Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 52

Sponsored links

Abby ne ya fara sauka bayan jirgin ya tsaya, Deen be motsa daga inda yake ba saima kokarin saita tracker da yayi ya duba yaga ko ansake kunna wayar be sani ba tinda yasa wayarsa a flight mode da sukayi taking off, saida ya gama saitawa tsap sannan yayi relaxing yana kallon yanda abun ke processing…….

Kamar a mafarki yaji takun takalma daga gefensa, mamaki abun ya basa dan duk a tinaninsa daga shi sai Abby a cikin jirgin bayan pilot da air hostress, juyowa yayi da sauri dan yaga su waye, yana juyowa idonsa ya sauka akansu, murza idansa ya hau yi dan ya tabbatar su din yake gani dagaske…….

Tinda sukayi ido hudu dashi suka sandare a gurin kadama fatima zainab taji labari dan lokaci daya ta nemi ta fita hayyacinta, ganin ya mike ya sata yin hanyar toilet a guje tana fadin;

“Runaway honey khal, ka guduuuuuu”…….

Dan a yan kwanakinnan ta saba dace masa honey khal ko darling khal bata iya kiransa kai tsaye…..

A guje shima Deen ya bita ganin ta fita a guje tana kiran wani gardi kuma honey a gabansa saidai ko kafin ya karasa ta shige toilet ta rufe kanta, kwafa yayi juyo yayi kan khaleel a zuciye…..

Chakumoshi yayi ya bugashi da kujerar da Abby ya tashi sannan ya shiga zabga masa maruka a fuska, saida ya zuba masa kyawawan maruka goma a hagu da dama sannan yayi ball dashi ya cilla shi inda suka fito, binsa ciki yayi yayi wani kukan kura ya shako wuyarsa cikin wata iriyar murya irin na wanda ya dade yana kwasar bakin ciki da takaici yace;

“Dan uwarka da ubanka an daura muku auren?”…

Shiru khaleel daya jigata ya kasa magana yayi…..

Sake ball Deen yayi dashi ya kuma binshi ya kamo shi cikin muryar datafi wanchan tashin hankali yace;

“Zaka bani amsa ko sai na kashe ka?”…….

Cikin tsoro da fitar hayyaci khaleel ya bashi amsa batareda yasan abinda yake cewa ba…..

“An daura”……

Wani irin kukan zaki Deen yayi ya shiga jibgarsa kamar an aikosa, tsabar yanda yake dukansa har kara jirgin yakeyi, ji kake kichi kichi kichi kamar ana yaki……

Ajiyar zuciya ya sauke me karfi yanajin wani sanyi a ransa bayan ya cilla khaleel ta window sai kuma ya koma toilet din data rufe kanta a guje……..

 

Bubbugawa ya hau yi kamar ze balla kofar, fadi yake;

 

“Ki bude kona balla kofarnan! Ki bude, I must kill you today, why did you marry him? Why will you allow him to sleep with you? Why? Why?”……..

 

Tana tsaye tana jinshi amma ko motsi ta kasa, sosai ta shiga tashin hankalin da bata taba shiga irinsa ba a rayuwarta, hankalinta in yayi dubu ya tashi sai gumi take dukda akwai ac a toilet din……..

 

Cigaba da buga kofar yayi yanata zuba sambatun dabe sani ba, yana kara maimaita mata saiya kasheta kamar yanda ya kashe khaleel…….

 

Kalmar data daga mata hankali kenan taji tsuuuuu period dinta ya zubo abinda taketa fama dashi yazo, sai ga wani zawo shima ya tawo mata, fashewa tayi da kuka ta zauna a toilet seat tana kashi……..

Be saurara ba ya cigaba da buga kofar yana kara fadin mugayen kalamai, a haka kofar ta dan fara losing alamun ze iya ballewa anytime soon……..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button