Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 54

Sponsored links

Saida Abby yaga abin nasu na neman wuce gona da iri sannan ya daka musu tsawa yana yafito Deen da hannunsa, yi yayi kamar be gani ba ya cigaba da binta, itako taki yarda ta tsaya dan bataki ko kwana zasuyi suna zagayen suyi ba da akan ta bari ya kamata, da taga hanya ma da tuni ta fita daga filin jirgin……

“Saifuddeen! Saifuddeen!”…..

Abby ya sake fada a kausashe……

Dan dakatawa Deen yayi ya kalli abby, babu alamun wasa abby yace masa yazo, zuwa yayi yana wani hura hanci, mamaki sai kama Abby yake ganin yanda Deen ya koma kamar ba wanda ya sani ba……

Asibiti motocin Abby suka nufa kamar yanda yace a fara zuwa chan dan a duba khaleel, neman birkice musu Deen yayi wai shi baze je asibiti, saida abby ya tsawatar masa ya kuma masa tatas akan rashin tausayinsa, ya zaayi ace ka jiwa mutum ciwo amma ko a jikinka, sai ce masa yayi khaleel deserves it, Abby kuma yace dole sai anje dashi, haka bashida yanda ya iya suka nufi asibiti, emergency akayi rushing khaleel suka zauna zaman jiran feedback………

Shirye dad da mom suke tsap kowannensu ransa a hade, kadama dad yaji labari dan shi yafi jin ciwon abinda ya faru tinda dansa ne wai a haka ma mom tanata kwantar masa da hankali………

 

Tun bayan ya kira mami ya mata kashedi akan rashin zama a gurinsa da Deen bayayi ta masa tass dan dama itama tana cike dashi kuma duk a tinaninta Deen yana kano, maganganu ta gayamasa san ranta, harda cewa Deen din da rabon da taganshi harta manta shine dan renin hankali ze kirata yau ya mata borin kunya ya nuna mata Deen baya kano bayan tasan yana kano, ransa ne yayi balakin baci yaga abun bazeyiwu ta waya ba, gwara yaje ya sameta face to face ya mata nasa cin mutuncin, mom dake zaune tanajin duk wayar da sukayi tashiga kwantarwa da dad hankali sannan tace zata rakasa, nan ko itama so take taje ta saukewa mami nata rashin mutuncin dan gani take mami ce ta hana deen ya so hameeda, gashi tayi duk wani abu daya dace amma yaki son yar lelenta…….

Shine suka shirya suka tawo abuja, a halin yanzu ma suna garin abuja sun gama shiri zasu tafi gidan mami……..

 

Sun fi two hours suna jiran zuwansu amma shiru basu zo ba, alhaji habibu ne yake ta basu karfin gwiwa akan su kara hakuri yasan yanzu zasu gansu, daddy ko dama bece uffan ba tinda suka zauna…….

 

Dafa kafadar daddy Alhaji habibu yayi yace;

 

“Ka kwantar da hankalinka babu abinda ze faru”…..

 

Kamar jira daddy yake yace;

 

“Ya zaayi in kwantar da hankalina? Kana ganin komai ya kusa kwabe mana kace in kwantar da hankalina? Bazan iya ba”……

 

“Ni nasan abinda zamuyi shiyasa nace ka kwantar da hankalinka”……

 

Daddy ze sake magana kenan suka ji knocking, fasa maganar yayi ya tashi da sauri yaje ya bude, kamar yanda yayi sammani su yagani, hanya ya basu suka shiga yana biye dasu……

 

Gaishesu suka farayi daddy ya katsesu da fadin;

 

“Just go straight to the point! Baku ganshi ba haryanzu?”………

 

Dariya wanda ya kasance ogansu yayi ya dora kafa daya kan kujera yace;

 

“Bamu ganshi ba amma muna da tabbacin inda yake!”…….

 

Zabura daddy yayi ya mike yace;

 

“Ina yake? Ina yake?”…….

 

“Kwantar da hankalinka alhaji! Zan fadamaka amma sai an bamu cikon kudin mu!”……

 

Alhaji habibu ne ya karba da fadin;

 

“Bangane sai an baku cikon kudin ku ba? Ai ba haka mukayi daku ba, cewa mukayi idan kunyi kidnapping dinshi zamu cika muku!”…….

 

“Eh toh bamu daukeshi ba amma mun samo inda yake, guri ne kuma da bazamu iya shiga ba sai dai kuje da kanku ku daukoshi, idan kun shirya sanin inda yake ku bamu sauran kudinmu, idan baku shirya ba kunga tafiyarmu”…….

Ya fada yana yiwa yaransa signal din su tafi, daddy ne ya dakatar dasu da sauri dan yasan idan suka wuce bazasu dawo ba, wa kuma zasusa su nemo musu khaleel idan wannan manyan yan ta’addan sun kasa……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button