Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 33

Sponsored links

Around 5pm fatima zainab ta bude kofa ta fito parlour, tsit kakeji kamar ba kowa a gidan, akan wayar Umm dake kan kujera idonta ya sauka, wayar da Umm batasan ta bari ba saboda rikicin da suka shiga, har zata share sai wani tinani ya fado mata kan ta dauka ta kira khaleel tinda ta haddace numbersa, dauka tayi tana duba wayar taga ba password, sai kuma wata zuciyar tace gwara ta samu ta fita daga gidan sannan ta kirashi, kamar wacce aka fadawa ta shiga laluben key a drawers din dake parlourn, aiko ta samo su dayawa, fita tayi da sauri hannunta rike da wayar Umm ta nufi gate din baya…..

Tafi 10mins tana trying keys din data kwaso be budeba, hartayi losing hope tana zira dayan daya saura a hannunta kofa ta bude!!!!!!

A hankali ta bude gate din ta fita, da sauri tayi gefe jin kamar motsi daga cikin gidan, saida taji shiru baa tawo ba sannan ta fara tafiya, tana tafe tana dialing number khaleel a wayar Umm data fito dashi, ringing wayar ta dingayi baa daga ba, bata hakura ba ta cigaba da dialing number, tana cikin wannan hali taji takun takalmi a bayanta, kirjin tane ya bada sautin rass, ko baa fadamata ba tasan waye balle ba wani nisa da gidan tayi ba, wata zuciyar ce tace ta zura a guje kawai, zatasa gudu kenan taji an kamo tsintsiyar hannunta, kin juyo tayi dan tasan bazasu kwashe ta dadi ba……..

“Wifey ina kuma zaki?”…..

Basuyi tafiyar 10 inches ba suka isa inda khaleel yayi parking dan nesa da gidan, shiga motar sukayi yaja suka fara tafiya in silence…….

Wani ajiyar zuciya fatima zainab ta sauke ganin dagaske sun bar unguwar, sai a lokacin ta samu nitsuwa taji hankalinta ya kwanta, ta kuma kudirta a ranta bazasu kara haduwa ba har abada ita da Deen….

Duk uban gudun da Deen yake khaleel be hakura ba haka yayita binsu shima ana kauce masa har yaga gidan da Deen yashiga, suna shigewa shima yayi yunkurin shiga saidai kememe securities din gidan suka hanasa dan baa san da zuwansa ba, sukace in ya matsu ya kira wani a gidan shikuma bashi da wanda ze kira, haka ya dawo yayi parking dan nesa da gidan ya cigaba da zama a cikin mota hoping fatima zainab zata fito anytime soon, ko damuwa da jinin dake fita daga goshinsa bayayi burinsa kawai yaga fitowarta dan yasan tinda tace zata bishi su gudu toh tabbas zata fito dan bata taba cewa zatayi abu batayi ba……. Sai yayi using time din wajan neman musu ticket din country din da zasuje, booking hotel da sauransu…

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button