Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 78

Sponsored links

“Be kyauta ba gaskiya, amma ba gashi munzo ba, ki kwantar da hankalinki”….

Shiru tayi batace komai ba amma haka kawai takejin zuciyarta ta aminta dasu….

“What’s your name?”…..

Cewar Umm tana shafa bayanta…..

“Fatima zainab! You?”…

Haka kawai ta samu kanta da jin dadin conversation dasu itada maganar arziki bata hadata da mutane….

“My name is jamila, you can call me Umm, but dear your name sounds complicated, ya akayi kike bearing two real names?”….

“Bansani ba!”…

Ta fada da iyakar gaskiyarta……

Shiru taga sunyi sai kuma taji wani iri tana tinanin kodai basujin dadin abinda tace bane, a karo na farko kenan a rayuwarta data farajin wani iri akan yiwa babba rashin kunya, cikin rashin sanin abinda zatace dan harga Allah she’s mannerless tace;

“Kunji haushi ne?, so kuke na muku karya?”…

Dariya Umm tayi tana jan kumatunta tace;

“Not at all dear ai nasan baki sani bane, kawai I thought you need some rest shiyasa nayi shiru”…

“Okay, ita wannan ya sunanta?”…

Ta fada tana nuna mami da take binta da kallon ikon Allah ganin yanda take magana anyhow……

“I don’t know if to call her your namesake or what tinda suna biyu gare ki, anyway she’s anty fatima, you can call her mami”…..

Dan jim tayi tanajin wani iri a ranta because she feels like this is the first time da take having conversation da wanda bata yiwa rashin kunya ba, hakanan taji kuma bataso maganar tasu ta tsaya”….

“Toh shikuma wancen dan iskan waye?”…..

Ta fada ko a jikinta…….

Rasa wanda zeyi magana a cikinsu akai dan maganar ta dakesu, gashi su basusan meya faru a tsakaninsu ba bare su kareshi….

Murmushi me kayatarwa Deen dake bakin kofa yayi yana jin duk abinda suke cewa, honestly he never thought she can be this sweet dukda yasan babu manner da respect a yanayin maganarta amma wannan ce magana me dadi daya farajin tayi da wani dukda bashida tabbacin haka take magana…. Kada kai yayi yana murmushi at the same time a ransa yana fadin ‘wannan melodious voice bata dace da masifaffiya irinta ba!”……..

“Ya kukayi shiru, ko baku gane wanda nake nufi bane, wanchan kidnapper din fa, ina magana kunamin shiru ko, wallahi idan nayi zuciya I’ll never talk to you people again forever!”…..

Ya sake tsinto muryarta tana fadin hakan, dariya yayi sosai ganin zata nuna musu halin tin baaje ko ina ba….

Ruko hannunta Umm tayi tana murmushi dan ita ma harta fara fahimtar yarinyar nada issue medically and it has to do with ego ko kuma she’s a spoilt brat irin yarannan masu ji da kansu da iyayansu suka lalatasu, shafa face dinta tayi tana fadin;

“Ba kin kulaki mukayi ba, bamu gane wa kike nufi bane, and I guessed you misunderstood him, he’s not a bad person”…..

Janyewa tayi tana bata fuska cikin wani irin murya tace;

“Zan wuce, ana jirana”….

“Wa yake jiranki?”….

“Mijina”…

Da sauri Deen ya banko dakin yana fadin;

“This is not her voice, wallahi ba ita bace!!

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button