedom yanxu, wanka ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta shirya, bayan ta shirya ta fita xuwa bangaren Mumy, Mumy na gyaran bedroom dinta Nihad ta jingina da kofar dakin da damuwa tace “Mumy kin ji abinda Abba yace?” Mumy ta kalleta tace “Na me kenan?” Nihad ta marairaice tace “Mumy ni ba son zaman gidan Aunty Kamila nake ba, it’s so boring there, ni kuma ban san ya xan yi ba” Mumy tace “Then u speak for ur self Nihad, ni me kike son ince a nan?” Nihad tace “I don’t Know what to tell Abba” Mumy tace “Ki nemi abinda xaki ce masa ai baxai maki tilas sai kin ji ba”

A hankali Nihad tace “Toh” Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakinta, hada kayanta ta shiga yi a akwatunan ta cike da farin ciki, bayan ta gama ta sauka downstairs tayi breakfast, sae wajen karfe sha daya da rabi ta fita gidan zuwa makaranta ranta fari sol, yau ma dai adaidaita Sahu ta tafi ta hau bata bi ta kan Khalil ba, su Husnah da Naf har sun fi ta murna da ta sanar masu xata dawo hostel ta kuma gaya masu irin plan din da Umma tayi ma Abbanta, Husnah tayi shewa tace “Kai amma Allah ya shi ma wannan Umman albarka, Allah tana sonki sosai, ta san kan komai…” Nihad tace “Ke dai bari, ba don ita ba i will keep on being miserable in that house ga Yaya Farooq ga Mumy, the house is already a living hell for me, yanxu gobe xan taho da kayana hostel, har na gama hadawa kafin in fito” Husnah tace “Kuma albishirin ki, kin san saurayina ya kama mana tsadadden hostel a off K, xuwa next week xa mu koma wllh…”

Nihad tace “Haba dai” Husnah tace “Wallahi, dama ina ta son xan gaya maki sai in manta, yanxu kinga Da ni, ke, Naf, Zully, da Ummi xa mu xauna dakin, ita Ummi part time xata dinga xama kinsan tafi zama wajen saurayinta sai in baya gari ne take xuwa hostel” Nihad tace “But bamu yi yawa ba Husnah? Kinsan fa bana wani son takura a rayuwata” Naf dake danna wayarta tace “Kin ji ki, 2 bedroom ne fa sannan har da parlor with two toilet, ai baki kai ni rashin son takura ba” Nihad tace “Ohk that’s enough….” Kamar shekaranjiya da jiya yau ma dai haka suka shiririce a Cafeteria babu wanda ya shiga lectures cikinsu, daga karshe ma suka fita xuwa cin pizza a cikin gari, suna wajen cin pizza Nihad tace “Lah gashi har xan dawo hostel ba ku je gidan mu kun ga wawan yaron can ba” Husnah tace “Ai ko yau ya kamata kawai mu je” Nihad tace “Toh ae ke wannan gashin dake kanki ne matsalar kuma ya Farooq na gari wallahi” Husnah tace “A jakarki ba kina yawo da Hijab din sallah ba” Nihad tace “Eh” Husnah tace “To ara min kawai in sa don baxan iya wani komawa hostel ba” Nihad tace “Ohk” Zully tace “Kawai ku tashi mu tafi yanxu tunda biyu ya wuce” Naf tace “Amma yana gidan idan mun je yanxu?” Nihad tace “Nace maku 24/7 babu inda yake xuwa, da ma talla ya kasa a bakin gate din da ya dinga ciniki” duk suka kwashe da dariya, tashi suka yi gaba daya suka nufi motar Naf Husnah ta shige gaba, Nihad da Zully suka zauna baya, gaba dayansu tsadadden abaya suka saka, Nihad ce kadai ta sa atamfa da gyale. Karfe uku da yan mintuna Naf tayi parking dai dai gate din gidansu Nihad tace “Ashe dai xan iya gane gidan” Husnah tace “Ka ji ta bayan na gama baki direction kenan” Nihad ta sauka daga motar praying and hoping that khalil na bakin gate, sauran yan matan ma duk suka sauka daga motar, ta shiga gaba suna biye da ita har suka shiga gate din gidan, Aminu ya mike yana masu barka da xuwa, Nihad na kallonsa daga sama har kasa tace “Ina Drivern?” Aminu yace “Ai ko minti biyar bai yi da barin nan ba, yaje can ciki ya watsa ruwa yace min” Nihad tace shit a xuciyarta, why today of all days xai bar bakin gate din, kallon su Husnah tayi sai kuma da turanci tace masu su shiga ciki kawai kafin su fito xai dawo bakin gate din, a haka duk suka bi ta har xuwa main parlor din gidan, Aminu ya bi su da kallo, direct parlon Umma ta tafi da su, Umma ta fito daga dakinta jin sallama tana kallonsu tace “Sannunku da xuwa”

 

Duk suka gaisheta suka xauna saman kujera, Nihad tace “Umma frnds dina ne da nake yawan baki labarinsu, Zully da Naf, Husnah kuma tana xuwa gidan nan ai kin ganeta ko?” Umma tace “Kwarai kuwa na gane Husnah, sauran ne dai sai yau na san su, Allah sarki, sannunku da zuwa yan mata, ya karatu?” Duk suka amsa da Alhamdulillah, Umma tace “Madallah, kun kwaso rana kuwa” Daga haka tace “Ina zuwa” fita tayi daga parlon, Naf tayi kasa da murya tana kallon Nihad tace “Is she ur step mom that u are talking about” Nihad tace “Yeah she is” Naf tace “Waow she is really nyc wllh, very nyc woman” Nihad tayi Murmushi tace “Sure she is” Ba a dau lkci ba sai ga Hafsah da tray din lemo da ruwa ta ajiye masu bayan ta gaishe su ta fita, sai gata ta dawo da warmer din abinci da plates da spoon, ta ajiye ta fita, duk suka sauko suka yi serving kansu, Nihad ma ta dau plate ta debi abincin. Aminu na ganin shigarsu Nihad gida dama ya tafi da sauri ya kai ma Khalil tsegumin Nihad ta xo da kawayenta su biyar suna ta tambayarsa da harshen turanci, ko minti daya bai kara a chalet din ba ya koma bakin gate da sauri ya zauna, sai bayan la’asar su Naf suka shirya xa su bar gidan bayan sun ci sun yi nak, har da coslow Umma ta hada masu, Umma tace “Toh kin kai su sun gaida Maryam kuwa Nihad?” Nihad tace “Tana nan ko?” Umma tace “Aa tana ciki, su je su gaisheta” Ta fita da kawayen nata xuwa ɓangaren Mumy, duk basu xauna ba suka gaida Mumy da bata wani sake masu fuska ba, kai kana ganinsu kaga yara marasu tarbiya marasu kamun kai, Nails Naf tayi fixing a farcenta, Zully kuwa kana iya hango tatoo dake bayan wuyanta duk da mayafin abaya dake jikinta, Husnah kuma boobs dinta da bayanta ba a cewa komai kuma farko da Mumy ta santa lkcn farawansu makaranta ba haka take ba, yar siririya ce ita ma, amma lkci daya ta dawo uwar mata, Duk gaba daya sun tsargu da kallon da Mumy ke masu, Nihad tace “Za su wuce ne Mumy shine suka shigo su gaisheki” Mumy tace “Toh maa sha Allah, Allah yayi albarka” suka amsa da Ameen suka fita daga parlon, Mumy ta kira Nihad ta dawo, Mumy na kallonta tace “Kar ki kuskura ki wuce bakin gate din gidan nan” A hankali Nihad tace “Toh” Daga haka ta juya ta fita tana turo baki. Downstairs ta tarda su, Zully tace “Ur mother is too serious oo”

 

Nihad ta kyabe baki ta fita suka bi bayanta, Naf tace “The real African Mothers they are talking about” Duk suka kwashe da dariya, tsaye Nihad tayi balcony ganin har sannan Khalil bai fito ba banda Aminu kawai da take hangowa a bakin gate, Naf tace “Toh ina ɗan iskan drivern ne?” Nihad tayi shiru, sai kuma tace “Ina xuwa, ku jira ni” Gun Aminu ta tafi tana kallonsa tace “Kai Aminu har yanxu bai fito bane, zai ɗan rage ma kawayena biyu hanya ne” Aminu yace “Ni ma kin ga shi nake ta jira a nan Hajiya” Juyawa tayi ta koma balcony tace “Idan na tafi chalet da few minutes ku biyo ni can din” Tana fadin haka ta dau hanyar chalet din, bata ga takalmin kowa a bakin kofa ba, dama isiya da Saminu gantalallu ne wani lkcn idan suka gama duk abinda suke da safe sai su fita, su da dawowa kuma sai biyar xuwa shidda, a hankali ta bude kofar parlon duk da haka sai da yayi kara, ta shiga da takalminta tana yamutse fuska tana bin ko ina da kallo, ba laifi yau parlon bai yi kaca kaca ba, kuma babu wari, cikin sanda ta nufi corridor din dakuna, ta kai hannu handle din kofar dakin da Khalil yake ta murda a hankali ta tura kofar dakin, mikewa zaune yayi da sauri daga kwancen da yake saman gado, lkci daya ya hade rai kamar yanda ita ma ta hade rai, Tana masa wani kallo tace “Samun waje, kana bakin aikin ne xaka shanya baki da yamman nan kana bacci?”

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button