Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 90

Sponsored links

Uwa ta faɗa tana mai ɓacema ganinta a sannu-sannu harta daina ganinta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke ranta duk babu daɗi. Dan zuciyarta kam ta fara ayyana mata ƙarfin ikon uwa ya fara sanyi. Dole ne ta nema sabon mai taimakonta duk da bazata taɓa mantawa da gudunmawar da uwa ta bata ba harta kawo wannan matsayin a wannan daula ta ruman da ayanzu take kamar mai juyata ta ƙarƙashin ƙasa da zahiri a yanda take so. Amma ga karamar yarinya da bata wuce kiyashin da take murjewa a ƙasan tsinin takalminta batare data sani ba tana neman zamewa rayuwarta wata ƙadangaren bakin tulu a gabar cikar babban burinta na ƙarshe…

A ɗan firgice Iffah da kiran sallar asubahi ya farkar take kallon kanta da inda take a yanzu. Cikin shiga razani mai ban tsoro ta diro a gadon daya kasance saɓanin inda ta kwanta a daren na jiya. Kamar wadda ake ingizawa ta fice a ɗakin cikin sassarfa. Tabbas sashen Tajwar Eshaan ne dai take. “Taya haka zata kasance?”. Ta faɗa cikin bugun zuciya. Sai kuma ta fara tunanin kodai mafarki take yine. Hannu takai ta ɗan mari fuskarta. Sai dai babu abinda ya canja daga wanda idonta ke gane mata a yanzu. Dan lallai da gaske a sashen Shahan-shan ɗin dai take.

 

“Ya ALLAH mike faruwa da ni ne haka wai. Taya zan kwanta a sashen da ba wannan ba na kuma buɗe ido na gannni? Jiya an ɗaukeni daga ƙasa an maida saman gado na share, amma shine yau kuma za’a ɗakkoni daga wani sashe zuwa wani daban. Anya ba matsafan gidan nan ke son min wasa da hankali na ba?”.

 

 

Wannan tunani na karshe ya sata saurin kama rigarta ta shinshina. Tabbas irin dai ƙamshin turaren jiya ne da karfinsa harya danne nata. “Ya Arrahaman” ta sake faɗa tana mai juyawa ta shiga kallon ɗakin da sauri. A kan tarin kayan turarruka da idonta ya sauka a kai ta nufa, ta buɗe gilashin da suke ciki kamar dai nacan ɗakin ta fara shinshinasu ɗaya bayan ɗaya. Sai dai abin mamaki babu wanda ƙamshinsa yay kama da wanda takeji a jikinta. (Dole ne ma na gano, kuma ta wannan ƙamshin insha ALLAH). Ta ayyana a zuciyarta cike da alwashin hakan. Alwala taje ta dauro jin makara na neman riskarta. Bayan ta idarne kuma ta sake nutsuwa wajen ƙarema ɗakin kallo yanda ya kamata. sai yanzu ma ta gane ba inda ta kwana a jiya bane wani ne daban. Sai dai shima wannan ɗin ya matuƙar haɗuwa fiye ma da wancan ɗin. Saɓanin wancan da tsarin komai na cikinsa ke fari anan kuwa komai blue ne, ga wani ƙamshi na fitina na tashi kamar dai wancan. Abu mafi ban mamaki nan ɗin dai duk da ya nuna ana tsaftaceshi a hargitse yake kamar anyi dambe a cikinsa. Ita kanta dama a shigarsa toilet har mamakin yanda taga kanta a birkice tai, dan tasan dai tsaf ta kwanta kuma bata buge-buge a barcin. Son yin salla a kan lokaci ya sakata bata maida hankali ba sai yanzu data idar ta samu nutsuwa. Tayi tunanin gyara ɗakin da fita binciken turaren nan na jikinta da alama ya tabbatar mata mai shi ke son wasa da tunaninta, sai dai wata zuciyarta ta bata shawarar ajiye waɗan nan batun ta sake kwanciya irin ta jiya tai likimo kozata samu bakin zaren ta hanyar shigowar wanda take zargin kamar jiya. Ta gamsu da hakan tako kwanta, sai dai tsahon kusan awa ɗaya babu wani wanda ya zo ɗakin, babu ma alamar wani ɗin zai zo harta tashi akan dole ta kimtsa ɗakin ta shiga wanka. Kayan data samu a lokacin gyaran ɗakin ta sanya babu ko ɗar a ranta. Tayi ƙyau sosai, ta kuma sake baza turarurrukansa a jikinta kamar jiya sannan ta fice a sannan kusan ƙarfe bakwai da rabi…

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button