Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 84

Sponsored links

Kamar bazata tanka ba, tai taku ɗaya zuwa uku batare data dubi Jasrah ba tace, “Zawjata-almilk. Da alama tana buƙatar sai an saita mata zama da tuna mata nan daular ruman ce ba getto eria ɗin data rayu ba. Komai muna yinsa da ƙa’ida bisa umarnin na gaba”.

“Kiyi haƙuri Akia. Amma na kasa fahimtar miya kawo wannan maganar, wace kuma Zawjata-almilk ce a cikin yaran? Dan nasan dai kinfi kowa so da ƙaunar wadda ke tare da shi a halin yanzu”.

“Ina sonta bashi zai bata lasisin shimfiɗa abinda ta gadama na a saman nawa ƙarfin ikon ba. Yanzu labari ya iso gareni ta fito daga sashen Saiful-malik zuwa books room tare da hadimai”.

“Tofa, ita kuma da wannan tazo? Mu muna murnar samunta matsayin wadda zata share kukanmu amma zata fara da haka?. To amma fa Akia wani hanzari ba gudu ba. Shin baki ganin salon yarinyar a wani mahangar nasara ce a garemu. Na farko dai babu wanda yasan ta fito ne batare da umarninki ba. Na biyu koba komai ta sake jaddada isar da saƙonmu akan maƙiya. Na uku salonta tamkar barazana ce ga duk wani shu’umi dake rayuwa a wannan masarautar. Inaga bai kamata ki damu ba, dan a wani ɓangaren ma kamar mune masu laifi, karki manta Mammah ta mikata sashen Abni batare da bin ƙa’idojin da ake kai Zawjata-almilk turakarsa ba. Sannan inada tabbacin ba’a sanar da ita komai game da tsarin komai ba fa, sai aikin da muka faɗa mata zatayi a garemu”.

A hankali Malikat Bushirat ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya. Cikin kwantar da murya ta ce, “Hakane kumafa Jasrah, kin tunatar da ni abinda ya ɓacemin har idona ya rufe. Sai yanzu na fahimci lallai wannan fitar tata ma da alama tanada manufa akan umarnin aikinmu. Duk Mamma ce da wannan kwamacalar da muka kasa fahimtar manufarta a kai, nayi niyyar zuwa sashen nata ma naji dalili baƙin nan na ɗazun suka cinyemin lokaci. Amma munyi magana da Ammarah zuwa anjima zanje ko cikin ɓadda kama ne”.

“Hakan yayi, dan koni ina son sanin yaya akai hakan ta kasance. Duk da dai Alhamdullah yarinyar ta kuɓuta. Amma mun kwana a fargaba ai dan ko barci jiya banajin waninmu yayi wlhy. Hatta da Abu Harith kwana yay tunani”.

Murmushi Malikat Bushirat tayi, dan har cikin ranta tana ƙaunar ƙanin mijin nata kuma mijin ƙanwarta, tare da yaba ƙoƙarin sa akan kulawa da kaunar da yake nunawa ga gudan jinin nata tilo da har wasu ke jin zafinsa a gidan bisa hakan…..

Katafaren ɗakin daya kasance mai cika ido ga Iffah tsarinsa ya matuƙar ƙawatar da ita. Ta samu jagorancin shiga lungu da saƙo na cikinsa bisa taimakon masu kula da ɗakin. Inda a zagayen nasu suke nuna mata abubuwan tarihi na tun farkon ƙarnin kafa Daular ruman ɗin da suka shuɗe cike da girmamawa a gareta. Tafiya kam mabuɗin ilimice haƙƙun dan Iffah ta ilmantu da abinda yafi wanda ta sani ƙalilan a baya dangane da tarihin daular ta ruman da akan tsakura musu a darasin makarantu.

Shugaban masu kula da sashen ya matuƙar nuna jin daɗinsa da bata shawarwari kan tsarin zama mai nazarin tarihi data ambata dan abune daba kasafai ake ganinsa ga matan cikin masarautar ba. Akwai wadda ma bata taɓa taka ƙafarta cikin ɗakin litattafan ba. Amma ita gata ƙaramar yarinya da rayuwarta ke kamar akan ɗar-ɗar abinda ta fara nuna sha’awa na farko akansa kenan. Shine ya fara zaɓa mata books daya ga ya dace ta fara dubawa, hakan yasa ta basar da waɗanda ta shigo nema kai tsaye, dan a ganinta bin shawarar tasa zaifi bata fiye da abinda take buƙata ɗin. Shugaban da shekaru sunyi matuƙar ja a garesa yaji daɗin amsar shawarar tasa da tayi, dan yasan duk da zai iya haifarta matsayinta ya bata ikon yin duk yanda taso a sama da shi

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button